Jihar Kano Na Bukatar Sanata Barau-Hon Hashim Kabo

Fitaccen dan siyasar nan kana kuma jigo a tafiyar gidan Sanatan Kano ta arewa wato Hon Hashim Sarki Kabo yace, idan Allah ya kaimu shekara ta 2023 ko shakka babu jihar Kano na bukatar mutum gogagge masanin ya kamata irin Sanatan Kano ta arewa wato Distinguish Senator Barau I Jibrin Maliya.

Hon Hashim Sarki kabo ya bayyana hakan ne a yayin hirarsa da wakilin gidan jaridar Globng.com a office dinta dake jihar Kano, a ranar Alhamis 19 ga watan Nuwamban shekara ta 2020.

Hon Sarki Kabo yace, Indai batun kishin al'umma ake yi to shakka babu Sanata Barau I Jibrin Maliya shine (DAN) da jihar Kano take bukata, domin a halin da ake ciki yanzu shine Sanata guda daya tilo da ya fitar da yankin Kano ta arewa daga halin data tsinci kanta a shekarun baya.

Hon Sarki Kabo ya kara da cewa, a cikin shekara biyar dasu ka gabata Sanata Barau I Jibrin Maliya ya samarwa da Kano ta arewa cigaban da bazai misaltu ba.

Hon Sarki Kabo ya lissafo kadan daga cikin ayyukan Sanatan inda yace, Sanata Barau Maliya ya samar da manyan makarantu Universities guda goma sha uku 13 a kowacce karamar hukumar ta Kano ta arewa.

Sannan ya Gina asibitoci, ya Gina kananan makarantun Firamare dana Islamiya, ya rabawa Maza da Mata jari kyauta, ya samar da ayyukan yi ga Matasa,ya raba motoci da mashika da kekunan dinki, ya haskaka kowacce karamar hukuma dake fadin Kano ta arewa da na'ura mai amfani da hasken rana,  ga hanyoyi kai Kace kasar turai kuke yawo.

Sannan duk wata yana rabawa Mabukata kudade dake kowacce karamar hukumar ta Kano ta arewa, domin rage radadin talauci ga al'ummar kananan hukumomin Kano ta arewa.

Daga karshe Hon Sarki Kabo yace saboda irin wannan tarin ayyukan ne yasa jihar Kano take bukatar Distinguish Senator Barau I Jibrin Maliya hasken Kano ta arewa.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author