HAUSAWA DA MAGUNGUNANSU

HAUSAWA DA MAGUNGUNANSU

Daga Almustafa Shehu Kofar Atiku

1. GWADDAR DAJI
Gwaddar daji Sassake yana maganin tsutasr ciki, zawo, ciwon ciki, saran maciji, ciwon baki da ciwon hakura.
Sassake hadi da sansami (Kunnuwa) suna maganin hakarkari, huka, asma, da sauran ciwon gaba.
Saiwa (Saye) tana maganin sanyin mata, da burkutar ciki. Sauran bangarorin bihiyar suna maganin ciwon idanu da fata.

2. TUMFAFIYA
Tumfafiya tana wanke ciki, tana maganin makero, kyafsi, kurkunu, kurajen zufa, Asma, cizon kunama, tunjere da ciwon idanu.
Saiwa tana maganin cizon maciji.

3. NAMIJIN YADIYA
Namijin yadiya ruwansa suna maganin zanzana (Ado) irinsa yana maganin ciwon idanu.

4. ADUWA
Sassaken aduwa da 'yayanta suna maganin fitsarin jini, kurkunu ciwon farfadiya, rashin haihuwa da ciwon hauka.

5. SANSAMI (Jiri)
Sassaken sansami, saiwa, da gidan iri suna maganin gyambo, kuraje, kuturta, sanyin mata da tari.

6. ISKICI
Sassaken iskici yana maganin cizon kunama, cizon maciji, masassara ciwon ido.
Saiwa tana maganin ciwon ciki da tsutsar ciki.

7. ANZA
Sansamin anza, yana maganin ido, fitsarin jinni, ciwon ciki, kuraje, kurkunu, da fitar bai (Basur)
'yaya suna maganin ciwon tunjere.

8. NAMIJIN TSADA
Saiwar namjin tsada tana maganin cizon maciji, ciwon tunjere, ciwon ciki, kuturta, diddira da karfin maza.
Sansaminsa suna maganin ciwon hakura, tsutar ciki, ciwon ido, rashin samun haihuwa ga mace, kuraje da wankin ciki.
9. SABARA
Saiwar sabara tana maganin zawo da diddira
Sassaken sabara yana maganin ciwon ciki. Sansami suna maganin tari, mashasshara da ciwon ciki.

10. KAIWA
Sassaken kaiwa yana maganin kuraje da gyambo.
Saiwarta tana maganin diddira, tsutsar ciki, mashasshara, hakarkari, tunjere da kuraje.

11. MALGA
Saiwar malga tana maganin sanyin mata, diddira, fitar bai,
Sansami suna maganin masassara, gyambo da kurajen baki da na dasashi.

12. KIRYA
Kirya tana maganin ciwon kai, ciwon haure, ciwon amosanin kashi, ciwon fata, masassara da diddira.

13. DOGON YARO (Darbejiya)
Sassaken dogon yaro kunnuwa da mai suna maganin masassara, ciwon fata, sanyin mata, ciwon amosanin kashi, da ciwon tsutsar ciki.

14. MADACI
Sassaken madaci yana maganin shawara, cizon kunama ciwon tsutsar ciki.
iri da sansami, suna maganin masassara da ciwon kai.
Saiwa tana maganin rashin haifuwa, da ciwon hauka, da karfin maza.

15. ZOGALA (Tamakka) 
Zogala tana maganin ciwon amosanin kashi, kurajen zufa, ciyon dasashi, shawara ciwon kai, sanyin mata, da tunjere.

16. MAGARYA 
Magarya tana maganin tsamukar ciki, ciwon gaba, ciwon hanta. Saiwa tana maganin zawo.

ABIN KULA 
Duk wadannan bayanai da aka yi a sama, an yi su ne domin yan uwana masu maganin gida (Gargajiya), ba an yi wadannan bayanai ba, don mutun ya yi wa kansa magani ba, domin hatsarorin da ke tattare da yin haka. Idan an kula ba a yi bayani cikakke ba a kan abin da ya shafi aikin warkarwa, ko kuma shirya magani, da kimar da ya kamata a sha, da adadin kwanuka, da kuma ko sau nawa ya kamata a sha. Don haka a kula. 
Muna bada magani a kan wadannan cutuka, kamar haka:
Shawara, sanyin mata, tunjere, tarin tibi, Kuturta, yankan gashi, rashin haifuwa, da sauransu.
A tuntubi:
Almustapha Traditional Medical Herbs,
Kofar Atiku,
Modibbo Adama Junction
08033875985.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

GLOBNG HUB - Best for All Globng Hub and SGL is for interested content creators who wants to share their experience to the whole world, you can create account with us, when your account is approve you can then proceed to create contents ranging from entertainment, sports, politics, health and fitness, society news, technology, business and industrial, lifestyle, education, pet and animals etc. The interested thing is you will get paid as far as your contents/articles worth paying. To Register click on the link below https://globng.com/register