Idan ya tabbata gwamnati zata cigaba da koran Ma'aikata to mai zai faru gaba?

Talakawa sun hakura da ilimin gwamnati suna biyan kudi? Sun hakura da ruwan sha na Gwamnati suna sayen na kasuwa? Sun yanke kauna kan Makomar lafiyar su suna neman magani ma kansu cikin tsananin tsada?
 
Abinci ya fara gagaran su Sabila da tsananin tsada da hauhawan farashi gwamnati ta kasa tsaida lamarin kullum sai kara dulmiyewa yake yi bisa cewa Fetir yayi tsada? Talakawa suna biyan kamfanoni kuɗaɗen wutan lantarki da bala'in tsada?
 
Yanzu haka tsaro ya zamo barazana mafi girma da talakawa suka zamo wata kaddara da ake iya kamawa ayi ciniki na kudi mai mugun yawa a biya? Yanzu haka dai wanda suka rage suke kallon kima da darajan Gwamnatin dai sune wanda suke samun dan kaso a karshen wata mai suna Salary. Wanda shima a daddafe wasu ke iya cin abinci da shi.
 
To yanzu ma'aikatan ma sun koma abin tausayi an fara musu koran kare kora ta rashin mutunci daga bakin aikin da suka dogara da shi tsawon lokaci.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author