Indai Ba Bala'i Kake Nema Ba Kar Kataho Gurina Da Sunan Allurar Korona-Sheikh Bello Yabo

Babban malamin addinin Islama dake jihar Sokoto a Najeriya, Sheikh Muhammad Bello Yabo ya ce inda ba bala'i kake nema da shi ba kada wani yazo gurinsa da sunan Allurar ragakin cutar korona.

Shehin Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa'azi a garin Sokoto, inda yace shi daman bai yarda da korona ba tun farko kuma shi baya dauke da ita saboda haka bai ga dalilin cewa shi za'a yimar Allurar ba.

Malam Bello Yabo ya ce, shi yana da magabata a Najeriya, domin ga su Gwamnan jihar kogi nan Yahaya Bello, da tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo da kuma dan majalisar wakilai wanda ya fito daga jihar Jigawa Hon Muhammad Nuhu Gudaji Kazaure dukkanin su sun ce basu yarda da cutar ba.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author