Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Jihar Kano Tafi Kowacce Hukuma Aiki A Najeriya-Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, inda yace itace mafi karfi a kasar nan wajen inganta lissafin kudaden jama'a da kuma jagoranci nagari.

Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na kungiyar akawun Najeriya (ANAN) wanda aka gudanar a Nassarawa GRA, Kano a ranar Talata , 17 ga watan Nuwamba.

Kalaman dai na Ganduje sun haifar da surutai a kasa ta la'akari da halin da Gwamnan ya taba tsintar kanshi a ciki na zargin karbar cin hanci da rashawa a shekarun baya, amma babu wani mataki da hukumar ta dauka a mataki jiha.

Duk da yake an rawaito cewa shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano Dr Muhyi Rimin Gado ya kalubalanci jama'a da cewar duk wanda ya gabatar da kwakkwarar shaida na karbar rashawa da ake wa Gwamna Ganduje ba kame-kame ba, hukumar zata yi aikin ta na ba sani ba Sabo.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author