Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un: Yanzu wani babban Malami mahaddacin Al-Ƙur'ani ya rasu a Kano

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un

Yanzu muke samun labarin rasuwar Ustaz Alaramma Abdul-Rahman Adam Shu'ibu, wanda ke ja wa Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo baƙi.

Kafin rasuwar marigayin, shine  babban mai jawa Shiekh Dr.  Muhammad Sani Umar  Rijiyar Lemo baƙi a Tafsirin Masallacin Gadon Ƙaya tun daga Shakarar 2009 har zuwa rasuwarsa a yau 2020 kuma shine babban lilamin masallaci Asibitin Makka dake Gadon Ƙaya dake birnin Kano.

 

Bisa sanarwar da Hausa Daily Times ta samu, za a yi Jana'izar Malamin da misalin ƙarfe 1:00pm na ranar yau bayan idar da Sallar Azahar, a masallacin Usman Bin Affan dake  Gadon Ƙaya.

 

Allah ya jiƙan musulmi. Ya karbi baƙwancin Malam. 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles