Hausawa Na Da Kirki, Fulani Ne 'Yan Ta'adda - Nnamdi Kanu

Shugaban haramtacciyar kungiyar masu yakin kafa kasar Biyafara, Nnamdu Kanu, ya bayyana cewa Hausawa na nuna halayen kirki gurin alaka da yan kabilar Igbo, ta hanyar zamantakewa da sauran harkokin kasuwanci.
Amma yace ƙabilar Fulani ne suka kasance matsala ga Inyamurai da sauran kabilun Najeriya, sakamakon miyagun ayyukan da suke aikatawa na kashe-kashe ga wadanda basu ji ba, kuma ba su gani ba.
Kanu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Emma a tsakiyar makon nan da muke ciki.
A cewarsa, Fulani na son shafawa Hausawa ɓangaren matsalar da suka haifarwa Najeriya ta hanyar kiran kansu 'Hausa-Fulani'.
Kanu ya yi kira ga Hausawa kada su bari wani ya jefasu cikin matsalar da Fulani suka haifar. Yace: "Tun 2015 muna jin Fulani kaza, Fulani kaza, amma saboda wutan da IPOB ta kunna musu, sun fara amfani da sunan Hausa-Fulani domin boye halinsu saboda Hausawa mutanen kirki ne."
"Ina son in bayyana cewa mu 'yan Biyafara bamu da matsala da Hausawa. Ina ganin girman Hausawa kuma ina son su. Hausawa mutanen kirki ne."
"Shi yasa mu 'yan Biyafara muka zabi Bahaushe ma matsayin kansila sau biyu a Enugu."
Matsalar Najeriya Fulani ce..Abinda ke hana Fulani Makiyaya kwace Najeriya kungiyar IPOB ce."

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author