Illar Sa Coge Ga Lafiyar Kafa

Takalmi coge yana da tsayi hawa-hawa kamar inci ɗaya, inci biyu da inci uku, da sauransu. Ana auna tsayin cogen ne ta hanyar auna tsayin tsinin cogen daga ƙasan tsinin zuwa tushensa da ke matakar dunduniya.
 
Tafin sawu da yatsun ƙafa waɗanda ke ɗauke da tarin gaɓoɓi da aka yi musu shiri na musamman domin tsaiwa, takawa ko tafiya cikin sauƙi. Daga cikin aikin wannan jerin gwanon gaɓoɓi da ke tafin sawu ya haɗa da shanye jijjiga ko girgiza da ke faruwa yayin tsaiwa, tafiya ko gudu sakamakon saukar nauyin jiki a kan ƙasa. A taƙaice dai, jerin gaɓoɓin tafin sawu an yi musu ƙira ne ta “shock absorber” kamar yadda ababen hawa ke ɗauke da ita domin shanye jijjiga yayin tafiya.
 
Saboda haka, a lokacin da aka sa coge wannan “shock absorber” za ta ɗame, don haka ba za ta yi aikinta na shanye jijjiga yadda ya kamata ba.
Haka nan, sa coge na tattare da haɗura da ka iya afkuwa nan take ko bayan wani lokaci kamar:
 
1) targaɗe
2) gurɗewa
3) gocewar ƙashi
4) karaya
5) ciwon yatsun ƙafa
6) ciwon idon sawu
7) ciwon ƙasan tafin sawu, da sauransu.
 
Bayan nan, kasancewar matsalolin sa coge ba su taƙaita iya ƙafa kaɗai ba, akwai matsalolin da sa coge mai tsayi yau da gobe fiye da ƙima kan kawo kamar:
 
1) ciwon gwiwa
2) ciwon baya
3) ɗaurewar dambubu (gungun tsokokin bayan sangalalin / ƙwauri), da sauransu.
 
Waɗannan matsaloli suna faruwa ne sakamakon jirkicewar tsarin zaman ƙashi da tsoka a jikin mutum tun daga tafin sawu har zuwa gadon baya a duk lokacin da aka sa coge yayin tafiya.
 
Domin haka, ya kamata mata masu sha’awar sa coge da su:
a) zaɓi mafi ƙarancin ko matsakaicin tsayi da tsini, saboda da haɗarin sa coge na ƙaruwa ne da ƙaruwar tsayinsa ko tsininsa. A shawarce, an son kada tsayin cogen ya wuce inci uku.
 
b) Sannan a guji sa cogen da zai matse yatsun ƙafa sosai, don haka a zaɓi mai yalwataccen wurin zira yatsun ƙafa domin jini ya ci gaba da gudana.
c) Bugu da ƙari, ba a son wuce fiye da awanni biyu zuwa uku sanye da coge ana takawa, domin wuce awanni uku sanye da coge na iya gayyato waɗancan matsaloli da muka ambata a sama, musamman ma tunda fa’idar sa coge ba ta wuce son ƙarin tsayi ko kuma ƙwalisa kawai ba.
 
Daga ƙarshe, idan kina da ƙorafin ciwon tafin sawu ko yatsun ƙafa, tuntuɓi likitan fisiyo (physiotherapist) a yau domin duba ki ko kuma neman shawarwari game da irin takalmin da za a sa don wanyewa lafiya.
May be an image of high-heeled shoes, sandals and text that says 'B 50% 50% 60% 40% 90% 10% Physio Hausa'
 
 
 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author