Idan Sojoji Sun ci Mutuncinka ko na Al'umma Kayi Kararsu a Wadannan Lambobi Ga Hukumar Soji

Hukumar rundunar sojojin Najeriya ta samar da wasu lambobin wayar salula guda 4, wadanda al'umma za su ringa kira domin su yi karar duk wani jami'in soji da ya ci mutuncin su kawai su kira Kai tsaye zuwa Rundunar sojojin.

 
Hukumar ta bukaci al'umma da su dauki hoto ko murya, ko kuma bidiyon a lokacin da abin ke afkuwa, ko kuma a tura a lambobi da aka samar  ta WHATSAPP ko TEXT.
 
Sannan an bukaci a sa daidai waje da rana da kuma lokacin da abin ya faruwa a aika zuwa lambobi da ke kasa. Kada a kira.
 
07017222225
09060005290
08099900131
08077444303
 
Kawai domin kira kai tsaye, sai a kira  193.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author