Hotuna: Kalli Hotunan Ɗalibar da ta shiga Makaranta da Bindiga don ta harbe Malamin da ya c eta aske gashinta mai launi
An kama dalibar makarantar Sakandare da ke Jihar Cross River dauke da bindiga a makaranta,
Rahotanni sun ce dalibar ta tafi da bindigar makaranta ne da nufin ta harbe malamin da ya ce ta aske gashin kanta, an kuma gayyaci sojoji su zo makarantar domin su karbi bindigar tare da mika ta ga hukuma haka kuma an kama wata dalibar makarantar sakandare dauke da bindiga kirar pistol na gargajiya da aka ce tana shirin harbin malaminta a makaranta wani malami a Makarantar Sakandare ta Gwamnatin na Ikot Ewa a jihar Cross ya umurci dalibar da aske gashin kanta da ta rina zuwa wani launi sai hakan ya fusata ta ta har ya zama silar wannan al’amarin.
Hotunan dalibar sakandaren da aka kama da bindiga za ta harbe malaminta da ya ce ta aske gashinta.
Source: Legit Hausa
You must be logged in to post a comment.