Izzar so Series Film: Shin ko kunsan nawa Bakori Tv ke samu a youtube kuwa?

Shin ko kun san nawa Bakori Tv ke samu a youtube

Film din dogon zango na Izzar So wanda ke karkashin jagoranci jarumi Lawan Ahmad na daya daga cikin taurarin fina-finan Kanywood da ake kira Blockbuster ma’ana wadanda suka kera sa’a.

Shine film din da bude kofa ga manya da kana nan masana’antun Kanywood suka soma gabatar da shire shirye masu dogon zango a YouTube wanda kuma ake kalla a kyauta.

Biyo bayan Izzar So an ga fina-finai irin su Galaba,Ruhin Mijina,Farmakin So da sauran su to amma sai dai har kawo yanzu Izzar So shine ke jan ragama su wanda kawo yanzu an kalli jerin fina finan guda goma sha tara sau kimanin miliyan tara da dubu dari takwas da saba’in da uku da dari takwas da arba’in da tara (9873849 Views)

Wanda akaf tarihin Youtube Channels da Arewa wannan shine adadi na biyu mafi yawa da wata channel ta samu cikin kasa da shekara daya bayaga YouTube Channel din fitaccen mawaki Hamisu Breaker wadda tasamu views fiye da miliyan 21.

Muhimman abubuwan da film din na Izzar so ya kunsa kama daga tantagar yar soyayya da izza da kuma ilimimantar wane suka sanya miliyoyin mutane ke son kallon film din a koyausheya.

Wanda anyi ittifakin a cikin awanni 24 da sakin kowwani daya daga cikin episode din film din akan kalleshi sau fiye da dubu dari biyar (500k Views)

Makudan miliyoyin naira mahukuntan film din na Izzar so suke kashewa domin samar dashi. Inda suke zakulo fitattun tsofaffi,matasa da kuma jaruman da ba’ama sansu ba wadanda kuma suke dacewa da roll din da ake basu.

Duba da wannan hidima ta kashe makudan kudi da akeyi domin samar da film din mai farin jini wanda kuma ake kallar sa adandalin YouTube kyautane yasanya wadansu ke tambayar to su masu samar da wannan film menene ribar su.

Ta yaya suke mai da kudin su kuma ribar nawa suke samu. To sanin kowwane cewar ba iya mahukuntan Izzar so ba kadai miliyoyin mutane da ake kira Content Creators a turance wato masu samar da bidiyoyin wakoki, karatuttuka (Tutorial) da sauran su daga ko ina a fadin Duniya sun dogara da wannan dandalin na YouTube domin sayar da bidiyoyin nasu kai tsaya ga masu bukata.

Ta hanyar yin abinda ake kira Monetisation wato sanya tallace-tallace a cikin bidiyon wanda ake shigowa a yayin da kake kallo lokaci bayan lokaci abinda ake kira Break ad.

Domin dai ga duk wanda yake kallon Izzar so a YouTube kai tsaye yana ganin biyon iya katsawa tallace na shigowa duk bayan wadansu mintuna kalilan.

To yadda Izzar so ke samun kudin sa shine kasancewar a yanzu tsahon bidiyon nasu iya kaiwa har fiye da minti ashirin (20 Minutes) ga duk wanda yayi playing din bidiyon ya kalla har zuwa karshe za a nuna masa talla akall guda uku (3) zuwa hudu (4).

Wanda kuma duk talla daya idan kakalla to abinda Bakori TV ke samu da kai shine $ 0.01 dala kokuma 0.03 daga ga wanda suke a kasashen waje irin su Amurka da India da ingila da sauran kasashen nahiyar Turai.

Ma’ana dai Bakori TV tafi samun kudi da talla daga masu kallon bidiyon su a kasashen waje. To abin tambaya shine nawa ne $ 0.01 dala da kuma $ 0.03 dala? Dalar Amurka guda daya na a matsayin kudin Nigeria naira dari uku da tamanin da shida (386) to dalar guda daya ana rabata gida darine 100 shine zai baka $ 0.01 dala.

Don haka idan ka raba dari uku da tamanin da shida zuwa gida dari zai baka naira uku da kwabo tamanin da shida (3.86 Kb) don haka duk talla daya da kake gani abinda ake biyan su kenan saboda haka idan kakalli talla 4 daga farkon Izzar so zuwa karshe Bakori TV zai sami naira goma sha biyar da kwabo arba’in da hudu da kai (15.44).

Hakan na nufin idan irinka dubu suka kalla kokuma koda basu kai su dubu ba inda an kalla sau dubu to Bakori Tv zata sami tsabar kudi naira dubu sha biyar da dari hudu da arba’in (15440). Ma’ana wannan shine adadin abinda suke samu duk views dubu 1k views.

To amma sai dai kamar yanda aka fada a farko idan tallace tallacen an kallesu ne a kasashen waje to adadin kudin zaifi fi haka sosai. To amma duk da haka ko a wannan adadin na dubu sha biyar da dari hudu a duk 1k views idan aka kalla sau dubu dari biyar wato 500k views Bakori Tv na samun 15440×500= Miliyan 7720000.

Da wannan adadin ne kuma kiyasi ya nuna cewar a kowwani wata channel din ka iya samun tsabar kudi har dalar Amurka dubu sha uku da dari biyar wato ($ 13.5k) dai-dai da kudin Nigeria miliyan hamsin da biyu da dubu dubu dari biyu da sha daya (531100).

A shekara kuma zasu iya samun abinda ka iya kaiwa dalar Amurka dubu dari da shashida dari da dari daya ($ 116.1) dai dai Naira miliyan dari hudu da da arba’in da takwas da da naira dubu daya da dari shida (4481600).

Wannan ne kuma dalilin da yasanya aka wayi gari wasu bata gari a YouTube dake kokarin samun irin wannan kudi da tashar ke samu suke ta faman satar fina-finan nasu suna dorawa a channel din su. Abinda yasanya shugaban channel din ta Bakori ya saki bidiyoyi har guda hudu a cikin sati biyu yana mai nasiha da gargadi ga masu aikata wannan mummunar dabi’ar da su daina kokuma su fuskanci hukuncin dakatar da channel din su kowwani lokaci daga yanzu.

Sai dai babban abinda yafi ciwa muhukuntan Izzar So tuwo a kwayar yanzu haka shine sanin kowwane film din ya tsayane a Zango na 23 (Episode 23) tun kimanin sati uku kenan kuma har kawo yanzu ba a saki kashi na ashirin ba.

Amma abin takaici shine yadda irin wadancan bata garin ke yada karya agameda cigaban film ta hanyar hada poster da jaruman film din suna kuma nuna rubuta episode 24, 25 har 26 a YouTube Channels dinsu da kuma dandalin Facebook.

Wanda hakance ta sanya Lawan Ahmad yayi gaggawar sakin wata sanarwa wadda ke nesanta Bakori Tv da dukkan wannan episode din da ake ganin wadan can bata gari na sanyawa inda yace ga duk mai son ganin ko Bokori Tv ta cigaba da sakin Izzar so ko akasin haka to yayi subscribe na wannan channel domin dazarar an dora din a sanar dashi.

Zai kuma iya dinga ziyartar channel din a koyaushe domin kauda shakku.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments
Abubakar yahuza - Nov 6, 2020, 4:04 PM - Add Reply

Good Allah taimaka

You must be logged in to post a comment.

You must be logged in to post a comment.

About Author