Ina Neman Ummi Zee-Zee Zan Bata Laƙani, Inji Kwamishiniyar Mata Ta Kano Dr. Zahra’u

Kwamishiniyar mata ta jihar Kano kuma malama mai wa’azi Dr. Zahra’u Muhammad Umar ta ce tana kira ga shahararriyar yar wasan kwaikwayon nan Ummi Zeezee da aka yaɗa labaran cewa ta ayyana cewa zata kashe kanta da ta zo za ta bata wani laƙani.
 
Dr. Zahra'u Ta ce da Ummi Zezee za ta ji da sai kawai ta zo ta sameta su rufe kofa domin ta haƙurƙur tar da ita, domin dai dama duniya ba hutu.
 
Dr. Dahra’u ta kara da cewa "Abin gaskiya ya dameni kuma ina ganin ƴar uwa ta ce mace kuma musulma, ya kamata ni in sameta, ina nemanta ruwa a jallo, ina neman lambar wayarta, zan gaya mata abubuwan da ya dace ta yi a rayuwarta ubangiji shi ne mai komai, da za mu hadu ido da ido zanji daɗi mu zauna da ita". Inji ta
 
Idan ba a manta ba tun a ranar 3 ga watan Afrilu ne dai IDON MIKIYA ta ruwaito muku cewar, Umme Zee-zee ta bayyanawa duniya cewa za ta kashe kanta, saboda damfarar miliyan 450 da ta ce anyi mata.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author