KAFTIN AHMAD JUNAIDU COMPLETE HAUSA NOVELS BOOK 6

Da asuba tare Junaid da El-Ameen suka fita xuwa masallaci, suna dawowa El-Ameen ya koma yayi kwanciyarsa ya ci gaba da bacci, Junaid yayi murmushi ganin haka, a xuciyarsa yace lallai kam sleep well, toilet ya shiga cikin minti ashirin yayi wanka ya fito ya shirya cikin khakin sa, kamshin turarrukansa ne ya tada El-Ameen, ya mike xaune yana kallon agogo yace "Wai kai barin gari xaka yi haka da asuba ne da baxa ka bar mutum yayi baccin safe ba captain, duk ka ishe ni ka hana ni bacci don xaka aiki" Junaid na saka wristwatch dinsa yace "sorry, go back to ur sleep, ni yanxu ma xan bar maka dakin" Yana fadin haka ya dauki wayarsa da hularsa ya nufi kofa, El-Ameen yace "Wait, wai Karfe nawa yanxu?" Junaid yace "6:40" daga haka yace "May be ka same ni part din Mumy in ka fito da wuri" El-Ameen yayi tsaki shi kuma yayi ficewarsa. Har El-Ameen ya koma ya kwanta ya mike da sauri tunawa da yayi akwae alluran da yake ma patient dinsa bakwai da rabi. Toilet ya shiga yayi wanka a gurguje ya fito, cikin mintunan da basu wuce goma ba ya kintsa cikin blue shirt da black jeans a closet din junaid, ya feshe jikinsa da turare ya dau wayarsa ya fice daga dakin, yana isa part din Mumy suka kusa cin karo da Humainah xata fito, ae da sauri ya sunkuyar da kai ya bata hanya ta bi ta gefensa tayi gaba abunta, ya sauke ajiyar xuciya ya shiga parlon, ko kallon Junaid dake xaune yana shan tea bai yi ba, ya gaida Mumy ta amsa tace "ga breakfast dinka can a dinning" yace "A'a Mumy sauri nake wlh, idan naje office xan yi" Mumy tace "Kan ka daya kuwa, Karfe nawa yanxu da baxa ka tsaya kayi break ba" kallon agogo yayi yace "Mumy wllh am in a haste ne..." junaid dake kallonsa yace "Da wannan surutun da yanxu ka gama hada tea" hararan sa yayi sannan ya karasa kusa da shi yayi kasa da murya yace "look akwae wani injection da xan ma patient dinka ne b4 7:30, shi yasa nake sauri," da sauri Junaid ya kalli Mumy dake kallonsu yace " Ohh Mumy ashe emergency aka kira sa ne fa" Mumy ta tabe baki tace "Kwa ji da gulmar ku ba ruwana" El-Ameen ya d'an yi murmushi yace "Ko xuwa Karfe goma xan dawo inyi wllh Mumy" Mumy tace "Ka fa rantse" dariya yayi yace "in'sha Allah Mum" mikewa Junaid ma yayi ya shiga bedroom din mumy ya dauki kardigan dinsa yasa don garin da d'an sanyi, ya fito yace "Mumy sai na dawo" ta bisa da kallo kafin ta tabe baki tace "Toh dai kar ka manta ku shiga kuyi wa Hajja sallama don yau xata tafi, ko Abba ma baku shiga kun gaida ba bare mutan gidan" Junaid yace "Xamu shiga" daga haka suka fita daga parlon, sae da suka fara shiga part din Abba suka gaida shi sannan suka yi part din Hajja, tana ta hada kaya, Humainah na xaune gefenta sai rusa kuka take ita ma da tata jakar a gefenta, Hajja na mata ruwan bala'i tana cewa tayi kadan ta koma da ita tunda dama ba ita tace ta biyo ta, xamanta daram a gidan ko suma take, Junaid ya fashe da dariya yana kallon Humainah, ita ko tana ganinsu ta hadiye kukan ta sunkuyar da Kai kasa, Hajja tace "Atoh, ka dai gan ni da gantalalliyar nan wae sae ta bi ni Amadi, sae kace ance mata wahalalla nake kamar irin ni na ce ta biyo ni din nan shegiya, nufin ta in koma da ita muna galallawa a titi, to dadin abun dai ba kudin banxa gare Muhammad ba, kuma ubansa Ahmad bae ce yaje xae gani ba bare ya biya kujeru biyu na jirgi" Junaid ya dinga dariya yana kallon Humainah, El-Ameen yyi murmushi ya gaida ta, ta kallesa ta gefen ido ta ci gaba da abinda take ba tare da ta amsa ba tana ci gaba da yi ma Humainah masifa, dariya yayi yana shafa kansa don yasan me yasa bata amsa ba, Junaid ya ciro dubu talatin da ya tanadar mata dama ya ajiye gabanta yace "Gashi ni da El-Ameen ki sha ruwa da dabbino a hanya kar ki je kina masu amai a jirgi" ta washe hakora tana kallon El-Ameen tace "Toh Allah maku albarka, ga kuma amanar jikata a hannun ku, don mayu sun yi yawa gidan, Amina na damka ma ita, tamkar yanda xata yi ma fatima xata yi mata" Junaid yayi murmushi yace "In'sha Allah" Hajja ta kara da cewa "Kuma ga maganin tsari kala kala can na kai ma uwarka idan taga dama ta baka, ka kuma sanma marowacin abokin nan naka don duniya bbu gaskiya yanxu, barin kai da kiri kiri matan ubanka ke nuna basa sonka" shi dai El-Ameen sae kallon agogo yake don bai son lkcn nan ya wuce duk hankalinsa yayi gun patient dinsa, Junaid yace "Toh Hajja" kallon Humainah yyi ya mike yace "Ae sae ki dauki jakar ki kai bangaren Mumy" ta fashe da kuka, Hajja tace "Tashi ki ban waje yar wahala, bbu inda xani da ke ki xauna gidan wan ubanki don shi xaki gani ranan gobe kiyama" Humainah na kallon Junaid cikin kuka tace "Ya Ahmad kace mata don Allah ta tafi dani wllh bana son in xauna gidan nan kullum fada ake yi" Hajja tace "A haka xaki saba ki koya ki iya kema" Junaid ya fice yana dariya ta bi bayansa da sauri, El-Ameen ya kuma yi ma Hajja sallama ya fice shi ma yana danne dariyarsa wai kullum fada, sae da suka fito compound Junaid ya kama hannunta yace "kinga ki bari ta tafi sai in maida ke next week I promise" da haka ya lallabata tayi part din Mumy tana kuka, Umma na daga balcony dinta xaune haka ma Hajiya kamar masu cin kasuwa kuma duk don sbda sa ido suke yin haka, ko kallonsu bai yi ba yayi gun motarsa, El-Ameen ma bai kalli idan suke ba ya bi bayansa, duk suka bi su da kallo ko wanne da tunaninta a xuciya, El-Ameen ya kwace key hannun Junaid ya shiga driver seat ya tada mota, Junaid yayi murmushi ya xaga daya side din, yana gama ba motar wuta ya ja suka har compound din bayan masu gadi sun bude gate, gudu kawae El-Ameen ke shararawa, Junaid yace "Wae lafiya wannan gudun Ahmad" ko kulasa bae yi ba, Junaid yace "Look kar kaje ka kashe ni ma uwata a banxa, wannan ae hauka ne are we flying, plss ka tsaya in sauka" nan ma dai bae kulasa ba sai da ya gansa a kofar gidansa yana kallon agogo yaga bakwae da minti ashirin, yyi ma junaid wani kallo yace "you heard me ryt daxu amma" daga haka ya bude motar ya shiga gidan, Junaid ya kalli agogo ganin da sauran time ya fito ya nufi cikin gidan shi ma, bbu kowa parlon sai kamshi dake tashi Mama Jummai ta tsaftace ko ina, daki El-Ameen ya nufa, ya tsaya daga bakin kofa bayan yayi sallama yana kallonsu, tana xaune gefen gado Mama jummai na packing mata gashinta, ta gama shiryata tsaf cikin doguwar rigar kanti sea green da stones gold colour a jiki, tun daga nesa kana iya ganin white eyeballs dinta sbda uban kwallin da mama jummai ta sa mata, wanda hakan ya kara fito da kyan idanuwan nata, kallonta kawae yake sannan ya shigo dakin, Mama jummai na murmushi ta gaida shi tace "Na ma yi xaton baxa ka xo yau ba ganin har lkcn xuwan ka ya wuce" murmushi yayi yace "Na makara ne mama" ta mike daga durkushen da take tace "Bari in hada mata abinda xata ci" daga haka ta fita, ya karasa kusa da ita ya duka yace "Morning" kallonsa kawae take, sai kuma ta dauke kanta, mikewa yayi da sauri tuna lkci na wucewa ya nufi gun alluranta, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata, xuwa yanxu ta fara hakura ta tsaya yayi mata alluran ba gardama, dagota yayi suka fita daga dakin yana rike da hannunta, Junaid na xaune parlor suka sauko ya bi su da ido, tsakar parlon El-Ameen ya xaunar da ita kan rug, Mama jummai ta fito daga kitchen rike da bowl din pap tace "Kaga jiya da rana na dama kunu ina sha naga tana tana kallonsa sai na bata ae ko tasha, kuma da yawa ta sha, shiyasa ma yanxu nayi mata" El-Ameen yace "Ohk" xaunawa Mama Jummai tayi kusa da ita ta fara bata, sau biyu ta sha ta fara kokarin amshe spoon din hannunta, shi dai Junaid kallonsu kawae yake, El-Ameen ya karbe spoon din hannun Mama jummai ganin ta dage sai ta karba yana mata wani irin kallo, lkci daya ta nutsu, da kansa ya shiga diban pap din yana kai mata baki tana bude bakin tana amsa, Mama jummai tayi murmushi ta Mike ta bar parlon don xuwa ci gaba da aikinta, cokali hudu kadai ta karba ta dauke kai, ya hade rai ya dafa kanta ya kai mata pap din spoon din baki, da kyar ta bude bakin ya xuba mata tayi saurin maido shi spoon din, wani tsawa ya mata, lkci daya jikinta ya dau rawa ta bude baki ya kuma maida mata ta hadiye, sake diban wani yayi ya bata taki karba yace "I will slap you fa" bata fuska tayi tana komawa baya a hankali, murmushi yayi yana kallonta, sai kuma ya lumshe ido ya kai kunun bakinsa ya sha, da sauri ya bude ido ya juya yana kallon junaid yaga kallonsa kawae yake. Jefar da spoon din yayi cikin pap din duk ya daburce yace "I I didn't even realize wat I was doing faa, hankali na duk baya wajen" ya runtse ido yana yamutse baki da fuska yace "So irritating" Junaid ya tabe baki ya mike ya dau wayarsa da makullin motarsa dake ajiye kan kujera ya fice daga parlon, El-Ameen ya bi sa da kallo, ita ko daukar spoon din tayi ta juya shi upside down cikin pap din ta debo ta Kai masa baki, murmushi yayi yana kallonta ya kauda Kai, ai ko ta xuba masa a kan hanci ta kuma debo wani xata kai hancin ya rike spoon din yana dariya yace "Keee" kokuwa suka shiga yi ita fa sae ta sa masa a hanci ta wani hade rai, da sauri ya bude baki sae ta xuba masa d'an kunun da ta debo ciki, ya lumshe ido ya shanye Sannan ya dauke bowl din ya boye a bayansa, xata mike ya komar da ita ya xaunar yace "C'mon"


Mama jummai ta shigo palon rike da bucket tace "Har ta shanye?" Yace "A'a barnatar da shi xata yi shi yasa na boye, ta koshi kuma" mikewa yayi ya dauke bowl din yace "Xan tafi yanxu, sai na dawo anjima mama" ta karba bowl din tace "Toh Allah ya tsare" daga haka ya ja dogon hancinta yayi hanyar kofa, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa, Mama ta saka dariya tace "Au, toh gashi xata bi ka" juyawa yayi da sauri yana kallonta ya galla mata harara yace "I will knock you idan kika xo nan" kamar ta ji me yace ta tsaya tana cixgar stones din rigarta tana kallonsa, ya juya ya fice daga parlon, mama jummai ta karaso ta kama hannunta suka koma cikin parlour'n. El-Ameen na fita ya rike waist a waje tunawa da yayi ai ba mota kuma bbu kudi hannunsa, tsaki yayi ya nufi main road da kafa ya tsayar da adai daita ya gaya masa anguwarsu, suna isa yace yana xuwa sannan ya shiga ya fito masa da kudi ya basa ya koma ciki, Ummi dake parlor sai binsa da kallo take bayan ta amsa gaisuwarsa tana ganin ya nufi daki tace "Xo nan Ahmad" komawa yayi ya xauna kasa yana kallonta yace "Gani Ummi" tace "Ina kake xuwa this dayz baka xaman office?" Ya d'an sosa kai yace "Ummi, dama... To wai Ummi wa yace bana xama office ni da kullum sai na je clinic" Ummi ta galla masa harara tace "Am not joking Ahmad, wannan sabon salon da ka tsiran ma rayuwarka ba fishshe ka xai yi ba don b'ata ma mahaifin ka rai kawae kake" ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, Ummi tace "Magana ta biyu kuma tunda kai ka kasa fito da mata toh ni na xabar maka...." Da sauri ya D'ago kai yace "Ummiii!" Tana masa mugun kallo tace "Ehh, ni ma xan rakaka gidansu yarinyar da kaina in ma ya kama ni xan maka maganar sai inyi, kuma ba wata bace facce 'yar abokin Abban ka Fiddausi" wani xufa ne ya shiga keto masa duk ya ma rasa abinda xae ce, da sauri yace "Ummi ni fa na riga da na samu yarinyar da nake so" Ummi na hararansa tace "Wannan kuma ba matsala ta bace, sai dai kuma ka raina ma kanka hankali ba ni ba" ya marairaice mata yace "Ummi Allah kuwa da gaske, a gidansu junaid ma take" Ummi tace "Wacece kenan?" Yayi kasa da kai a hankali yace "Humainah take ko wa? kuma niece din Junaid ce" Ummi tayi shiru tana hararansa yace "Allah kuwa Ummi, naji kamar ina sonta" tace "Toh ae xanje gidansu junaid din kuwa" bai kuma cewa komai ba sai tunani yake anya gskya ya fadi ma Ummi kuwa, can dai ya mike yace "Bari in tafi office Ummi", tace "Allah ya tsare"

Karfe Hudu saura Junaid yayi parking kofar gidan El-Ameen ya fito, ya koma back seat ya cire hularsa ya ajiye da rigar khakinsa ya dauki well ironed shirt dinsa dake bayan mota don bae rasa mofti a motar ya saka sannan ya fito ya shiga gidan, Mama jummai na share parlor ita kuma tana tsaye jikin bango kamar xata shige ciki, Mama jummai tayi masa sannu da xuwa, ya amsa tare da gaisheta hankalinsa na kanta, Mama jummai tace "ka ganta can tafi awa biyu tsaye taki xaunawa" murmushi yayi ya karasa inda take tsaye, ya kama hannunta suka dawo parlorn ya xaunar da ita, ya rike chin dinsa da duk hannunsa biyu yana kallonta ita ma kallon nasa take, fine beard din da ya xagaye bakinsa ta kai hannunta ta taba, yayi murmushi ya kama hannun cikin nasa yana kallon manyan fararen eyeballs dinta cikin sanyin murya yace "I will call you Jasmine! Do you like dat?" Kwace hannunta tayi daga nasa, ya tsura mata ido, bude kofar parlor aka yi El-Ameen ya shigo, ae tana ganinsa ta mike da sauri ta nufesa ta isa gabansa ta tsaya, Junaid ya bi ta da kallo, El-Ameen ya ja hancinta ya bude hannayensa yace "toh dai bbu abinda na siyo maki" kallon junaid yayi yace "The great Capt Ahmad Junaid ashe kana nan" mikewa junaid yayi yace "Sure!" Daga haka ya nufi kofa, El-Ameen yace "ba dai har xaka tafi ba" junaid yace "Yea daga office nake" daga haka ya fice daga parlorn, bin sa da wani irin kallo El-Ameen yayi kafin ya fita yayi saurin cewa "Hey a minute" junaid ya tsaya sannan ya juya yana kallonsa, El-ameen yace "gaskiya ya kamata ka shiga kasuwa ko kuma ka bada kudi a shiga a sama mana TV a gidan nan, ko ka mance yanda muka yi da kai?" Junaid yace "I will transfer the money later sae ka samu me siyo maka TVn" yana gama fadin haka ya fice daga palon, El-ameen ya d'aga kafada ya kama hannunta suka koma parlor.As usual ya dade xaune mota bayan yayi parking a lot din gidansu kuma har lkcn bae kashe mota ba yana danne dannensa a waya, Khadija ce ta fito daga part dinsu ta karaso gun motar ta bude tace "ina yini yaya A.jay" ya kalleta yace "Lafiya lau" ta d'an marairaice masa tace "yaya yau ciwo ciki na ke min wllh" tabe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, ta dan shagwabe masa tace "Yaya ka d'an ban kudi in siya magani mana, Umma ta ki bani" dubu daya ya xaro aljihunsa ya mika mata cike da murna tayi masa godiya ta kara gaba, shigowar motar Suhaima yasa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya fara tafiya, Hajiya ce suka fito daga part din Umma da wata mata alamar rakiya xa su mata, duk suka bisa da kallo, ba tare da ya kallesu ba ya gaida su don dama sai lokacin da yayi suit dinsa yake gaishesu, matar ce kadai ta amsa shi, bae damu da haka ba yayi part din Mumy, Matar da ta bisa da kallo ta maido da dubanta gun su Umma murya can kasa tace "Shine yaron hala?" Cike da tsanarsa Hajiya tace "Ehh wllh" matar tayi wani murmushi murya can kasa tace "Duk ku kwantar da hankalin ku, ku bar min komai a hannu na baxan baku kunya ba" babu wanda yace komai cikinsu suka rakata har waje gun motar ta. Junaid na shiga parlon Mumy ya tarda Humainah kwance da ganinta kasan ba kuka kadan tayi ba, dariya ya saka yace "ohh shikenan an bar mana ita" mikewa tayi xaune idon ta ya cicciko ta kwalo ma Mumy kira, Mumy ta fito daga daki tace "be careful Mr" dariya yayi yana shafa kai yace "Ya hakuri Mumy, ina yini" ta karaso parlorn tace "Nayi xaton ae baxa ka kashe motar ka shigo gida ba" yyi murmushi yace "Ac fa nake sha Mumy" ta tabe baki tace "Haka ne, ga abincin ka can" kujera ta xauna tana kallon Humainah tace "Kema kije ki dau naku abincin ke da fatee, ko baki hakura ba har yanxu" bata ce komai ba tayi kasa da kai, Junaid ya mike yace "Xan dawo Mumy bari inyi wanka" tace "Ohk," bin sa da kallo tayi sae da ya kai bakin kofa tace "Canxa kaya kayi office" murmushi kawae yayi ya fita. Wanka yayi ya kuma canxa kayan jikinsa yyi kwanciyarsa parlor don bai jin yunwa, ya kusa awa daya kwance Humainah ta shigo parlorn rike da tray dauke da abincinsa, ta karaso ta ajiye masa, ya mike xaune cike da xolaya yace "Shikenan fatima ta huta an kawo mana maid kyauta" mikewa tayi a fusace xata fita ya rikota yana dariya yace "Ke dalla wasa nake maki" ta fixge hannunta tace "Bana son wasan" ya daga kafada yace "Ni kuma sai nayi din" wani kallo ta shiga yi masa fuska daure, ya hade rai yace "Toh in kince a biya ki kudin aikin ba sai a biya ki ba ma" hawaye ya cika idonta ta juya xata fita aka bude kofa El-Ameen ya shigo da sallama, da sauri ta kuma juyawa tana kallon Junaid da ya bude ido ganin El-Ameen da ya kasa Karasowa cikin parlorn, Junaid ya mike yana dariya yace "C'mon ka karaso frnd" El-Ameen yace "Um ban gaida Mumy ba am coming" da sauri junaid ya karasa ya rufe kofar da key ya cire sannan yace "ba ta kofarta ka wuce ba kafin ka karaso nan" El-Ameen ya ma rasa me xai ce masa, dawowa cikin parlorn junaid yayi ya xauna yana kallon Humainah yace "Toh ae sai ki goge hawayen yanxu tunda ga shi ya xo koh, duk kin isheni kin daga min hankali ina El-Ameen toh ga ki ga shi" Humainah tayi wani kara ta durkushe wajen ta shiga kai masa duka tana cewa "ni bana son haka ya Ahmad, bana so" El-Ameen yayi murmushi ya nufi daki, da sauri Junaid ya mike ya rigasa shigewa dakin ya saka key daga ciki yace "Ji min munafukai" gajiya yayi da tsayuwa ya dawo parlorn, can nesa da ita ya xauna yace "Ina yini" ta d'an kallesa ta hade rai tace "Lfya lau" bai kuma cewa komae ba ya dau remote yayi powering Tv, sun kusa minti talatin parlorn bai ce mata ba bata ce masa ba, kamar wanda ya tuna abu ya mike da sauri yana kallon agogo ya nufi dakin junaid ya kwankwasa yace "Look captain akwae drugs din da xanje in ba patient dinka open the door plss ka bude kofar parlor am leaving" junaid dake kwance ya fara bacci ya mike jin abinda El-Ameen yace ya bude kofar, El-Ameen yace "D'an rainin wayo bacci ma kake koh" fitowa junaid yayi suka dawo parlor a tare, kallon Humainah yayi yana murmushi yace "Har kun gama xancen kanwata" ta hararesa ta dauke kai, shi kam El-Ameen har ya kai kofa, Junaid yace "toh dai ki ajiye abinda ya baki idan na dawo mu raba, kuma ki d'an gyara min bedroom saura ki min satan turare ki ga ko ba na saurayin ki xan je in sace ba" yana fadin haka yyi kofa ya bude ya fice yana dariya, El-Ameen ma ya fita, Part din Mumy suka shiga El-Ameen ya gaida ta, Junaid yace "Xan d'an rakasa indawo yanxu Mumy" Mumy tace "Toh sai ka dawo" daga haka suka fice da El-Ameen. suna isa El-Ameen yace "Baka yi min transfer din kudin Television din ba fa, if you provoke me xan fa je in siya da kudina" Junaid yace "I forgot xan yi" fitowa suka yi daga motar suka shiga gidan, Mama jummai na xaune parlor ta daura kanta kan cinyarta idonta rufe, El-Ameen yace "dama tana bacci ba da daddare ba" Mama jummai tace "Ina jin bata jin dadi ne yau, sau biyu tana amai ga jikinta da dumi, ita da ko xama bata yi da rana bare ta kwanta" El-Ameen ya karasa ya durkusa gabansu ya d'ago kanta ta bude ido tana kallonsa, ya gyara mata gashinta a hankali yace "Malaria... I guess" xaunawa Junaid yayi shi dai bae ce komai ba, El-Ameen ya d'agota ya xaunar da ita kan kujera yace "Sorry...." Ya kalli Junaid yace "Ka bada kudi in tafi in siyo mata drugs da injections" kallonsa kawai Junaid yake bai ce komai ba, El-ameen ya kalli mama sannan ya kallesa ya juya xuwa harshen turanci yace "It's not a matter of looking at me dat way captain, don't forget she's ur patient, ur mind agreed to the terms nd condition of helping her, nd I guess before u jumped into the conclusion of doing dat, you already know...." Katse sa junaid yayi yana masa wani kallo yace "did you hear me complain?" El-ameen yayi dariya yace "Not dat I don't have the money to assist you but...." Tsaki Junaid ya ja yace "Enough plss, I don't even need ur goddam help," El-ameen yayi murmushi yace "Ni kuwa kake bukatar taimakona, cos lokacina da na ware for her is far far better then dat money you are spending, anyway! 20k will do for the test nd everything" Atm junaid ya ciro ya mika masa ya karba, ya mike ya haura sama syringe ya dauko a daki da plastic tube na drip ya dawo parlon, da kyar ta bari ya debi jininta don sae da Mama jummai ta riketa, ya mike yace "Bari in je in dawo yanxu, Mama ki d'an bata kunu ko kadan ne ta sha" Mama tace "Toh" sannan ya fita daga parlorn, xamowa tayi daga jikin mama ta kwanta kasan tiles, mama ta d'agota tace "Sannun Kinji Baiwar Allah, Allah ya sauwake maki" kara ta saki alamar bata son tashi a kasan, Mama ta kyaleta ta tafi kitchen, mikewa Junaid yayi ya isa gabanta ya durkusa, kallonsa kawae take kafin ta kauda kanta, ya d'agota a hankali yace "Sorry Jasmine, get well soon" mikewa tayi ta kwace hannunta a nasa ta fara tafiya, ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya, can jikin bango taje ta tsaya, ya mike ya koma kujera ya xauna, har mama ta fito kitchen rike da pap bata bar jikin bangon ba, Mama ta ajiye bowl din hannunta ta karasa ta kamo hannunta, da kyar ta biyota suka dawo parlor ta xaunar da ita ta shiga bata kunun amma taki sha, da ta takurata mikewa tayi ta dawo kusa da junaid ta xauna gefen shi ta jingina jikinsa ta rufe ido gam, duk tayi wani laushi da ganinta kasan bata da lafiya, shi kam kallonta kawae yake wani tausayinta ya dinga ji, ya ji dama ciwon ya dawo jikinsa, ya rungumota jikinsa a hankali yace "Sorry My Jasmine" mikewa mama tayi ta mika masa kunun tace "Toh ka bata Junaid kila ta karba ko kadan ne" yyi murmushi ya karba ya janyeta daga jikinsa ta bude ido tana kallonsa, ya debi kunun kadan ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, rasa yanda xae yi ya bata yayi, kawae ya ajiye, ita ko ta sauka kasa ta kwanta, bayan minti goma El-Ameen ya shigo parlorn, ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yana kallon junaid yace "Ta sha kunun" girgixa masa kai kawai yayi, El-Ameen ya jawo bowl din kunun ya debo ya kai mata baki, ta kauda kae da sauri, ya hade rai yace "I will knock you, c'mon bude baki" kara ta saki ya xuba mata kunun a baki ta xubar da sauri, ya daka mata tsawa, nan da nan jikinta ya dau rawa ya debi wani ya bude bakin ya xuba mata, da kyar ta hadiye hawaye na sakkowa idonta, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, haka El-Ameen ya dinga bata tana karba da kyar har tayi four spoon sannan ya ajiye, ya fara hada drip da xai sa mata da alluran da xai mata, ita ko kwanciya tayi kan tiles ta rufe ido, yana gama hada alluran ya D'ago ta ta bude ido, gown din jikinta ya d'aga don a lap xae mata alluran, kallon junaid yayi yaga idonsa na kansu, da sauri junaid ya kauda kai, El-Ameen ya kwantar da ita yayi mata alluran, tun bai gama ba ta fara kokarin mikewa, duk jikinta yayi xafi ba kadan ba, ya maidata ya kwantar har ya gama sannan ya dagota yace "Sorry" komawa baya kawae take hawaye na xuba idonta, El-Ameen ya d'an yi murmushi don hawayen shaidar wataran xata dawo me hankali ne sai dai fatansa daya kar tayi loosing memory dinta, kusa da junaid ta koma ta xauna gefensa ta daura kanta a kafarsa ta rufe ido, yana son ya lallasheta duk da yasan ba gane nufinsa xata yi ba amma bae son yin hakan gaban El-Ameen ya ya kafa masu ido, hakan yasa ko kallonta bai yi ba, El-Ameen yayi murmushi ya mike ya nufi kitchen don dauko cup yyi mata diluting drugs ya bata ta sha, Junaid ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace "Sorry Jasmine...." Ta bude idonta da suka sauya launi tana kallonsa, da sauri ya D'ago jin fitowar El-Ameen, ko kallonsu bai yi ba yi diluting drugs din da ruwa ya dawo kusa da su ya xauna ya dagota yace "Tashi ki sha magani" kara ta saki ta boye fuskarta jikin junaid tana shishshige masa kamar xata shiga jikinsa, El-Ameen ya mata wani tsawa, jikinta na rawa ta rike Junaid tana ihu, janyeta El-Ameen yayi ya hade rai yace "Keehh" cup din ya kai bakinta ta ki budewa, ya mata wani rankwashi ta kwala ihu, da sauri ya jawota ya juye maganin bakinta ya rufe hancinta, sae da ya tabbatar ta shanye su gaba daya sannan ya cire hannunsa hancinta, lkci daya duk ta amayo maganin jikinsu gaba daya su ukun, daga nan ta dinga amai gashi bata ci komai ba, El-Ameen ya mata wani tsawan da ya rikitata ta fasa ihu xata mike ya fixgota da karfi ta fado kansa ya rungumeta tsam jikinsa, sunkuyar da kai junaid yayi jin wani abu da bae taba ji ba a xuciyarsa a lkcn, a hankali ya shiga cire shirt din jikinsa da ya baci da amai, Mama jummai dake tsaye daga bakin kofa cike da tausayinta taji kamar tayi mata hawaye duk ita ma jikinta yayi sanyi, mikewa junaid yayi har lkcn bae kallesu ba ya haura sama, El-Ameen ya bi sa da kallo, a hankali ya d'ago kanta jin ta sakar masa jiki gaba daya ya ga bacci tayi, kamar me rada yace "Jewel!" A hankali ta bude ido tana kallonsa.
El-Ameen ya sakar mata murmushi murya can kasa yace "Sorry!" kauda kai tayi, ya mike ya d'agata suka tafi sama, bin bayansu mama jummai tayi, yana shiga daki ya xaunar da ita gefen gado ya xauna gefen gadon shi ma yana cire shirt din jikinsa Junaid ya fito daga bayin rike da shirt dinsa da ya wanke, ko kallonsu bai yi ba ya fice daga dakin El-ameen ya bi sa da kallo, yana sauka downstairs ya dau makullin motar El-Ameen ya fice daga gidan. Gida ya tafi, yana gama parking ya fito rike da shirt din nasa ya nufi part dinsa, su Hajiya dake xaune tsakar gidan suka bi sa da kallo ganin daga shi sai singlet da jeans, bae ko kallesu ba ya bude kofa ya shiga parlornsa ya rufe, kallon juna suka yi tare da tabe baki, bathroom Junaid ya shiga ya sakar ma kansa warm shower, ya fito daga karshe ya shirya cikin jallabiya duk jikinsa ba kwari ya kwanta har lkcn bae ji xuciyarsa ta dawo dai dai ba. Kiran magrib yasa shi mikewa ya fita xuwa masallaci, Yana dawowa mosque ya shiga part din Mumy, Humainah ce kadae xaune parlor tana kallo, ya xauna fuskarsa daure yace "Mumy fa?" Ta tabe baki ta dauke kai, bae kuma cewa komai ba har Mumy ta fito tace "Har ka dawo" ya shafa kansa a hankali yace "Eh Mumy" tace "ga abincin ka can, na daxu ma baka ci ba sai dawo da shi Humainah tayi" xae yi magana aka bude kofa Sadiya ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tana taunar cingam tana kallon Mumy tace "Wae Abba a kira ki!" Mikewa junaid yayi yace "Ke don uwar ki baki iya sallama bane xaki shigo ma mutane parlor kamar dabba" Mumy ta hade rai tace "Ahmad!" Wani mugun kallo yake mata xuciyarsa na tafarfasa, ita ko ta tabe baki ta kauda kai tana murgurda baki, wani tsawa ya mata ya nufeta Mumy ta fixgosa tace "Xan saba maka wllh Ahmad, kana da hankali kuwa" Sadiya tayi tsaki ta fice daga parlon fuu, cikin bacin rai yace "Mumy ko gaisheni fa 'yar iskar nan bata yi a gidan nan yanxu, ni din sa'anta ne" Mumy tace "Sae me don bata gaishe ka ba, uwar me gaisuwarta xae kara maka, ko da can gaishe kan take idan ba gulma ba, kaje an bata maka rai a waje xaka xo ka huce ma mutane a gida, ina raba ka da mutanen nan baka ji koh Ahmad, dole ne sae ka tanka duk abinda suka yi" shiru yayi bae ce komai ba ya koma ya xauna ya rike kansa don shi kansa bai san me yasa yayi hakan ba, he just don't know what came over him, don da can ma ba gaishesa step sis din tasa take ba kuma bai taba ce wa komai ba, Mumy tayi kwafa ta dau hijab dinta ta fita. dawowa kusa da shi Humainah tayi ta xauna kasa a hankali tace "Kayi hakuri ya A.jay, nima daga yau baxan sake gaisheta ba, shikenan na rama maka" kallonta kawae yake bai ce komai ba, sai kuma ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idonsa, ta bata rai tace "Shine ka min shiru koh" ba tare da ya bude idon ba yace "Anki maki maganan, ke din gaishe ni kike?" Mikewa tayi ta take kafarsa ta nufi daki tana cewa "Idan ba sai na gaisheta ba gobe me nake!" ya bude ido da sauri ya bi ta da kallo yana murmushi, Bayan kusan minti talatin Mumy ta dawo parlor, junaid ya mike ya dawo gefenta ya xauna a hankali yace "Kiyi hakuri plss mum I don't know what came over me, baxan sake ba wllh" tace "It's ohk" daga haka bata kuma cewa komai ba shi ma haka, bayan kusan minti goma yace "Mumy fushi kike da ni I know, don Allah kiyi hakuri plss" ta girgixa kai cike da takaici tace "uhn naxari kawae nake ne Ahmad, kaji inda yan gidan nan suka kuma bullowa wae duk me girki shi xae yi girkin gidan gaba daya yanxu, sae kace da can basu suka ce kowa yayi nasa ba, ko me suke nufi da hakan kuma oho" junaid ya d'aga kafada yace "Sai su ci kayansu ai, don ni baxan ci girkinsu ba" daga haka ya mike ya nufi dinning, Mumy tayi murmushi a xuciyarta tace "Ae dama baxan ma bari kaci abinda ya fito daga bangarensu ba idan Allah ya yarda"Kwata kwata Junaid bai runtsa daren ranan ba ya rasa dalili, sae dai yafi danganta haka da tausayin baiwar Allahn da yake, Washegari Wednesday bai yi wani breakfast din kirki ba ya fita as early as 7, tun daren jiya El-Ameen ke kiransa baya dauka, a hankali yake driving ya kalli wrist watch dinsa yaga bakwae da minti goma, ganin yana da sauran time yasa shi nufan gidan El-Ameen, a waje yayi parking ya shiga gidan, kwance ya tarda El-Ameen a parlor yana bacci kan 3sitter, Mama kuma na kitchen, ya kusa second ashirin tsaye yana kallonsa sannan ya tabe baki yyi hanyar stairs, a hankali ya tura kofan dakin ya ganta kwance kan gado cikin bargo, ya karasa cikin dakin yana kallon empty roban drip din da aka cire mata, gefenta ya tsaya ya yaye bargon jikinta, ya tsura ma fuskarta ido, Ya fi minti biyu yana kallonta tana bacci, ya daura hannunsa a hankali a forehead dinta ya ji da d'an dumi, bude ido tayi da sauri ta mike xaune, kallonsa take ko kiftawa bata yi, lkci daya ta saki wani kara ta shiga komawa baya tana ihu da karfi, ya koma baya da mamaki yana kallonta, El-Ameen ne ya shigo dakin da sauri, ya tsaya daga bakin kofa ganin Junaid a dakin, sauka tayi daga kan gadon tayi kofa da gudu xata fita tana ihu har lkcn, El-Ameen ya fixgota yace "Keeh Meye haka!" Ihu ta dinga yi xata kwace kanta tana yi tana waigan Junaid, El-Ameen ya kalli Junaid yace "Ohhh it seems Khakin nan naka ke tsoratata fa Captain" Junaid ya juya yana kallon kansa a madubi, farin well ironed navy shirt ne jikinsa, well tucked in cikin navy blue trousers dinsa, sae hat dinsa a kai, sae black socks din dake kafarsa don ya cire takalmin a waje, juyawa yayi ya fice daga dakin, sai a sannan tayi tsit sai dai har lkcn jikinta rawa yake tayi lamo jikin El-Ameen, El-Ameen yayi dariya yace "Toh fah" xaunar da ita yayi gefen gado yana kallonta yace "That's intresting! kina tsoran soldiers kenan!" Kauda kai tayi ta xamo kasa ta kwanta, mikewa yayi yana kallon agogo, da sauri ya fita dakin ya sauko parlor sai dai bai ga junaid ba, ya kalli Mama dake shara yace "Mama junaid din ya tafi ne?" ta washe baki tace "Anya ya tafi, kaga makulli can ya ajiye kan kujera, ashe sojan ruwa ne yau na gansa da khaki" Dariya El-Ameen yayi yace "Ehh Navy ne" tace "Allah sarki, khakin sun masa kyau" kallon Makullin yayi yaga ta motarsa ce, ya d'an tabe baki ya karasa ya dauka yace "D'an rainin wayo" fita yayi don ganin ko motar tasa na waje yaga bbu motar makullin kawai ya kawo masa, girgixa kai yayi ya koma cikin gidan. Junaid na kwance parlor da yamma b4 magrib yana danne dannen waya, khadija ta shigo parlorn, Karasowa tayi ta xauna gefensa tace "Ina yini ya A'jay?" Yace "Lfya lau, kar ma ki fara tambayata kudi don bani da" dariya tayi tace "Kai yayana" sai kuma ta d'an yi shiru, a hankali tace "Kasan me yaya, karka ci abincin gidan nan yau, just go out and get somethin to eat ae kasan yanxu an daina girki daban daban koh" yana kallonta yace "Why!" Ta daga kafada tace "Just, beside ma porridge ne kuma ae bama ka ci" mikewa tayi tace ina xuwa, ta fice daga parlon, ya bi ta da kallo yana murmushi. Wayarsa ne ya soma ring ya duba ya ga El-Ameen ke kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne bai ce komai ba, daga daya bangaren El-Ameen yace "You try fa captain, nine ban san dadin gidanmu ba ko, how on earth xaka dinga bari na ni kadai ina fama da patient din ka?" Junaid ya tabe baki yace "Naga tana tsorona ne, kai ne bata tsoro dat's why I decided not to show up today" El-Ameen yayi tsaki yace "Didn't you see dat uniform dinka ke scare dinta, wear mofty while coming always, yanxu dai I will text u some drugs da xaka siyo idan kana tahowa, and ka siyo mata fruits taki cin abinci" Junaid ya kuma tabe baki ya katse wayar ya ajiye. Kallon agogo yayi yaga an kusa magrib, ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala sannan ya fito ya dau makullin motarsa da Atm sae wayarsa ya fita ya rufe kofarsa. Bangaren Mumy ya fara shiga, yana kallon fatima dake guga yace "Mumy fa?" Tace "tana bayi" juyawa yayi ya tafi masallaci, ana idar da sllh ya dawo gida, Mumy da fitowarta daga kitchen kenan tace "Ga abincin ka a dinning can" kallon dinning din yayi yace "Porridge?" Mumy tace "Shi kake so?" Girgixa mata kai yayi yace "No khadija ce tace min porridge aka yi" Mumy tace "Ehh amma kai na maka girkin ka daban" yace "Toh nagode Mum, but xan d'an fita yanxu idan na dawo xan ci" tace "Fita kuma? Ina xa ka?" Yayi kasa da murya yace "xan d'an raka El-Ameen wani gun ne, daga can xa mu je kallon kwallo" ta tabe baki tace "Xa dai ku je tadi koh?" Dariya yayi yace "A'a fa Mumy" murmushi tayi tace "Toh kar dai ka wuce 8:30 a waje, ka ma shiga gun abbanka kuwa" yace "Ehh daxu na shiga" daga haka ya juya xai fita, Humainah tace "Ya Ahmad xan raka ka" yace " Nooo" daga haka ya fice daga parlon, Mumy tayi dariya tace "Ki bari ran lahadi ya xaga da ke katsina" tayi murmushi tace "Toh Mumy, ko yace A'a kiyi masa masifa sai ya kai ni" sae da junaid ya fara siyan abubuwan da El-Ameen ya ce masa ya siya ready made din fura da nono sannan ya nufi gidan, Mama kadai ce kwance parlor kan darduma, ya gaisheta ya bata nata fruits din da fura tayi ta masa Godiya yayi murmushi kawai ya haura sama. Xaune ya samu El-Ameen yana danna laptop, ita kuma tana tsaye can jikin bango ta jingina, El-Ameen yace "Sae da ka ga dama kenan" Junaid bai tanka sa ba ya ajiye ledan hannunsa ya xauna gefen gado, El-Ameen ya ya juya yana kallonta yace "Ba dai baki ji ba, wait in tashi xa ki ga abinda xan maki a wajen nan" Junaid ya kallesa kafin ya girgixa kai a xuciyarsa yace ae Kaine mahaukacin ma, takowa tayi ta karaso kusa da ledan da junaid ya ajiye ta durkusa, El-Ameen ya daka mata tsawa yace "c'mon ance maki naki ne" mikewa tayi da sauri, Junaid ya dauki ledan ya mika mata ta karba, El-Ameen ya mike tana ganin haka ta sake ledan ta koma jikin bangon da take, dariya yayi yana kallonta yace "kai! Yarinyar nan ba dai tsoro ba" shi dai Junaid ko kallonsa bai yi ba, Karasowa yayi ya dau ledan ya bude ya fito da bunch din Ayaba ya mika mata, ta karaso da sauri ta karba, xata juya ya fixgota ya xaunar da ita gabansa, da kansa ya shiga bude mata ayabar yana mika mata, tana karba tana ci, ana uku ne taki ci, ta kalli Junaid dake danna wayarsa sae dae gaba daya hankalinsa na kansu, ta matsa kusa da shi a hankali ta kama hannunsa ta sa mashi Ayaban, tabe baki El-Ameen yyi ya kuma bare mata wani ta karba ta kuma kama hannun Junaid ta basa, El-ameen ya hade rai ya kuma bare wani ya bata xata ba Junaid yayi mata tsawa, a tsorace ta juyo, yace "I will knock you yanxu, ina shan wahala ina bare maki abu kina kyauta da shi, da xan bar ki yanxu da peel din xaki hade ki cinye," kafa masa manyan idonta tayi ko kiftawa bata yi, junaid yayi murmushi ya girgixa kai, wayar El-Ameen ne ya fara ring ya dauka, xaro ido yayi ganin Abbansa ne ke kiransa, ya kalli Junaid yace "Kasan kuwa ban je clinic throughout yau ba" ko kallonsa Junaid bai yi ba, ya daga a hankali ya kai wayar kunne, daga daya bangaren Abban nasa yace "ka taho clinic ka sameni yanxu Ahmad, clear?" yayi kasa da kai yace "Toh Abba" daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace "Look! Xan je clinic yanxun in dawo, wait har sai na dawo don't go plss, kaga bata da lafiya karfin hali kawae gareta she just finished vomiting kafin ka shigo, dats why nake nan har yanxu, am giving her her drugs before leaving yanxu" Junaid ya xaro ido yace "Idan Mumy ta kira ni fa, beside 8:30 tace in dawo gida, nd this is almost 8 o clock" Kallonsa El-Ameen ya tsaya yi sae kuma ya girgixa kai yace "Tashi ka tafi toh, wato nine bansan darajan parent dina ba koh Captain, nine na iya karya kai baka iya ba, you know am doing this goddam job for ur sake if you provoke me wllh sae in fasa kawai ka kaita asibiti, kullum safiya sai na xo nan sbda drugs dinta da injections, at mid day ma I have to leave whatever i am doing in xo nan bata magani, haka da yamma ma, sannan da daddare bana barin gidan nan sai kusan sha daya, Haba!" kallonsa kawae junaid yake bai ce komai ba, tsaki yayi ya mike ya dauko maganinta da cup yayi diluting da ruwa ya xauna kusa da ita xai bata tana ganin haka ta fara kokarin mikewa ya fixgota, bbu gardama ta shanye maganin duk jikinta na rawa, ya mike ya dau makulli da wayarsa yana kallon junaid on a serious note yace "Look! In har ka bar gidan nan kafin in dawo wllh wllh kaji rantsuwan musulmi koh, toh sai dai ka san yanda da xakayi da yarinyar nan don ba fina biyayya kayi ba, I am taking my hands of her case" daga haka ya fice daga dakin, Junaid da ya bi sa da kallo yana murmushi snn ya juya yana kallonta, yatsine fuska kawae take, ta matso kusa da shi ta mika masa Ayabar hannunta, a hankali ya sauko daga kan gadon ya karba ya kai mata baki yana kallonta yace "Eat!" Ta kauda kai da sauri, kallon Ayabar yake yana son ci amma ya kasa, ajiyewa yayi ya dau Apple ya mika mata, Kin karba tayi, yayi murmushi ya ajiye shi ma, a hankali ta kwanta nan gefensa, ya tsura mata ido, kamar warce aka tsikara ta mike xaune da sauri, ya koma baya yana kallonta.Amai ta shiga kwararowa a gurin, ya mike yana kallonta har ta gama ta koma xata kwanta yayi saurin riketa, kara ta saki ta turasa da karfi xata kwanta gun aman yaki saketa, nan ta shiga kokuwa da shi ita sai ta kwanta, ya rike ta gam yace "Wait Jasmine..." ta kuma sakin wani ihun da ya tsorata shi, ae da ta turasa sai da ya kusa faduwa ba shiri ya saketa, ta yi kwanciyarta nan kasa, ya sauke ajiyar xuciya ya nufi toilet, mop da bucket ya dauko ya dawo dakin, rasa ta inda xae fara gyara wajen aman yayi, ya ajiye ya fita don kira Mama jummai, tare suka shigo dakin, ta karaso kusa da ita da sauri cike da tausayinta ta dagota tana mata sannu, ihu ta sakar mata ita ma ta kwace kanta ba shiri ta saketa ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi, girgixa kai mama tayi ta mike ta shiga gyara wajen, tana gamawa ta kuma gwada d'aga ta a kasan tiles din still taki tashi, kyaleta tayi ta fita, Junaid ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito jin kiran isha, a nan dakin yayi sallah, yana xaune kan darduma ya ga tana juye juye a kasan da take kwance. Kallonta kawae yake cike da tausayinta don da ganinta kasan tana jin jiki, ta mike xaune a hankali ta dawo inda yake tana kallonsa ta kwanta kusa da shi, dagota yayi murya can kasa yace "Sorry Jasmine" lumshe ido tayi ta kwanta nan kusa da shi lkci daya bacci ya dauketa, ya mike ya koma can jikin gado ya xauna, har Karfe tara El-Ameen bai dawo ba, duk ya kagu ya dawo ya wuce kafin Mumy fa kirasa, tara da rabi kiran Mumy ya shigo wayarsa, k'asa d'agawa yayi don bai ma san me xai ce mata ba har sai da ya kusa katsewa sannan ya daga da sauri, Mumy tace "Where are you Ahmad" kallon dakin yayi kafin a hankali yace "Mumy, am am with El-Ameen" strictly tace "You are very stupid, within the next 10 to 15 mins ka tabbatar kana cikin gida if not xaka ga bacin raina, in kuma kaya ku ka kasa a titi ku ke saidawa da daddaren nan xaka gaya min" kamar mai shirin kuka yace "Kiyi hakuri Mumy xan dawo" katse wayar tayi, ya rike kansa, layin El-Ameen ya shiga nema yana ta ring bai d'aga ba, ya lumshe ido ya jingina jikin gado, he just don't know wat to do, haka yayi ta kiran El-Ameen bai daga ba, Shivering yaga tana yi daga kwancen da take kan darduma, ya mike ya karasa inda take ya dago ta ta bude ido da sauri, kan gadon dakin ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, ta cire xata sakko ya riketa da damuwa yace "You are shivering Jasmine" ba shiri ya saketa a dalilin kara me karfi da tayi masa a kai, ta sauka nan kasan dakin ta kuma kwanciya. Har goma El-Ameen bai dawo ba, Junaid ya rasa me ke masa dadi shi da bae taba yi ma Mumy musu ba, yasan kuma fushi tayi shi yasa bata kara kira ba, da yayi niyar tafiya sae ya tuna abinda El-Ameen yace masa, ya kuma san xai aikata, shine xaune har sha daya, Mama jummai ta shigo tace "Kai xaka kwana yau a nan kenan junaid?" D'an murmushi yayi yace "A'a ina jiran El-Ameen ne yace xai dawo" tace "Toh tafi daki can ka kwanta inda yake kwana xan kula da ita" Junaid yace "yana kwana nan ne?" Tace "Eh wani lkcn yana kwana can dakin don akwai alluran da yake mata da sassafe, toh duk ran da xai mata alluran a nan yake kwana, ni kuma tare muke kwana da ita saboda shiga bayi da daddare" Junaid ya gyada kai yace "Bari in jira sa a nan Mama ni ba kwana xan yi ba ai" tace "Toh" sannan ta juya ta fita. Lumshe ido yayi ya jinginar da kansa jikin gado, wani bacci ya ji na fixgarsa ya bude ido yana kallon agogo yaga sha biyu, kallonta yayi ya ga ta canxa position, a hankali ya mike ya isa inda take xai dagata ta bude ido da sauri, birginawa tayi ta bar gun ta juya masa baya, ya mike ya koma ya xauna kan gadon, xuwa yanxu kam ya gama sanin iskanci El-Ameen yayi masa, dole ko yaki ko ya so a nan xai kwana hakan ba karamin bata masa rai yayi ba, sha biyu da rabi ya kuma mikewa jin yana jin bacci sosai ya bude closet ya dau bargon da ya gani ya koma daya side din gadon ya shimfida a kasa ya kwanta dai dai yanda xai dinga ganinta, nan da nan bacci ya daukesa.

Bude ido yayi jin an bude kofa don ko k'adan bashi da nauyin bacci, El-Ameen ne ya shigo dakin yana ganinsa ya dauke kai, kallo daya El-Ameen yayi masa yana murmushi bai ma san idonsa biyu ba ya karasa gun da take kwance a kasa, durkusawa yayi gabanta ya dagota, ta bude ido da sauri, lumshe ido yayi jin xafin jikinta a hankali yace "Sorry, Jewel" xata koma ta kwanta yaki saketa, ya mike ya dauketa ya nufi kan gado da ita ya kwantar, kokarin sauka ta shiga yi da kyar, ya hade rai yace "No" bata kuma yunkurin saukan ba, ya gyara mata kwanciya ya mike ya shiga bayi, duk wannan abun Junaid na kallonsu, ya dawo dakin rike da bowl din ruwan sanyi ya bude closet ya ciro towel karami da babba ya saka karamin cikin ruwan bowl din ya dawo kan gadon ya ajiye bowl din kan bedside drawer, ya dagota yana kallonta don idonta biyu, ya dawo da bowl din ruwan gefensa ya matse ruwan towel din a hankali yana goge mata forehead dinta da shi, kara ta saki xata sauka ya hade rai yace "Wait!" Bata kuma yunkurin saukan ba, haka ya ci gaba da goge jikinta da yayi xafi sosai da towel din yana mata sorry, mikewa Junaid yayi, El-Ameen ya juya da sauri ya kallesa sannan yayi saurin rufeta da bargo yace "Ohh you weren't sleeping dama" Junaid bai tanka sa ba ya dauke bargon da ya shimfida kasa ya mayar cikin closet, El-Ameen ya tabe baki yace "Ni ban ma yi tunanin xan dawo in same ka ba Mumy's boy, theatre muka shiga da Abba and we came out few minutes ago, saboda nasan condition din patient dinka shi yasa na fito cikin daren nan, I ought to...." jin anyi banging kofa El-Ameen ya kalli kofar da sauri don dama yana magana ne yana matse towel a ruwa, murmushi yayi ganin ficewa yayi, ya ci gaba da abinda yake, har sai da yayi make sure temperature dinta ya dawo dai dai, still yayi ganin hawaye idonta, ya sunkuya a hankali ya goge mata fuskar yace "Am sorry Jewel, am only helping" sauka yayi daga kan gadon yaje ya xubar da ruwan ya shanya towel din a bayi ya fito, bacci ya sameta tana yi a yanda ya barta, ya gyara mata kwanciya sannan ya hada allura yayi mata da kyar don a tsorace ta farka ta fara kokuwa da shi, sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita dakin ya shiga master bedroom duk a tunaninsa xae tarda junaid nan, sae yaga otherwise, tabe baki yayi sanin yana parlor knn, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canxa kaya yayi kwanciyarsa dakin, sai dai before dawn yaje dubata ya fi sau goma duk da a shigowarsa na uku ya tarda mama jummai a dakin, Karfe biyar da minti arba'in ya sauko parlor ya tarda Junaid xaune kan darduma, xaunawa yayi kan kujera yana kallonsa yace "A parlor ka kwana kenan?" Junaid ba tare da ya kallesa ba yace "Yea!" El-Ameen yace "Ohk, gud morning, yanxu dai you need to transfer some money into my account xuwa later akwae drugs din da na mata prescribing, and you know wat? Suna da tsada gaskiya or I shud just text you their names, tell you where to get them, kaje da kanka ka siyo, if you need my assistance let me know" El-Ameen ya kare maganar yana d'aga kafada, Junaid ya mike ya dauke darduman da yayi sallah yace "nawa ne kudin?" El-Ameen yace "100 nd 50k will be enough" Junaid yace "Alryt" ajiye darduman yayi kan kujera ya kalli El-Ameen yace "Na tafi, I will transfer it later in the day" bai jira cewarsa ba ya nufi kofa ya fice daga parlorn, makullin motarsa ya ciro a aljihu ya fita waje inda ya ajiye motarsa ya bude ya shiga ya kama hanyar gida, driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa ba ya tare da shi, bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, toh ina ma xai ce mata ya je, gidansu El-Ameen? No yasan xata iya kiran Ummi, murmushi yayi yana tunanin randa xae samu freedom, don ya fara damunsa yanxu on like before, a waje yayi parking ya fito, gabansa ne ya fadi ganin Abbansa alamar daga masallaci yake, da kyar ya ja kafa ya isa gun gate ganin Abba ya tsaya har ya risina xai gaida Abba, Abba ya dakatar da shi yace "Daga ina kake?" Yayi kasa da kai zai yi magana Abba ya juya ya shiga cikin compound, bin bayansa yayi har suka isa part din Abba, Hajiya ke ta goge goge a parlon, Abba ya xauna kujera yana kallon Junaid, a hankali ya xauna kasa ya juya yana kallon Hajiya dake kallonsa da d'an murmushi mai wuyar fassara a fuskarta yace "Ina kwana Hajiya" tace "Lfya lau Ahmad" sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Daga ina kake Ahmad?" A hankali yace "Tare muke da El-Ameen Abba" Abba yace "Tare a ina?" Hajiya ta dawo cikin parlon tana girgixa kai tace "kwata kwata ni hankalina bai kwanta da abotansa da yaron nan wai El-Ameen ba, yaron da bai da nutsuwa ko maganan iyayensa bai ji, kusan duk dare sai ya shigo ya fita da shi, Ahmad baxae dawo gidan nan sai kusan sha biyu wani lokacin har daya, duk ina lura da yake ni ba mai nauyin bacci bace ka sani Alhaji, to amma kar mutum yayi magana ace hassada ko kuma ace don ba d'an sa bane, amma kwata kwata Ahmad ya sauya hali a gidan nan, jiya wllh wllh khadija ca tayi min mace ta gani a motarsa da magariban nan da ya fita, to ina yaje yake dawowa yanxu, kuma duk Hajiya Amina tana ganin abinda yake baxata ce komai ba saboda ta dauki son duniya ta daura ma yaro, meye amfanin haka, in ma aure yake so ba sai yayi magana ba, ae ba wae bai isa bane" tunda ta fara magana Junaid ya kafeta da ido ko kiftawa bai yi, Abba kuwa sai kallonsa yake bacin rai karara a fuskarsa.
Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido a hankali bai dai ce komai ba, Abba ya kalli Hajiya yace "A kira min Aminar" da sauri Junaid ya bude ido ya marairaice masa yace "Don Allah don annabi Abba ka min duk abinda xaka min, amma bbu ruwan Mumy bata ma san bana nan ba, plss..." wani tsawa Abba ya daka masa, babu shiri yayi tsit, Hajiya ta juya ta nufi kofa lebbenta dauke da wani murmushi, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Suhaima ta tafi kiranta" Abba bai ce komai ba ta nemi waje ta xauna tana girgixa kafa tana tabe baki, ba a dau lkci ba Mumy ta shigo parlon da sallama, sai dai duk jikinta yayi sanyi ganin junaid xaune parlon tasan ba abun arxiki ya sa aka kira ta ba, kujera ta samu ta xauna tare da gaida Abba. Bbu yabo bbu fallasa ya amsa, junaid ya k'asa dago kai ya kalleta duk jikinsa yayi sanyi, Abba yace "Ke a tunanin ki so kike nuna ma yaron nan koh Amina, har ya kai matsayin da Ahmad baya kwana gida yanxu shi ba nyt duty ba kika xuba masa ido koh, toh dama an sha gaya min ban yarda ba amma yau idona ya gane min komai, don haka ni baxan bari ya dauko min abun kunya ba ina xaman xama na, just few weeks na basa ya fito da mata idan ba haka ba xai sha mamaki na wllh....." Mumy da har idonta sun cicciko ta kallesa cike da takaici tace "Alhaji kar ka manta Ahmad ba mace bane da har kake tsoron ya dauko maka abun kunya, kuma mace ake ma kulle ba namiji ba, ko yau ya ga bai son xaman gidan nan yana iya barin sa ya koma duk inda yake so don namiji yake ba mace ba kuma ya mallaki hankalin kansa, ni na haifi Ahmad na kuma fi kowa sanin halinsa ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba baxai aika ta mugun kaxamin kaxafin da ake son lika masa ba, I know my son" hawaye na bin kuncinta ta kare maganan, Hajiya ta bude baki ta saki salati tana tafe hannu, Abba ya mike fuskar nan tasa a murtuke yana kallonta yace "lallai Amina wato ni ke masa kaxafi kenan koh, to bari ki ji, wllh sati uku na basa yayi aure ya bar min gidana idan ko ba haka ba xai gane matsayina a gun sa" mikewa Mumy tayi tana kallonsa tace "Toh sai me, bai isa auren bane!" wani kallon Allah wadaran shaidanin mutum ta jefa ma Hajiya ta fice daga parlon, Hajiya ta dinga salati tana cewa "kiri kiri mutum yasan gaskiya ya danne don bai son laifin d'an sa, Allah sarki duniya" Abba ya kalli Junaid yace "Ka dai ji me nace maka, sati uku na baka wllh, get away" mikewa Junaid yayi da kyar ya fita daga parlon kansa na juya masa, part din Mumy ya shiga ganin bata parlor ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta gefen gado tayi tagumi, ya durkushe gabanta, ya daura kansa bisa kafarta cikin sanyin murya yace "Don Allah forgive me mum, it wasn't my intention disobeying you yesterday, I.. I am sorry mother forgive me plss" jin bata ce komai ba ya dago idanuwansa da suka kada yana kallonta, kamar xae sakar mata kuka yace "Plss Mumy kiyi hakuri!" "Ina ka tafi jiya?" Ta jefo masa tambayar tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi Cause he is not dat gud at lying, yanxun nan sae ta gano sa, ya kalli agogo, kallon agogon tayi ita ma taga bakwai saura ta d'an sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Tashi ka tafi" a hankali ya kamo hannunta yace "Plss Mumy kiyi hakuri nace" a nutse tace "Leave!" Ya kusa minti biyu durkushe gun sannan ya sake hannunta ya mike a hankali ya juya ya fita daga dakin ya shiga part dinsa. Cikin minti ashirin yyi wanka ya gama shirinsa, ya fito sae dai da ganinsa kasan bashi da nutsuwa, part din Mumy ya koma, ya sameta tsaye dinning tana jera masa breakfast, karasawa yayi yana rike da hularsa, Mumy ta bar dinning din, sosai jikinsa yayi sanyi ya ja kujera a hankali ya xauna ya dau mug din tea'n da ta hada masa ya shiga sha ba don yana jin sha ba, tea kawae ya iya sha ya mike ya dawo parlor yana kallonta yace "Xan tafi aiki Mumy" tace "baka ci dankalin ba, wa ka bar ma? go back and eat it yanxu" ba musu ya koma ya d'an ci kadan sannan ya kurbi ruwa ya dawo yace "Na ci Mumy" tace "Allah ya tsare" a sanyaye ya nufi kofa ya fita, Humainah da fatima sun fito daga part din Abba kenan, Humainah ta nufesa ganin parking lot ya tafi ya bude motarsa, kan ta iso har ya shiga, ta bude motar ta wara ido tace "Ya Ahmad Abba yace anjima ka kai ni islamiyyar su fatima ni ma a min...." Fixgo kofar motarsa yayi ya rufe, tayi still wajen tana kallon bakin glass din motar, yana gama ba motar wuta ya ja ya bar wajen, tsaki ta ja sai kuma ta fashe da kuka ta juya suka yi ido hudu da Hajiya da suhaima dake kallon duk abinda ya faru, Suhaima ta fashe da dariya, da gudu tayi part din Mumy tana kuka kamar wata jaririya. Haka Junaid ya wuni gun aiki duk bai da sukuni, colleagues dinsa har tambayarsa suka dinga yi ko lafiyarsa yace he's just having a slight headache ne, duk ya tuna abinda Abba yace sai gabansa ya fadi ba kadan ba, wai 3wks, kuma yasan ba lallai yayi kaffara a kansa ba, tunda ya dauki kudurin taimakon baiwar Allahn nan yake fuskantar challenges iri iri ga shi bashi da rest of mind as before, and he knows he is only doing it for Allah's sake ba da wata manufa ba, damuwar da yake ciki bai hanasa yi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin din da yace na drugs dinta ba, Hudu bai karasa ba ya bar gun aiki ya dawo gida, part dinsa ya nufa ba tare da ya kalli su Umma da Hajiya dake xaune balconyn Hajiya ba yayi shigewarsa parlor yyi banging kofar, Hajiya ta tabe baki tace "Ke maganar ki gaskiya ce wllh, tsinannan uwar nan tasa bata bari yaci girkin mu, ita ke masa da kanta kullum" Umma tayi kwafa tace "Ahaf Ba baki yarda ba da, ae wannan matar ae sai dai muyi adduar ganin karshenta" Hajiya tace "Toh wai meye kuma next move din da xa mu dauka tunda gashi ance ya fito da mata nan da sati uku, ke kar fa kuma yace wannan shegiyar Humainah take kowa, kinsan fa ba kula matan yake ba, kar uwarsa tace ya fito da Humainahr kawai mu shiga uku, wannan fa shine anyi ba ayi ba" Umma ta xuba tagumi tana gwalo ido yace "Yo ni ae wannan tunanin bai fado min ba wllh, kai da mun shiga uku, ni fa Humainahn nan ba karamin tsana nayi mata ba fa don duk da dududu bata fi sati gidan nan ba naga alama bata da kunya ko kadan, kuma ko shigowa gaishe mu bata yi, sai ma taga dama take gaishe mun in ta shigo gun Alhaji, kuma ina ga kamar tsinannar Aminan nan ke xuga ta" Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Xamu san yanda xa muyi da shegiyar ita ma, kuma ma ni ban ga alamar suna soyayya ba kin san halinsa ai, kuma ni shawarata kawai mu hade kai mu san yanda xa ayi Alhaji ya hada sa da Suhaima ko Muhibba shikenan sai yanda muka yi da shi" Umma tace "Toh ai matsalar ynxu kawai kullin da aka bamu mu barbada kofarsa ne, ya xa muyi? kinsan ba xuwa can bangaren muke ba, muna xuwa yanxu xa a gano mu, kuma don tsiya wai sai da magriba, dama da rana ne bbu wanda xai lura shi kuma yana gun aiki, ita kuma sallamammiyar 'yar ki khadija ba bamu hadin kai xata yi ba" Hajiya ta d'an yi shiru sannan a hankali tace "Suhaima xata yi mana aikin, nasan halin abata tsaf xata yi ba tare da an xargi komai ba" Umma tace "Toh Alhmdllh" da haka suka ci gaba da hirarrakunsu cike da rashin tsoron Allah.Junaid kam wankansa yayi ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin kananun kaya yayi la'asar a dakin sannan ya fito yayi part din Mumy, suna xaune da Humainah tana mata tsifa, Ya xauna yana kallon Mumy yace "Ina yini Mumy" bbu yabo bbu fallasa tace "Lfya lau" shiru yayi, Mumy ta hade rai tace "Ka kyauta Ahmad ita 'yar uwar taka ka walakanta gaban idon makiyan ka koh?" Humainah ta bata rai, sai kuma ta fashe da kuka, Mumy tace "Ji walakanci, meye haka ke kuma" mikewa tayi fuu ta koma dining tana rera kuka, Mumy tayi tsaki ta galla masa harara ta shige daki. Murmushi yyi yana shafa kansa ya mike ya nufi dinning din, kujerar dake kusa da wanda ta xauna ya ja ya xauna ta mike xata bar wajen ya rikota ya mayar da ita ya xaunar yace "Wai dama daxu magana kike min" ta fizge hannunta tace "Ohon maka" dariya yayi yace "Ni fa nayi xaton da kofar mota kike, toh tunda da ni kike yi hakuri..." Ta fashe da wani sabon kukan tace "Allah bana so" murmushi kawai yake yana kallonta yace "Toh kar ki so din, har da wani kwalliyarta tayi xaton da El-Ameen xamu dawo" ta dago da sauri tana kallonsa ta tsuke fuska tana goge hawayen idonta tace "Wani kwalliya nayi" giranta ya taba a hankali yace "Ba gashi ba har da wani shafa baki kika yi anan irin yanda kuke yi" ya kuma kallon pink lips dinta yana murmushi yace "Har da wani shafa jan baki a nan duk don ki burgesa" buge masa hannu tayi fuskarta daure tace "Tun da kai ka shafa min ba" mikewa tayi xata bar wajen ya rikota da sauri yana dariya yace "Toh na dai ce kiyi hakuri koh" ta turasa tayi gaba abunta, murmushi yayi ya tabe baki, fatima dake bakin kofar kitchen tayi gyaran murya tace "Uhum ya A.jay Humainaj kadai yake ma dariya a gidan nan" wani kallo yayi mata, ta juya da sauri ta koma kitchen tana dariya, tsaki yyi ya bude food warmern dake dining din, kadan ya xuba shinkafar ya ci ya dawo parlor don duk bai da Appetite, kofa ya nufa ya koma part dinsa ya kwanta ya lumshe ido, yana son ya gansa can gidan El-Ameen ya ga halin da Baiwar Allahn ke ciki amma yasan baxai ma fara cewa xai fita ba, haka yayi ta juye juye kan kujeran duk ya rufe ido ita yake gani, shi kam tun da ya fara ganin yarinyar nan nutsuwarsa ya ragu, toh ko dai haushin taimakon nata da yayi take ji shiyasa ya kasa samun kwanciyar hankali, bude ido yayi jin an bude kofarsa, ya juya da sauri ya ga Humainah ce, ta hade rai ta dungure masa bowl din fruit salad din hannunta a kasa, murmushi yayi yace "da kin xubar ai," ko kallonsa bata yi ba ta fice. Washegari haka ya tafi aiki da safe as usual, ba laifi Mumy ta d'an kulasa da yaje breakfast, Abba kuwa dama da yaje gaishesa ca aka yi masa yana bacci, ko ta kan Umman bai bi ba yayi ficewarsa don ya saba in dai ba Mumy ce da girki ba to ba lallai ya ga Abba ba sae ko a masallaci, kasa samun natsuwa yayi gun aiki har sae da ya dau excuse din minti ashirin ya fita ya kama hanyar gidan El-Ameen, su biyu kadae ne parlon ita da mama dake mata kalaba daga tsaye don taki xama, sae xagaye parlon suke ana kitson a haka, tana ganinsa suka hada ido ta kurma wani uban ihu da yayi mugun tsorata mama don kan kace me har ta kai bakin kofa, shi kam tsayawa kallonta yayi, har lokacin ihun take da karfi tana shisshigewa jikin bango ko ina na jikinta na rawa, lumshe ido yayi a hankali ya bude ya kalli uniform din jikinsa White navy shirt ne jikinsa da dark trousers navy blue, ya kalleta ya ga yanda ta runtse ido tana k'uwa, bude kofar parlon aka yi El-Ameen ya shigo da ledoji a hannunsa, sake ledojin yayi da sauri ya karasa gunta, ya riketa, bude ido tayi a gigice ta kara fasa wani ihun tana ganin El-Ameen ta rungumesa, ya rufe bakinta lkci daya tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya a hankali, kallon Junaid yayi ya hade rai yace "Look captain, I've warned you not to come to this house on uniform again, look how you are scaring the life out of her, a haka xata samu lafiya? Plss ka daina xuwa nan da uniform" Juyawa Junaid yayi ya fice daga parlon, Mama dake bakin kofa har lkcn tace "Auuu wae khakin take tsoro? Allah sarki Baiwar Allah" dago kanta El-Ameen yayi yana kallonta ita ma haka, kama hannunta yayi yana rike da ita suka haura sama. Junaid na komawa gun aiki ya ci gaba da harkokinsa sai dai da ka gansa kasan there is something eating him inside, karfe biyar saura ya isa gida, ya jima xaune motarsa yana danne danne a waya, ganin motar da ke kokarin parking gefensa ya kashe motar ya fito ya rufe yayi part dinsa. Yana kwance parlor'nsa dab da magrib yana kallon wani program though absentminded yaji Humainah na kwalo masa kira daga waje, mikewa xaune yayi jin irin yanda take kiransa da karfi, ya mike da sauri ya nufi kofa ya bude, tsaye ya ganta d'an nesa da balconyn rike da kugu tana tafe hannu tace "Taho taho ka ga yaya" yana fitowa sai kuma tayi bangaren Mumy da sauri tana kwalo mata kira ita ma, wanda hakan ya ja attention din 'yan gidan da ido da kunnensu na kan duk wani motsi na gidan kamar masu gadi, Umma ta riga Mumy da fatima fitowa sannan Hajiya, su khadija Rabi'a, sadiya, Muhibba duk suka fiffito, shi kam Junaid abinda ya daure masa kai bai wuce na ganin Suhaima tsaye bakin kofarsa tana xaxxaro ido sai kokarin boye abu a hannunta take, Humainah ta dawo da sauri Mumy na biye da ita a baya haka ma sauran, Hajiya kam ko ina na jikinta rawa yake ji take kamar ta saki gudawa tsabar rudu shikenan asirinsu ya tonu, garin yaya Suhaima taje bakin kofar ba tare da ta sa ido taga bbu kowa a tsakar gidan ba, ita kanta umma sai da hanjin cikinta ya kada sai dai duk basu nuna a fuska ba, don Hajiya sai ma wani hade ran karfin hali tayi, A takaice Humainah ta rike kugu tace "Abu naga tana shirin barbada wa bakin kofar ya Ahmad, duk bata san ina can bakin pampo naje daurayo takalmana ina kallonta ba" ta fadi haka tana nuni da kusa da bangaren da Hajja ke sauka, Suhaima dake ta salati a rikice tace "Sharri xa ki min don kin gan ni a nan, na shiga uku na lalace, Hajiyanmu kina jin abinda yarinyar nan ke cewa" a fusace Humainah tace "koh ba sharri ba, ki bude tafin hannun ki munafuka, kin wani xo kina yi kamar mage baki san ina kallonki ba xaki wani ce ina maki sharri, wllh Mumy abu take shirin barbada masa bakin kofa" Hajiya ta hadiye yawu da kyar tace "Ke yanxu 'yar nan sharrin naki kan 'ya ta kuma xe sauka, duk shekarunta gidan nan bata taba barbada ma Ahmad abu ba sai da kika xo munafuka algunguma toh wllh sai Alhaji ya xo ya mana shari'a don baxan yarda da kaxafin nan ba" fuu Humainah ta haura balconyn ta fixgo hannun Suhaima dake jin kamar ta saki fitsari tana huci tace "Bude hannun to idan sharri na maki, ki bude, uwar me ya kawo ki bangaren sa da daddare ke da ko during daylight ba xuwa kike ba munafukaa, toh wllh sai kin fadi Meye wannan kike shirin barbada masa ko in gaggalla maki mari a nan don ubanki" Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Humainah!" Humainah na girgixa kai ido rufe tace "Ni dai Mumy Allah sai ta fadi meye a hannunta ko kuma muje ta barbada shi a kofar uwarta ni baxan yarda ba"Suhaima da duk ta jike da xufa ta fara kokarin kwace hannunta daga rikon da Humainah tayi mata tana cewa "Na shiga uku ki cika ni, me na maki xaki min irin wannan sharrin?" Banda murmushi babu abinda khadija take, Hajiya dai da kyar kafafuwanta ke daukarta ga wani kullewa da cikinta yayi, Umma kuma sai wuwwurga ido take tana xufa, Sadiya ta haura balconyn a fusace tana kallon Humainah tace "Ke karamar 'yar iska cika mata hannu kar in baki mamaki yanxu....." Humainah ta juya a hankali tana mata wani matsiyacin kallo tace "Kambu! Ko kuma ni in baku mamaki ba, ai wllh sai ta fadi kullin uban meye a hannunta kuma wa ya aikota idan ba haka ba in karya hannun" Khadija tace "Toh ke Anty suhaima ki bude hannun a ga kullin mana, ko dai yaji xa ki kai masa?" Hajiya tayi kanta xata cafke ta ai da gudu ta bar wajen, cike da karfin hali Hajiya na huci tace "Ae sun yi kadan ta bude masu hannu wllh, sai dai duk...." Fitowar Abba yasa ta kasa karasawa ta fara girgije girgije ae kawae sae ta fashe da kuka tun kan ya karaso tace "Na shiga uku ni fateema me muka tare ma mutane a gidan nan ni da 'ya yana" A hankali Mumy tace "Cikata Humainah" Humainah ta girgixa kai ta cakumi rigarta tace "Noo! Ae sai ta bude hannunta mun ga ko menene wllh Mumy" shi kam Junaid tsaye kawai yayi ya kasa cewa komai duk jikinsa ba karfi, Abba na isowa ya shiga tambayar Meye haka, Humainah tace "Abba wallahi barbade take shirin yi ma Ya Ahmad Allah ya toni asirinta na kamata kuma ni sai taje bakin kofarsu ta barbada koma Meye xan kyaleta" Hajiya ta fashe da matsanancin kuka ko ina na jikinta na bari tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji koh...." Abba kam kallonsu ya tsaya yi, can yace "Cikata Humainah" Humainah ta fashe da kuka tace "Ni wallahi baxan saketa ba Abba, sai ta nuna abinda ke hannunta kuma muje ta barbada shi a kofarsu, duk bata san ina can ina kallonta ba, ni wallahi baxan kyaleta ba" dariya khadija ta dinga yi can ciki ciki ganin yanda 'yar uwarta ke wurga ido kamar barauniya, da kyar Mumy ta haura balconyn ta kamo Humainah tace "Saketa Humainah" still taki sakinta ita fa sae ta bude hannunta, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa kusa da su a sanyaye ya janyeta yace "Kyaleta Lil sis" fashewa tayi da wani kukan tace "Ya Ahmad abu fa tayi niyar barbadawa da ban ganta ba" ae Suhaima tun da ta samu Humainah ta saketa kan kace me har ta sauko kasa tana tuntube, ta fashe da kuka tana kallon Hajiya da Abba tace "Kudi fa na xo tambayarsa don ta ga ina leke leke shine take cewa barbade xan masa," Hajiya ta rungumeta ita ma ta fashe da kukan tace "Na sani Suhaima Allah xai saka mana kiyi shiru" Humainah ta kwace kanta daga rikon da Junaid yayi mata ta sauko tana kallonta da kyau tace "Kuma wallahi daga yau na kuma ganin kafar ki a nan wajajen sai na karya su duka biyun, munafuka kawai dama ni Hajja tace min boka da malamai kuke bi" tsawa sosai Abba ya daka mata, ta turo baki ta bangajeta tayi part din Mumy fuu tana gunguni, duk suka bita da kallo fatima ta ni bayanta, Abba ya kusa minti daya bai ce komai ba, can ya kalli su Hajiya yace duk kowa ya koma ciki, haka duk suka juya Hajiya na kuka har lkcn tana rike da hannun Suhaima Umma da baki ya mutu na biye da ita a baya, shi ma ya juya yayi part dinsa ana kiraye kirayen sllhn magrib. Mumy ta juyo a sanyaye tana kallon Junaid, shi din ma duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba, kasa cewa komai tayi ta sauka ta koma part din ta, ya lumshe ido ya bude ya bi bayanta. Xaune suka tarda Humainah palo sai rusa kuka take bakin rai, Mumy tace "lafiya kuma Humainah" cikin kuka tace "Mumy ba shine baku bari na mata duka ba, wllh wani kulli ne hannunta tana shirin xubawa bakin kofar na kamata" Mumy ta xauna kusa da ita tana murmushi ta jawo ta jikinta tace "Kiyi hakuri mu bar su da halinsu Allah ya fisu da shi kuma muka dogara, in'sha Allah bbu abinda xai same mu kin ji Humainah" kallon Junaid dake tsaye ya kasa xama tayi tace "Kai kuma ya Ahmad maimakon ka faffala mata mari shine ka tsaya kallonta" Xaunawa yayi yyi murmushi bai ce komai ba, lallashinta Mumy ta dinga yi har dai ta samu tayi shiru, Junaid ya mike ya shiga bathroom din dake parlon ya dauro alwala ya fito ya fita xuwa masallaci, Mumy ta kalleta tace "tashi ki je kiyi alwala" ba musu ta mike ta shiga bathroom Mumy ma ta tashi ta shiga dakinta don yin alwalan. Ana idar da Sllh Junaid ya shigo, Humainah na xaune da Mumy da fatima suna cin abinci, ya xauna yana kallonsu, kwankwasa kofa aka yi lkci daya aka bude aka shigo, Sadiya ce ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskarta tamke tace "Humainah kike ko wa? Abba na kiran ki" Humainah ta galla mata harara tace "A'a Mantawa kika yi dai, Sadiya sunana" Mumy tace "Ke kina da hankali Humainah?" ta turo baki ta ajiye spoon din hannunta, Sadiya tayi kwafa tana gyada kai ta fice, mikewa Humainah tayi, Mumy tace "Ki gama cin abincin tukunna, baxa mu kuma shirya da ke ba idan kina rashin kunya" kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo yana girgixa kai. Da sallama Shukrah ta shiga parlorn Abba, yana xaune kujera Hajiya da Umma ma na xaune sai Suhaima da ke xaune kasa, can jikin kujera ta samu ta xauna tace "Abba gani" a nutse Abba yace "Daga yau kika sake abinda kika yi daxu sai na yi mugun saba maki, Ashe ke shashasha ce, kina daga can bakin pampo ta ya kika ga abu a hannunta" Hajiya ta goge d'an guntun hawayen idonta tace "Babu maganan taya ta gani, wllh sa ta aka yi Alhaji don wnn yar mitsitsiyar hankalinta baxae bata tayi abinda tayi mana daxu ba, to ni kam me na tsare masu xa su yi ma 'ya ta irin wannan mugun sharrin?" Kuka ta fashe da sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Xancen ki gaskiya Hajiya, amma Allah ya san dai dai, kuma baya bacci" Abba ya kalli Humainah da ta wani hade rai kiris ya rage ta fashe, yace "Don uwar ki wa kike ma wannan kallon" mikewa tayi ta fashe da kuka tace "Na rantse da Allah Abba wani abu ne a hannunta tana son budewa ta barbada fa na kama ta, ni ba karya na mata ba, meyasa baka ce ta bude hannun ba tun a can..." Wani tsawa Abba ya daka mata yace "Ke!! Baki san ni ba koh?" Hajiya ta girgixa kai tace "Babu ruwan yarinyar Alhaji da ba a ce tayi hakan ba baxa ta yi ba" Abba yace "Toh maxa ki tafi ki tattaro kayanki ki koma gun Hajiya tunda munafurci kike koya can, maxa maxa yanxun nan ba sai da safe ba" Hajiya ta dan yi murmushi da iyakan sa lebbe, ficewa Humainah tayi da gudu daga parlon, tayi part din Mumy, Mumy na xuba ma Junaid abinci ta fado parlon ta xube nan kasa ta dinga rusa kuka kace yar jaririya ce, Mumy ta karasa da sauri ta dago ta tana tambayarta abinda ya faru, kuka take sosai tace "Wayyo Mumy ni gidanmu xan tafi wallahi baxan xauna a nan ba, ki bani wayar ki in kira Hajjah" Mumy tace "Kiyi hakuri, gaya min me ya faru, me Abban yace maki" cikin kuka tayi ma Mumy tsarin yanda suka yi da Abba, Mumy tayi murmushin takaici bata ce komai ba, Junaid kam lumshe ido yyi ya jinginar da kansa jikin kujera, tana ci gaba da rusa kuka tace "Ni wallahi wucewa xanyi baxan xauna ba" Mumy rasa me xata ce mata tayi, mikewa Junaid yayi ya dago ta yace "Kiyi hakuri, Abba is angry shi yasa ya maki magana haka, xaki ga ya huce xuwa gobe" tace "A'a ni ka ban wayarka in kira Hajja tafiya ta xan yi" cikin sanyin murya Mumy tace "Kar ki kirata, xai iya cewa ni na sa ki kirata" mikewa Humainah tayi ta nufi daki tana kuka. Junaid ya koma ya xauna, Mumy ta girgixa Kai ta ci gaba da xuba masa abincin da take yi. Kasa cin abincin Junaid yayi, Mumy ta lura da hakan tace "Dama ka ci abincinka ka share komai, I keep telling you Junaid never depend on ur father, duk da nasan you are not depending on him dama, kar ma ka sa rai da komai nasa, sannan kayi ta bin sa ku rabu lafiya, you can see how things are going this days nasan ba yin kansa bane, banda hada ka da shi bbu abinda ake yi, lastly be prayerful" a hankali yace "In'sha Allah Mum" tace "Ya maganan da yayi maka jiya, kasan dai yana can yana kirga kwanakin da ya baka, ko kuma ince ana can ana Kirga masa koh" shiru Junaid yayi, Mumy tace "It's better ka kwantar da hankalin ka ka fito da mata tun kan ya nuna maka matsayinsa gun ka kamar yanda yayi ikirari" ae gaba daya abincin fita ran Junaid yayi, da kyar ya dinga tutturawa, Mumy na kula da hakan duk tausayin sa ya rufeta, tasan ba yin kan Abba bane yake masa haka, amma bbu yanda ta iya sai dai ta dage da Addu'a kamar yanda ta saba. Mikewa yayi jin ana kiran isha ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito ya tafi masallaci, ana idar da sllh yana tsaye da Abdul suna gaisawa ya ga tsayuwar motar El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito suka gaisa da Abdul sannan ya kalli Junaid ya shiga gida, part din Mumy ya nufa suka gaisa ta tambayesa mutan gida yace Duk suna lafiya, ya kalli hanyar bedrooms yace "Wa ke kuka kuma Mumy?" Mumy tayi murmushi tace "Humainah ce, daga Abba yayi mata fada wai fa" dariya yayi bai ce komai ba, Mumy tace "toh je ka lallasheta kila tayi shiru, ni taki saurara na" shiru yayi sai kuma ya mike kamar munafuki ya nufi bedroom din Mumy, tura kofar yayi ya shiga ya sameta xaune can karshen gado tana rera kukanta, ya kusa minti biyu tsaye kafin yasa kai ya shiga dakin, ya karasa inda take a hankali, ya duka yana kallonta, tuni ta hadiye kukan da take ta kauda kai, ya d'an bude ido yace "Am, dama Mumy ce tace in xo in baki hakuri wai kina kuka" juya masa baya tayi da sauri, ya d'an sosa kai murya can kasa yace "Kiyi hakuri" taki cewa komai, a hankali yace "Kin ji" Junaid ne ya shigo dakin yana ganinsu ya saka dariya yace "Uhnn! har dakin ka biyota Dr, ba sai ka jira in dawo in kira maka ita ba" El-ameen ya mike yace "Mumy ce tace in xo in bata hakuri Mr man" daga haka ya fice daga dakin, Junaid yace "ba wani nan da'alla kai dai fadi gaskiya" Humainah ta mike xata shiga bathroom ya fixgota yana dariya yace "Oya sorry lil sis" fixge hannunta tayi tace "Ae next time ko boka aka kawo xa a ajiye bakin kofar ka baxan ce komai ba" dariya yayi sosai yace "Nafa ce kiyi hakuri, beside Allah ya fisu I believe" goge mata fuskarta yayi yace "Yanxu sai ki je ki wanke fuskarki kiyi kwalliya kin ga saurayin ki ya xo" Turasa tayi ta shige bathroom, yayi murmushi ya fita, a parlor ya tadda El-ameen yace "Mu je" mikewa El-ameen yayi, Mumy tace "Baxa ka ci abinci ba Ahmad" El-ameen ya girgixa kai yace "Naci abinci Mumy" Mumy tace "Toh shikenan," har sun fita Mumy ta kira Junaid ya dawo, ya isa gabanta yace "Gani Mum" tana kallonsa a hankali tace "Kayi addu'a kafin ka shiga" ya sunkuyar da kansa yace "Toh Mumy" daga haka ya fita daga parlon, suka nufi part dinsa da El-ameen, yayi yanda Mumy tace masa ya bude kofar ya shiga, El-ameen ma ya shiga, El-ameen ya xauna yana kallon Junaid yace "Did you tell anyone about our patient?" Junaid yayi shiru sannan ya girgixa kai yace "Not at all" El-ameen yace "Ohk, daxu mama Jummai take ce min xata je kauyensu gun dotan ta ta haihu, amma kwana biyu kawae xata yi, toh I don't know yanda za ayi abun, who will stay with ur patient during her absent?" Junaid yayi shiru yana kallonsa, can yace "Or shud we get a new...." El-ameen yace "Noo! Kwana biyu tace xata yi beside yarinyar tafi sabawa da ita kafin ta saba da wata kuma is something else, yau satin su kusan uku tare if am not mistaken" Junaid bai kuma cewa komai ba, El-ameen yace "Hurry plss ina son komawa can gidan kafin in tafi clinic" Junaid yace "I don't know what to say" El-ameen yace "How about khadija, naga u guyz are close" lkci daya maganganun Hajiya na daxu da safe ya fado masa wai khadija ce tace mata ta gansa da mace a mota, girgixa kai yayi yana murmushi coz yasan khadija won't do that, a hankali yace "Humainah?" El-ameen yace "Baka tunanin xata yi exposing din mu, beside wannan me kukan me ma xata iya yi?" Junaid yyi murmushi yace "She won't, matsalar kawai Mumy ce" El-ameen yace "Alright, y not make it look as if gidanmu xaka kai ta gun Ummi, daga nan dai xa mu san yanda za muyi" Junaid yayi shiru sannan yace "Ohk Allah yasa ta yrda" mikewa El-ameen yayi yace "Gud, yanda ku ka yi gobe ka kira ni" Junaid yace "Wait, but kasan da wuri nake barin gida ai" El-ameen yace "However, just make sure gobe around 12 tana gida na or she shud meet me at the clinic" Junaid yace "Wait plss don Allah kamar yaushe kake ganin xata samu lafiya, will it take long?" El-ameen ya wara ido yace "Uhn! Har ka fara gajiya da kashe kudi kenan?" Junaid ya girgixa kai yace "Not at all, ina son ta samu lafiya ta nemo 'yan uwanta case dinta ya fita daga hannuna, har kuma hakan ya kasance bana fatan 'yan gidanmu su san komai" El-ameen ya daga kafada yace "But I hope you weren't daft the other day I was saying it's difficult to predict how, when, or to what degree she's going to get better, dat aside ma kayi addu'ar kar tayi loosing memory idan ma ta samu lafiyan!" Zaro ido Junaid yayi yace "Loosing memory kuma, No No in'sha Allah hankalinta gaba daya xai dawo, if not ya za muyi da 'yar mutane?" El-Ameen yayi murmushi yace "Allah dai ya kiyaye hakan" daga haka ya fice daga parlon yana cewa "Am off!", Junaid ya bisa da kallo sannan ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ya Allah ka ba ma wannan baiwa taka lafiya" mikewa yyi shi ma ya fita, part din Mumy ya shiga ya tarda El-ameen yana ma Mumy sallamah, Mumy tace "Yauwa Ahmad ku fita tare ka siyo min fruits" Junaid yace "Toh Mumy" tare suka fita da El-ameen a motar El-ameen din, Suna isa inda ake saida fruits yyi parking, Junaid ya fita ya siya fruits leda biyu ya dawo motar, ya ajiye ma El-ameen daya yace "For our patient" El-ameen yace "za ka raka ni shopping complex xan siya ma Ummi perfume wai" Junaid yace "Ohk" Suna isa bayan El-ameen yyi parking suka shiga babban mall din, El-ameen ya nufi gun perfumes, ya debi wa enda yasan Umminsa na amfani da, junaid dai binsa kawae yake, Suna isa gun teddy bears manya El-ameen ya dauka wani me kyau yana kallo, Junaid yace "toh fah!" El-ameen yyi murmushi ya ajiye a basket yace "For ur patient" daga haka suka bar wajen, biscuits da chocolates me yawa El-ameen ya dauka a trolley din, shi dai Junaid binsa kawae yake har ya gama daukan abinda xai dauka suka tafi inda ake biyan kudi, Wata yarinya ce tsaye gabansu sanye da hijab har kasa tana rike da basket dinta, gabanta kuma mutane biyu ne, El-ameen ya dawo kusa da Junaid murya can kasa yace "Don Allah ka d'an mata magana kace sauri muke ta bari mu fara biya, dubi fa kayanta da yawa" Junaid yyi masa wani kallo yace "Tunda kai baka da baki sai ni" El-ameen yyi tsaki yace "matsalata da kai kenan kamar ba namiji ba" Junaid bai kuma ce masa komai ba, har aka zo kan yarinyar bude Jakarta tayi xata fito da Atm bayan ta xube kayan da ta siya kan table ana lissafawa, dube dube kawai take a jakar, El-ameen yyi dariya can kasa yace "are you seeing what am seeing frnd?" Sharesa Junaid yayi, yarinyar ta juyo tana duba kasa, Junaid ya tsura mata ido yana tunanin inda ya taba ganinta amma ya k'asa tunawa, juyawa ta kuma yi tana kallon mutumin dake xaune yana jiran kudi tace "Malam Atm card dina ne ban gani ba wllh, kayi hakuri ka ajiye kayan tukun" sai a sannan Junaid ya tuna inda ya taba ganinta ta dalilin muryarta da ya ji, ya laluba jikinsa yaji bai fito da Atm card dinsa ba, kallon na hannun El-ameen dake dariya can kasa yana cewa "Karyar banxa wai bata gani ba" ya warce atm card dinsa ya nufi gun biyan kudin, El-ameen ya xaro ido yace "Kaiii" ko kallonsa Junaid bai yi ba ya mika masu yace "Gashi ku cire kudin ku" kallonsa yarinyar take ita ma tana son tuno inda ta taba ganinsa, su ko tuni suka karbi atm ya danna masu pin suka cire kudinsu har dubu talatin da biyar. A hankali yarinyar tace "Thank you" da alama ta tunasa ita ma, yayi murmushi yace "Never mind, it pays to be kind" Murmushi kawai tayi, ya juya yana ma El-ameen wani irin kallo.
Karasowa Junaid yayi gun El-ameen da ya wani hade rai yana kallonsa, junaid yayi murmushi ganin bai da niyar motsi daga inda yake gashi jiransa ake ya karbi basket din hannunsa ya tafi ya biya kudin kayan ciki, godiya yarinyar ta kuma yi ma Junaid bayan ta dauki kayanta da aka yi packaging a leda ta bar wajen, El-ameen ya bi ta da harara har ta fita, Junaid ya dinga danne dariyarsa har aka masa package din kayan da El-ameen ya siya ya bar wajen yana kallon El-ameen yace "Let move frnd" wani mugun kallo yayi masa yayi gaba ya bar sa a wajen. Junaid ya dinga dariya ya bi bayansa, a waje suka ga yarinyar tsaye bakin motar ta, tana ganin sun fito ta nufe su, Har Junaid xai shiga mota ya tsaya, ta karasowa cikin sakin fuska tace "Am really grateful, Allah ya saka da khairan" xai yi magana yaji El-ameen ya warce ledan hannunsa ya xaga ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, Junaid ya wara ido ya bi motar da kallo, haka ma yarinyar ta bi motar da kallon mamaki, can ta maido da dubanta ga Junaid ta kirkiri murmushi kawai ta juya tace "Sai da safe" ta bar wajen, Junaid ya sauke ajiyar xuciya sai kuma ya d'aga kafada ya bi bayanta, kusan a tare suka shiga motarta, ya kalleta yace "Amm drop me plss idan ba damuwa, abokina ya tafi da motar" ta gyada masa kai tace "Alryt!" Sai da suka hau kan titi sannan tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, ta bude ido tace "Ohh it's very far, mu nan kusa muke, kaga kafin in kai ka in dawo dare xai yi kuma Mum xata min fada ne, but nevertheless bari kawai inyi driving xuwa gida idan ya so sai ka tafi da motar ko gobe sai ka maido min" shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Baxa ace komai a gidanku ba" a hankali tace "I will explain everything to mum" yace "Toh nagode" cikin mintunan da basu wuce goma ba ta iso anguwarsu tayi parking kusa da gate din wani kantamemen gida ta juya tana kallonsa tace "Nan ne gidanmu" yace "Ohhk" bude motar tayi ta fito ta bude back seat ta kwashi kayanta ta rufe tana kallonsa tace "Tohm sai da safe" bude motar yayi ya fito ya dawo driver seat yace "Ohk, alryt! Tnx a lot, but sai da yamma xan maido maki motar don da safe nake fita aiki" tace "Alryt bbu damuwa" har ta fara tafiya yace "Ur Name?" Ta juyo tana kallonsa tace "Hafsat!" Ya gyada kai yace "Nyc name, am Ahmad Junaid!" Ta d'an yi murmushi ta gyada masa kai sannan ta juya ta nufi gate dinsu. Tada motar yayi yayi reverse ya bar anguwar. Sai da ya fara tsayawa gun masu saida fruits ya kuma siya ma Mumy wani fruits din sannan ya kama hanyar gida. A parking lot yyi park din motar sannan ya fito ya nufi part din Mumy, Bbu kowa parlon ya ajiye ledan fruits din ya shiga bedroom din Mumy, ya sameta kwance ya karasa ya xauna gefenta yace "Mumy na dade ko, kiyi hakuri pls ga fruits din can parlor" tace "Ohk na gode" mikewa yayi yace "In kawo maki?" Ta mike ita ma tace "A'a bar shi kawai ban jin xan iya sha kuma bari in sa a fridge" fita tayi daga dakin ya bi bayanta, ya bude bedroom din fatima ya sameta kwance tana waya Humainah kuma tayi bacci, ya karasa dakin yana kallon Humainah, murmushi yayi a xuciyarsa yace "Fitinanniya" ya juya kawai ya fita, a parlor Mumy tace "Gobe idan ka dawo gun aiki wai xaka kai Humainah gidan Aysha, wai baxa ta xauna ba" shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Toh Mumy kar Abba kuma yayi magana" tace "Ae kwana biyu kawai xata yi ka koma ka daukota" bai kuma cewa komai ba, har Mumy ta xuba fruits din cikin fridge sannan yace "Sai da safe Mumy" tace "Allah ya tashe mu lafiya, kayi addu'a kafin ka shiga" yace "In'sha Allah Mum" daga haka ya fice daga parlon. Yana gama shirin kwanciya ya jawo wayarsa ya wani hade rai yayi ma El-ameen transfer din dubu talatin da biyar ya jefar da wayar yayi kwanciyarsa.Washegari da safe Junaid ya rasa yanda xai fara ce ma Mumy xai kai Humainah gidansu El-ameen kamar yanda suka shirya, har ya gama breakfast bai samu courage din gaya mata ba don yasan dole xata zargi abu, Mumy tace "Kana kallon lokaci ma kuwa" da sauri ya mike daga dinning ya dau hularsa da waya yace "Am off Mum" tace "Allah ya tsare, ka shiga gaida Abban ka?" yace "Eh but yana bacci" daga haka ya fice, Hajiya ya gani tsaye da Umma a bangaren Umman suna kallon bakon motar dake ajiye parking lot suna kus kus, duk a tunaninsu sabuwa ce, ko kallonsu bai yi ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga, yana warming motar ya hango Khadija a balconynsu tana shara, y'afito ta yayi, ta ajiye broom din hannunta ta taho, su Umma suka bi ta da harara, gaishesa tayi, yace "akwai maganar da zamu yi dake a waya, you make sure you are alone while picking my call kin ji" tace "Alryt big bro" daga haka ya rufe motarsa, ta koma balcony. Karfe sha daya El-ameen na xaune office dinsa rike da wayarsa yana jujjuayawa da ganinsa kasan ransa a bace yake, kwafa yayi ya ajiye wayar yana tunanin walakancin da xai ma Junaid, shi kansa ya rasa gane dalilin da ya sanya ya kasa cire hannunsa a patient din Junaid, kila don ya fara tausayin yarinyar ne, sake daukar wayar yayi ya kira Junaid for the 5th time, yanxun ma har ya gama ring bai daga ba, El-ameen ya fuzar da iska ya ajiye wayar, toh yanxu ina xae samo Wanda xai kai can gidan ta xauna da ita gashi Karfe sha biyu mama jummai xata tafi, tsaki ya ja ya jawo files din gabansa, why is he even bothering his self this much, tayi ta xama ita kadai a gidan after all ba shi ya ajiyeta ba, kwankwasa office dinsa aka yi ya daga kai yace "Come in" wata nurse ta shigo tace "Sir kana da bakuwa a waje" ya sauke kafarsa daga kan table yace "is she a patient?" Ta girgixa kai tace "I don't think so" yace "Ait, let her in" juyawa tayi ta fita ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo tare da bakuwar, da sallama ta karaso tana murmushi tace "ina yini ya El-ameen" ya sauke ajiyar xuciyar relieve yace "Lafiya khadija," ta xauna saman table dinsa tace "Ya Ahmad yace in xo office in same ka" yace "Ya maki bayani ne?" Tace "Eh daga wajensa ma nake yanxu" kallon agogo yayi ya mike ya dau makullin motarsa yace "Amma Hajiya baxa ta neme ki ba?" Tace "Gidan kawata nace mata xa ni" a tare suka sauko reception, ya kalli nurses din yace "If MD shud ask of me tell him I was called for an emergency" suka amsa masa da yes sir, sannan ya fita khadija na biye da shi duk suka bi sa da kallo, front seat khadija ta bude ta shiga, shi ma ya shiga ya tada motar suka bar haraban hospital din. Sai da suka yi nisa tace "Yaya kai kuma ina ka samo mahaukaciya?" Kallonta yayi, yayi murmushi yace "Tsarin da ya maki kenan?" Ta d'an bude ido tace "Ehh ca yayi min taimakon ta kake, a hanya ka tsince ta" dariya El-ameen yayi yace "Gaskiya ne, amma ae shi ya ban kwarin gwiwan taimaka mata" khadija tace "Toh Allah ya baku lada duka" yace "Ameen," tace "Toh amma Yaya bata ma mutum komai, ni tsoro nake ji" yace "Bata komai yanxu, ta d'an saba da mutane, iyaka yanxu kawai xuwa xa kiyi ki xauna da ita, duk barnar da kika ga xata yi ki hanata, kar kuma ki bari ta fita, sai d'an potatoe da xa ki soya mata ki cika mata ketchup a ciki," a hankali khadija tace "Toh, amma ni dai ina jin tsoro" dariya yayi yace "Ke bata komai, you will like her" suna isa gidan yayi parking a waje ya fita ta bi bayansa, da ganinta kasan a tsorace take, dariya kawai yake har suka shigo parlon, bbu kowa parlon sai ita kadai ga 'yar jakar mama jummai da ta hada kaya duk ta watsar da kayan a parlon, da alamar mama jumman na kitchen, khadija ta labe jikin kofa sai faduwa gabanta yake tana leko parlon, karasowa kusa da ita El-ameen yayi ya fixge jakar yace "Ke idan baki yi barna ba baki ji dadi ba ko" daukar kayan tayi ta mika masa, ya fixge ya ajiye ya xauna ya jawo ta gabansa yace "look. I've brought a new frnd for you, hope xa ku saba da wuri, she's khadija by name" kallonsa kawai take ko kiftawa bata yi, yayi murmushi ganin yanda yayi mata maganar kamar wata me hankali, a hankali ya d'agota ya xaunar da ita gefensa ya juyar da kanta yana nuna mata khadija da taki karasowa murya can kasa yace "A frnd jewel, ur mate" kauda kanta tayi ta xamo kasa xata ci gaba da birkita kayan da take, yayi mata tsawa, da sauri ta dawo jikin kujera tana shisshigewa jiki a tsorace, sosai hakan ya ba khadija da ta kasa daina kallonta dariya, wani tausayinta ya rufeta ganin irin kyanta amma wai ba hankali, mama jummai ta fito tace "A'ah Sannu da xuwa Ahmad, har na fidda ran tafiya yanxu da naga baka xo ba" yace "Warce xata xauna da ita na je daukowa mama, kin ganta can, kanwar Junaid ce" Mama ta kalli khadija tace "Allah sarki, sannu yarinya karaso mana" yayi dariya yace "Wai tsoronta take fa" mama tace "Yo ae ita bata komai wllh" da kyar khadija ta yrda ta shigo tana kallon yarinyar da ita ma ta bi ta da ido, Mama jummai tace "Amma nan xata dinga kwana da ita koh?" El-ameen yace "A'a gaskiya xuwa bayan magrib xata koma gida" "Toh wa xai dinga kwana nan da ita" cewar mama jummai cike da mamaki, ya d'an yi shiru sannan yace "Xan dinga kwana nan ko kuma junaid" mama jummai ta girgixa kai tace "A'a wannan ba mai yiwuwa bane, ko kuma kawae in tafi da ita in dai xa ku yrda wannan ba wani abu bane a gu na" Shiru El-ameen yayi yana kallonta sai kuma yace "Saboda me baxai yiwu ba mama?" Ta xauna tace "A ina addini ya yarje mana da haka d'an nan" xaro ido yayi sai kuma yayi dariya ganin inda xancen nata ya dosa yace "kar ki manta mama ba fa lafiya gareta ba kuma shi ake kokarin ganin an nema mata, karkashin treatment take yanxu, don haka...." ta girgixa kai tace "A'a gaskiya ba wai ina maku shisshigi bane amma bai dace ba, sai dai kawae in hada kayanta mu je kuma na maku alkawarin kwana biyu xamu yi in juyo, kayi mata duk allurorin da xaka mata yanxu" El-ameen ya jinginar da kansa jikin kujera yana murmushi yace "Komai na hannun junaid mama sai yanda yace" tace "Toh kirasa" yana ciro wayarsa kiran Junaid ya shigo ya d'aga, Junaid yace "have you seen khadija?" El-ameen ya hade rai yace "Y weren't you picking my call daxu?" Bbu yabo bbu fallasa Junaid yace "Was very busy, ya ake ciki yanxu?" El-ameen yace "Zaka san you were busy ne, mama dai tace xata tafi da ita don bbu wanda xai dinga kwana da ita a nan," da sauri Junaid yace "What? No, no how can dat be, idan ta kara gaba fa, No she shud leave her xa mu san yanda xa muyi" El-ameen yace "Zaka san yanda xaka yi dai" daga haka ya katse wayar ya kalli mama jummai yace "Kin ji mama wai xai kai ta gun yayarsa ne har ki dawo" mama tace "Atoh hakan ma yayi bari inje to in hada mata kayanta" El-ameen ya bi ta da kallo har ta haura sama, ya juya yana kallon khadija dake ta kallonta ko kiftawar kirki bata yi, yace "Wannan kallon fa" ta kallesa ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "She's so beautiful brother" murmushi yayi bai ce komai ba ya fara danna waya, tace "wace yayar ya Ahmad yake fadi" El-ameen yayi dariya yace "Oho" Mama jummai ta sauko rike da jaka dauke da kaya tace "Ga kayan na hada" El-ameen yace "Sannu mama" kitchen ta shiga ta fito da plate dauke da potatoe da ketchup a gefe ta ajiye gabanta, El-ameen yace "Shikenan mama xa ki iya tafiya kar dare ya maki a hanya" Mama tace "Toh," ta maida dubanta ga khadija tace "Da kin ga ta nufi sama toh kilan bayi take son shiga, ko kuma tana son xuwa ta xuba ruwa jikinta, tana son tea sosai don Allah a dinga mata, sai wannan abun da na soya mata da kunu" Khadija tace "Toh" El-ameen ya ciro dubu talatin ya mika mata yace "Ga kudin mota mama sauran sai kiyi ma mai jego siyayya" dukawa tayi ta karba tana ta sa masa albarka, ta karasa ta shafa kanta tace "Sai na dawo diyata, Allah ubangiji ya yaye maki" kamar taji me tace ta mike da sauri, mama tayi murmushi ta dau jakarta bayan ta gyara kayan da ta xubar mata, tayi wa El-ameen sallama ta nufi kofa, ai da sauri ta bi bayanta El-ameen ya mike yyi dariya yace "ta fa gane tafiya xa Kiyi" shigewa jikin mama tayi, mama tayi dariya tace "Ikon Allah, baxan dade ba 'ya ta jibi xan dawo kin ji" El-ameen ya karasa ya janye ta daga jikin mama ta fasa wani kara xata kwace kanta yayi mata tsawa, tsit tayi tana kallonsa, mama ta juya ta fita cike da tausayinta, yana rike da ita suka koma parlon ya xaunar da ita gefensa hawaye ya gani idonta, khadija ta xamo kasa ganin hakan a hankali tace "She's crying" kallonta yayi yace "Tafi kitchen ki debo min ruwa" mikewa tayi ta nufi kitchen din, tana shiga ya dafata ya lumshe ido a hankali yace "Am sorry jewel, mama xata dawo soon kin ji" dogon hancinsa ya ji ta ja kamar yanda yake mata ya bude ido da sauri, sai kuma yayi murmushi ya lakaci nata hancin a hankali yace "Pretty~Jewel"A hankali ya dago kanta yana kallonta, ya ciro handkerchief aljihunsa ya share mata idonta murya can kasa yace "Am sorry jewel" yana jin fitowar khadija daga kitchen yayi saurin dauke hannunsa a shoulder dinta ya koma baya, ta karaso parlon ta mika masa cup din ruwan, ya amsa ya ajiye sannan ya saukar da ita kasa shi ma ya sauko, dankalin da mama ta ajiye parlon ya jawo ya dauka ya hada da tomatoe ketchup ya kai bakinta, ta sa hannu ta karba ya sake mata, ta lashe tomatoe din, khadija tayi murmushi ta dawo kasa d'an nesa da su ta xauna tana kallonta, haka ta dinga shan tomatoe din kanta a kasa, ya tsura mata ido yana kallo, ta d'ago manyan idonta ta sauke kan nasa, dauke nasa yayi ya mike ya koma kan kujera yace "tafi kitchen ki hado mata tea khadija" khadija ta kama hanyar kitchen yana ganin haka ya kuma saukowa ya dawo ya xauna gabanta ya dau potatoe ya kai mata baki xata kauda kai ya rike kan ya hade rai ya tura mata dankalin yace "Eat!" taunawa ta shiga yi tana kallonsa tana yamutse fuska, ya kalli kofar kitchen sannan ya kalli ragowar ketchup din dake gefen bakinta, ya matso a hankali ya sa yatsa ya kwashe ketchup din ya lumshe idonsa ya kai baki, dai dai nan aka bude kofar parlon, ya koma baya da sauri yana goge bakinsa, Junaid ya shigo parlon, kallo daya yayi masu ya sunkuya ya shiga cire takalmi da safar kafarsa, El-ameen ya mike ya koma kujera yana shafa kai, karasowa cikin parlon Junaid yayi, yana sanye da trouser din uniform dinsa sai farin polo, El-ameen na kallonsa yace "Gud you came, so ya xaka yi da ita da nyt?" Xaunawa Junaid yayi bai ce komai ba, ta dauki plate din gabanta ta mike ta dawo kusa da shi ta daura kan kafarsa, murmushi ya d'an yi ya rike plate din yace "No! Thank you" El-ameen ya dauke kai hade da tabe baki, khadija ta fito rike da cup din tea ta ajiye tana kallon Junaid tace "Welcm bro" yace "Thank you, how about you telling Hajiya you will be spending the nyt at ur frnd's place?" Shiru tayi sannan ta langwabar da kai ta xauna tace "Kasan Abba yana nan" shafa kansa yayi bai ce komai ba ya dauke plate din da ta daura masa a kafa ya ajiye kasa, El-ameen ya d'aga kafada ya mike ya haura sama, kallon khadija Junaid yayi, tayi murmushi tace "Wai yaya ka ban labarin inda Ku ka ganta mana, dama kun santa ne?" Junaid yace "I donno for El-ameen" tablets dinta El-ameen ya dauko a sama ya dawo parlon, sai da ya fara shiga kitchen yayi diluting dinsu sannan ya fito, ba musu ta bude baki ya juye mata tana yatsina fuska, Khadija tayi murmushi ta daura kanta jikin Junaid a hankali tace "I like her Ya A.jay" murmushi yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "I will be going back to clinic yanxu, nan da thirty mins xata yi bacci, duk inda ta kwanta ki kyaleta kawai" a hankali khadija tace "Ni fa ina jin tsoro, tafiya duk xa ku yi ku bar mu" El-ameen ya harareta yace "An ce maki bata komai da'alla" Junaid ya tashi shima yace "Baxata maki komai ba sister, am also leaving" shiru tayi bata ce komai ba, El-ameen yayi hanyar kofar, Junaid ya bi bayansa, da sauri ta mike ta nufe su khadija ta bi ta da kallo gabanta na faduwa, gun Junaid ta nufa, El-ameen ya juya yana kallonsu, shima Junaid kallonta ya tsaya yi, tsaki El-ameen yayi ya xaro mata ido yace "C'mon koma kar in baki knock" kara ta saki kamar ta ji abinda yace, El-ameen ya fice daga parlon, Junaid yayi murmushi ya kama hannunta suka koma parlon ya xaunar da ita yana kallonta yace "Look Jasmine xa mu dawo anjima kin ji, khadija will be staying with you har mu dawo" Khadija tace "Waow yaya sunanta Jasmine?" Da sauri ya kalleta don ya manta gaba daya tana gun, yace "Ohh! Did I call her dat" khadija tayi dariya tace "Ehh mana" ya mike yace "No I didn't" ihu ta fasa ta mike da sauri ganin ya tashi, Khadija ta langwabar da kai tace "Yaya ba ka baro gun aiki ba, stay with her plss, bata son ka tafi" yace "Am hungry, gida nake son tafiya in ci abinci" khadija tace "Ae Akwae food stuffs a nan ba sai in girka maka ba" shiru yayi sannan yace "Alryt ki min indomie kawai" tace "Toh" ta mike ta shiga kitchen, xaunawa yayi ya xaunar da ita gefensa yayi murmushi ya ja dogon hancinta yace "I will stay with you Jasmine" suna nan xaune har khadija ta dawo parlon rike da tray me dauke da indomie da fried egg a gefe sai roban ruwa da cup ta ajiye kasa tace "Gashi yaya" saukowa kasa yayi ita ma ya sauko da ita suka xauna sai kallon indomien take kamar idonta xai fito, murmushi yyi ya kalli Khadija yace "Ke baxa ki ci ba" ta girgixa masa kai tace "Na koshi" daukar fork din yayi ya debi indomie kadan ya kai mata baki bayan ya d'an huce, wani kara da yasa shi sakin fork din tayi khadija ta mike da sauri ta bar wajen, ta dinga ihu tana komawa baya tana kallon indomien duk ta ruda shi, ya riketa yana cewa "What happen jasmine, bakya so ne" ihu kawae take tana komawa baya, ya kalli khadija yace "Take it away" dauka tayi ta nufi kitchen da sauri, tsit tayi ta bi khadija da kallo, ta dawo kusa da shi ta xauna, shi kam kallon mamaki kawai yake mata, hannu ta sa ta taba long lashes dinsa, yayi murmushi ya cire hannunta yace "Indomie kike tsoro Jasmine" khadija ta fito tace "Yaya kila tsoron shi take ji, kaje kitchen ka ci" ya girgixa kai yace "no idan naje gida xan ci abincin" kallonta Junaid yayi jin ta jingina jikinsa ya ga bacci ya fara daukarta, ya mike ya kwantar da ita kan kujeran, khadija tace "Baxa ta fadi ba yaya?" Yace "Ehh, bari in tafi gida in dawo yanxu tun da tayi bacci" a hankali khadija tace "Toh amma ka dawo kafin ta tashi plss Allah tsoronta nake ji" Junaid yace "Ohk" yana fita ta dawo kusa da ita a hankali ta xauna tana kare mata kallo, doguwa ce yar siririya da ita, ta tsura ma kyakkyawan fuskarta ido da d'an karamin jan bakinta dake sheki, Khadija ta kama long fingers dinta a hankali tace "I like you sister, Allah ya baki lafiya" kallon hular kanta tayi ta dawo wajen ta d'an cire hular tana lekan kanta ta ga bakin gashinta sai sheki yake, fito da gashin ta shiga yi ta bude ido ganin tsayin gashin, ta lumshe ido tace "Waoww!" Haka tayi ta xama kusa da ita tana kallonta, komai na jikinta me kyau ne, mamaki ta dinga yi inda suka samota har suke son warkar da ita, to yan uwanta fa?? Mikewa tayi jin ana kiran la'asar taje tayi alwala tayi sallah, sannan ta d'an gyara gidan ta dawo ta xauna ta ci gaba da kallonta daga inda ta tsaya, bude kofa taji anyi ta juya da sauri, taga El-ameen ne, ya karaso parlon yace "Capt ya tafi ne" ta gyada masa kai, ya iso kusa da su yana kallonta yace "She's still sleeping koh?" Ta gyada masa kai, ajiye ledan hannunsa yayi ya tada ta ya tafi sama da ita, khadija ta hade rai ta bi sa da kallo, haka kawae taji haushin abinda yayi, ta ja tsaki ta dauke kanta hade da tabe baki ta mike ta koma kujera ta xauna, ba a dau lokaci ba ya sauko, kallonta ya tsaya yi ganin yanda ta hade rai yace "Ke in kin gaji ne tashi ki tafi gidan ku" mikewa tayi ta dau Jakarta ta fice fuu, yayi tsaki ya dau wayarsa da ke ring. Tana fita ta kira Junaid yana d'agawa yace "Ta tashi ne?" tace "Wani tashi? Bayan ya wani ce wai in tafi" Junaid yace "Wa?" Tace "Ya El-ameen mana, wai wani in tafi gida" shiru ya d'an yi kafin yace "Saboda me?" Tace "Oho masa, ya wani dauketa ya kai ta daki bayan bacci take" mikewa Junaid yayi daga zaunen da yake parlon Mumy yace "daki kuma, ke kina ina?" Khadija tace "Ehh mana, ni na riga na fito ma tafiyata xan yi" katse wayar yayi kawai ya ajiye, Mumy dake ta kallonsa tace "Wani dakin? Kuma da wa kake waya" Kallonta yayi da sauri don ya mance tana wajen yace "Ohh dama, dama na aiketa ne, shine... no wai ce min tayi yayarta ta kulle ta a daki, khadija ce" Mumy na masa wani irin kallo tace "Karya kake" ya xaro ido yace "Mumy karya kuma" ta girgixa kai tace "Ahmad am beginning to suspect you this days, behaviours dinka sun fara canxawa, i notice kana boye min wani abu, but be careful" daga haka ta shiga bedroom, Humainah dake xaune parlon ita ma tana gyada kai tace "ta tashi ne? uhnn ko waye ya tashi oho, daki kuma? Uhnn ko wani dakin yake nufi oho, ke kina ina? Uhn ko wacece haka oho, hmm we are beginning to suspect you this days Captain be careful" wani harara ya watsa mata ta mike tayi masa gwalo tace "In tayi tsami ma ji dai" da sauri ta shige dakin Mumy ita ma. Ya shafa kansa a hankali don yasan ko hauka yake baxae bari Mumy taji xancen mahaukaciyar nan ba, tabdi! mikewa yayi da sauri ya dau makullin motarsa ya fita, waje ya fita don bai shigo da motarsa compound ba ya hau motar ya nufi gidan El-ameen, cikin few mins ya isa, yana Parkin ya fito ya shiga gidan, xaune ya tarda El-ameen balcony yana waya, ya tsaya yana kallonsa har ya gama ya hade rai yace "Y did you send khadija away?" El-ameen yace "Haka tace maka, to let me get hold of her" Juyawa Junaid yayi jin an bude gate, wata mace da baxata wuce 27 ba ta shigo, ta karaso balcony ta gaida Junaid, ya gyada mata kai kawai, mikewa El-ameen yayi yace "Welcm, ki shiga daga ciki" ba musu ta shiga parlon, El-ameen yace "we are hiring her for 2 dayz kafin Mama ta dawo, sai ka biyata 10k, old nurse din clinic din mu ce" Junaid ya daga shoulder yace "Anyhow" juyawa yayi yace "sai gobe, na tafi" El-ameen yace "Wato xuwa Kayi ka ga what I was up to da nace khadija ta tafi koh?" Junaid yayi murmushi bai ce komai ba yayi gaba abunsa, El-ameen yayi kwafa ya shiga parlon. Karfe shidda da wani abu Junaid ya shigo gida, ya ga khadija tsaye nesa da balconynsu, Hajiya da Umma na xaune sai Sadiya da Suhaima, Sadiya sai cewa take "Kawai ki bar min komai a hannuna Hajiya idan na lallasa ta xata fadi inda taje wllh" Umma tace " Ni tun da ta fara mu'amala da shegiyar 'yar da aka kawo gidan nan Humainah take kowa, dabi'un ta suka canxa, ke har kin kai matsayin da xa Kiyi karyan xuwa gidan kawa ki fita tun safe sai yanxu kike shigo mana gida don Kazan ki" junaid ya karasa wajen ya gaida su yace "Hajiya tare muka fita, ta rakani ne" Umma ta watsa masa wani kallo tace "Da yake ba Aysha bace ko Fatima dole ka kareta mu bar ta ta lalace" Juyawa khadija tayi fuu ta nufi part din Mumy, Hajiya ta shiga kwala mata kira tana cewa "Kika kuskura kika shiga wajen nan mai raba ni da ke sai Allah, kuma wllh kin ji na rantse sai kin fadi daga inda kike"


Junaid ya juya shi ma ya bar wajen, Hajiya ta bi bayan khadija tana huci, a balcony ta tsaya ta tura kofar tana cewa "Kar ki bari in shigo parlon nan khadija, tun muna mu biyu ki fito ki wuce" tsayawa Junayd yayi yana kallon ikon Allah, Humainah dake xuge jakar kayanta da ta gama hadawa a parlor ta tabe baki ta mike, ta dauki remote din TV ta kure maganar gaba daya, Hajiya ta xaro ido tana kallonta, ji take kamar ta shaketa kawai ta huta, can dai tace "Ke wai ni sa'ar uwar ki ce kika raina ni haka a gidan nan, ina magana za ki kure min TV?" Humainah ta rike kugu tace "Ni ba dai uwata ba wllh" Sadiya ta karaso bakin kofar parlon tana cewa "Bata fito bane Hajiya" Hajiya ta fashe da kuka tace "Yanxu ni yarinyar nan take ma rashin kunya Sadiya, a haihuwar kaji ban yi jika da shegiyar ba" a fusace Sadiya ta shige parlon tayi kan Humainah, Junaid na ganin haka ya bi bayanta, ai tuni Humainah tayi dakin Mumy da gudu tana kwala mata kira, hakan kuma bai hana Sadiya bin ta ba tana kunduma mata xagi, wani tsawa Junaid yayi mata tun kan ta shiga dakin Mumy ya fixgota ya nuna mata kofa yace "Get out, ko a mafarki kika kuskura kika yi attempt din t'aba ta wllh sai na ba66allaki a gidan nan" kallonsa kawai take fuskar nan nata daure don tasan tana iya magana yanxu ta sha mari, Hajiya ta shigo parlon tana huci tace "Wllh Ahmad idan ka bari na saka ka gaba a gidan nan sai xaman duniyar nan gaba daya ta gagare ka, kayi hankali da ni ka bi ni a hankali, bani da kyau wllh, amma in dai ni ce mu je xuwa sai ka gwammace uwar ka bata haifo ka gidan nan ba, xaka san da ni kake" Mumy ta fito tana ma Hajiya wani kallo tace "Babu abinda kika isa ki masa wanda Allah bai masa ba, mu da Allah muka dogara, aniyar ki ta bi ki kuma" Hajiya tayi shewa tana murmushi tace "Toh mu xuba da ku," daga haka ta juya fuu ta fice, Sadiya ta bi bayanta. Junaid ya girgixa kai ya juya ya fice daga parlon, shi gaba daya xaman gidan ma ya ishe sa kawai. Mumy ta kwalo ma Humainah kira ta fito, strictly tace "ina raba ki da mutanen nan baki ji ko Humainah, ina ruwan ki da su wai da har xaki dinga shiga tsabgarsu, kinsan Allah baxa mu shirya ba idan magana za ki dinga dauko min, so kike su sa ki gaba kema koh? To maxa gama hada kayan ki yanxun nan Ahmad ya tafi da ke inda xai kai ki kafin Abba ya dawo su kuma hada ki da shi" Juyawa Humainah tayi ta koma daki kamar xata yi kuka, Khadija ta fito daga daki tace "Mumy kiyi hakuri," Mumy tace "Kinga idan kin yi laifi ki daina yo wa nan khadija, sai ki tsaya can ki basu hakuri" Khadija ta turo baki ta koma dakin su fatima. Junaid na shigowa bayan yayi wanka ya canxa kaya Mumy tace "Maxa kai ta gidan Aisha kan dare yayi Ahmad" ya kalli agogo don dama fita xai yi ya maida motar jiya, yace "Toh Mumy" Mumy ta kwalo ma Humainah kira tace "Dauko jakar ki da hijab" tana kumbure kumbure ta fito rike da 'yar jakar kayanta da Hijab, Junaid ya mike yace "Sai na dawo Mumy" Mumy tace "Allah ya kiyaye, amma motar waye ka dawo gidan nan jiya da?" Ya d'an shafa kai yace "A frnd, idan na ajiyeta xan mayar ne ma" Mumy tace "Ohk," ya fita Humainah na biye da shi a baya, Mumy tayi murmushi tace "Ba sallama Humainah" kamar xata yi kuka ta daga mata hannu ta fice, Mumy tayi dariya tace "Lallai Humainah" As usual Hajiya da Umma na balcony, duk suka bi su da hararan tsana, tsayawa yayi har Humainah ta karaso inda yake ya karbi jakar hannunta suka nufi parking lot, Umma ta kalli Hajiya tace "Ke wllh naga kamar sonta yake, dubi fa har da wani rike mata jaka, sai ya iya yiwuwa ma ya fito da ita a matsayin warce xai aura idan lokacin da Alhaji ya dibar masa yayi" Hajiya ta xaro ido tace "Ae ko da mun banu mun lalace, meye abun yi Bilki?" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "ba mu ga ta xama ba," Humainah ta kalli motar da Junaid ya shiga tace "Motar waye wannan?" Kallonta yayi ya bude ido yace "Naki" ta hararesa ta xaga ta shiga, yana warming motar ya kira El-ameen, bugu biyu ya d'aga, Yace "kana ina ne Dr?" El-ameen yace "ina gida" Junaid yace "Ohk plss ka fito mu hadu kasan layin ku" El-ameen yace "Why?" Junaid yace "kai dai ka fito, it's urgent, kuma ka taho da motarka" daga haka ya katse wayar, ya ja motar suka bar gidan, Humainah tace "Amma ya Ahmad gidan Anty Aysha aka ce ka kai ni fa xaka wani ce ku hadu a kasan layi, to yawo xaka yi da ni a mota" ba tare da ya kalleta ba yace "Ni tricycle ma zan je in saka ki yanxu ya kai ki" ta xaro ido tace "Ehh!" Yace "Yess!" yana isa layin su El-ameen ya hango motarsa ya isa gun motar yayi parking ya fito, xuge glass El-ameen yayi yana kallonsa a bit surprise yace "Whose car is dat?" Junaid yace "A good samaritan's, jiya da ka yasar da ni a titi ka wuce...." El-ameen yayi tsaki yace "Kayi mugun bata min rai jiyan nan, don me yarinya xata shirga karya wai ta mance Atm card a gida ka yi amfani da kudina ka biya uban kayan da ta siya" Junaid yace "Ba dai na mayar maka da kayan ka ba, keep dat matter aside kar kayi provoking dina" El-ameen ya tabe baki yace "Ni Mama jummai ma na ba kudin da xata tafi daxu, and dat's ur responsibility not mine" Junaid yace "Whatever, gidan Aisha xaka taimaka ka kai budurwar nan taka, ni ina son maida motan mutane ne kar ayi tunanin guduwa nayi da shi" El-ameen ya leka motar suka hada ido da Humainah, da sauri ya dauke kai ya bude ido yana kallon Junaid, Junaid yayi 'yar dariya yace "Ehh ita din ce" daga haka ya juya yana kallon Humainah da ta hade rai cikin mota ya duka yana kallonta da kyau yace " Oya fito saurayin ki ya kai ki ni....." Kuka ta sakar masa tana yarfe hannu tace "Wayyo ni, wallahi kai aka ce ka kaini bbu inda xan bin sa" ya bude ido yace "Ke ba motata bace wannan, xan maida ma me shi ne" ta marairaice masa cikin sigar shagwaba tace "Plss mana ya Ahmad don Allah ka kaini" murmushi kawai yake yana kallonta, can ya mike ya juya gun motar El-ameen da ya wani hade ya daga kafada yace "Kaji wai tsoronka take ashe, don haka plss frnd just excort me in maida motar sai mu tafi gidan Ayshan da naka motar" El-ameen yayi masa wani kallo yace "I don't have dat time, dama kiran da ka min kenan?" Junaid yayi murmushi yace "Toh shikenan, idan mun je can xa mu samu tricycle" daga haka ya xaga ya koma driver seat ya tada motar ya bar layin, tsaki El-ameen yayi ya bi motar da harara can ya tada nasa motar ya bi bayansa, Junaid na ganin haka yayi murmushi don dama yasan sai ya biyo sa. Cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba ya iso layinsu Hafsat, yayi parking inda tayi jiya, ya fara kalle kalle don bai karbi numberta ba, Humainah tace "Ya Ahmad ina ne nan" yace "gidan su budurwata" kallonsa kawai take ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata ta fito, dai dai nan El-ameen ma ya fito ya rungume hannu ya hade rai yana kallonsa, murmushi Junaid yayi ya daga kafada ya nufi gate din gidan, yana danna bell maigadi ya leko, Junaid yace "Amm ina yini, Hafsat nake nema a gidan nan," Mai gadin yace "Toh bari a mata magana" komawa Junaid yayi kusa da El-ameen ya tsaya yace "Da ma ka saki ranka kar Humainah tace ta fasa" shi dai El-ameen bai tanka sa ba, Humainah kam ko kallonsu bata yi ba, bude gate din gidan aka yi ta fito sanye da jan atamfa sai farin Hijab, xaro ido El-ameen yayi yana kallonta sai kuma ya kalli Junaid, murmushi tayi ganin Junaid sai dai lokaci daya murmushin ya bace ganin El-ameen gefensa da tayi, ta karaso kusa da su ta gaida su, Junaid ne kadai ya amsa don shi El-ameen juyawa ma yayi ya shige motarsa, banda kallonta babu abinda Humainah take, Junaid ya shafa kansa yace "Ga motar ki, tnx a plenty, am grateful" ta kirkiri murmushi kawai tana gyada masa kai, ya mika mata makullin motar ta karba, ya kalli Humainah yace "ga kanwata can ku gaisa" karasawa tayi gun Humainah tana kallonta murmushi dauke fuskarta tace "Sannu, ina yini?" Humainah ta dauke kai babu yabo bbu fallasa tace "Lafiya" juyawa tayi ta bar wajen duk jikinta yayi sanyi, ta kalli Junaid tace "Toh nagode" yace "Ni ne da godiya" kallon Humainah yayi yace "Taho mu wuce" kamar xata tashi sama ta karaso ta bude bayan motar El-ameen ta shige, Junaid ya ciro wayarsa ya mika ma Hafsat yace "Sa man digit dinki mu dinga xumunci" karba tayi ta sa numberta ta mika masa suka hada ido da El-ameen dake kallonsu, da sauri ta dauke kanta, shi ko ya tabe baki, Junaid ya mata godiya ya xaga ya bude front seat ya xauna, El-ameen ya figi motar suka bar layin. Sai da suka hau main road El-ameen yace "Da nasan inda xaka kenan wllh ban xuwa, yaushe ka xama haka Captain, yaushe ka fara ware ma mace lokacin ka har da wani karban numberta, Tabdi" har suka iso gidan Aysha ana kiraye kirayen Magrib Junaid bai ce ma El-ameen komai ba, ya juya yana kallon Humainah yace "Toh gashi mun kawo, ki gaida ta" daukar jakarta tayi ta bude motar ta fice ta nufi gate, Junaid ya bi ta da kallo sai kuma ya bude motar ya bi bayanta, tsaki El-ameen ya ja ya danna masa horn, har gate Junaid ya shiga ya fixgota ta hade rai tace "Meye kuma" ya wara ido xai yi magana, ta fashe da kuka, kallonta ya tsaya yi, can ya d'ago kanta yace "What happen?" Ta fixge hannunta taki cewa komai, yace "Baki son xama gun Ayshan ne kuma?" Ta girgixa masa kai tana goge hawayen dake kuma sakko mata tace "To wace wannan yarinya" kallonta kawai yake sai kuma yayi murmushi ya ciro wayarsa daya a aljihu ya mika mata yace "Anjima xan kira ki in gaya maki wacece" juyawa tayi zata bar wajen ba tare da ta karba wayar ba, ya kuma dawo da ita ta fashe da kuka, murmushi yayi ya kama hannunta ya saka wayar, ya juya ya fita daga gate din don El-ameen ya danna horn ya kusa sau biyar, yana shiga motar El-ameen ya figi motar yana cewa "Wai meyasa kake min abinda ka ga dama ne Capt, ka wani shanya ni a mota kana biye ma karamar yarinya 'yar cikin ka, ga baiwar Allah can ko abinci nasan bata ci ba...." Junaid yace "Budurwar ka fa na rako" El-ameen ya tabe baki yace "No, ni ban ce ina sonta ba kawai nace tana da kyau ne, kuma ni ba budurwa ta bace, warce nake so ma ta fi ta komai" dariya Junaid yayi yace "Xa ma ka fadi gaskiya ne, a ina ka samo warce kake son kai da kake tsoron mata" El-ameen yace "Am serious, ni bana son mace me tsiwa da jaraba, warce nake so is very gentle...." Junaid yayi dariya yace "Ita ma bata son mai tsoron mace" El-ameen yayi tsaki yace "Can gidan fa nake son in je don nasan baxata ci abinci ba sai naje shine ka wani bata min lokaci" Junaid ya tabe baki yace "Irin kamar ka damu da ita din nan koh" El-ameen yace "Of course na damu, nama fi ka, kai da baka da aiki sai na bada kudi, ni kuma lokacina gaba daya na bata, a yanxu haka I know her likes nd dislikes, duk motsin da xata yi nasan me yake nufi, I've studied her more than you can imagine, kai you are only showing dat you are a millionaire kana nuna kai kadai ma xaka iya kashe ko nawa ne ba sai ka nemi assistant ba, ni kuma...." Junaid ya ja tsaki yace "Aikin banxa kenan, don without that money you are talking about all this you are listing won't come to action, kai da kake kyashin kashe mata naira biyar din ka, my frnd ka daina listing kan ka a wa enda suka taimake ta ma a rayuwa, you are only decieving ur self, coz I hired you and am paying you for the job, yau nace bana bukatan service dinka you are gonna quit!" Parking El-ameen yayi yana kallonsa yace "Haka kace Ahmad?"


Junaid yayi dariya yace "Of course haka nace ko nayi karya, ka fadi sisin da ka taba kashe mata in biya ka, kai yanxu har ka nuna mun ka fi ni damuwa da ita, wanda da na biye ka tun farko da baxa mu daukota ba ma, wani irin discourage dina ne baka yi ba, wani irin dariya ne baka min ba kan yarinyar nan..." El-ameen bai ce komai ba ya ci gaba da tukin sa, banda dariya babu abinda Junaid yake, ganin El-ameen hanyar gidansu ya nufa Junaid yace "Ohh ka fasa xuwa ka bata abincin ne?" Shi dai El-ameen bai tanka sa ba har ya isa bakin gate din gidansu, ya juya yana kallonsa yace "Idan kaga na kuma bi ta kan patient dinka, ka gaya min wanda ya fi wannan," daga haka ya fice daga motar ya shige gida. Junaid yayi murmushi yana shafa kansa yace "Uhum wai fushi yayi?" D'aga kafada yayi ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, gida shi ma ya nufa abun sa. Washegari Junaid na gun aiki ya dinga kiran El-ameen ya ki d'agawa, shi dariya ma abun ke basa, don bai ga abun fushi ba daga fadin gaskiya, Karfe biyar ya baro gun aiki, ya canxa uniform din jikinsa xuwa mofti ya tafi can gidan nasa, a hankali ya tura kofar parlon, nurse din dake kula da ita na tattare biscuits din da yayi littering din tsakar parlon, ita kuma tana kwance nan kasa tana bacci, Junaid ya karaso ya amsa gaisuwar da nurse din ke masa yace "Dr El-ameen ya xo yau kuwa?" Ta girgixa kai tace "Bai xo ba, na kirasa ma he's not responding" Junaid yayi murmushi ya xauna yace "Ohk, amma ta ci abinci?" Nan ma ta girgixa masa kai tace "tun jiya ma taki cin komai, kaga biscuit din nan ma na fiddo mata shima bata ci ba ta watsar, yanxun ma da kyar ta kwanta tun safe taki xama na rasa me take nema, duk ta ki yarda da ni" Junaid yace "Ohk, me yace maki ta fi so, I mean abinda take ci?" Tace "Kasan yace xai dawo jiya toh bai dawo ba bare ya gaya min, kuma duk yau ba a mata allura ba tunda bai gaya min yanda zan yi ba" Tabe baki Junaid yayi ya mike ya fice daga parlon. Gidansu El-ameen ya nufa Ummi tace ai tun safe yana clinic, ya mata sallama ya fito ya kama hanyar clinic din, Yana isa nurses din dake reception suka ce masa ai baya nan, yace "Ohk haka yace maku ku ce min idan na xo" kallonsa suka tsaya yi, ya haura sama ya tafi office dinsa, ya murda kofa yaji da gasken baya nan, tsaki yayi ya sauko ya fice daga asibitin, a mota ya dinga kiransa ya ki dagawa, shi ya rasa abun jin haushi a maganarsu ta jiya, daga fadin gaskiya, tsaki yayi ya tada motarsa ya tafi gida abun sa. Wasa wasa har 2 dayz El-ameen yaki xuwa can gidan, ya ma kashe wayoyinsa gaba daya, shi ma Junaid ya fita harkarsa bai kuma bin ta kansa ba, matsalarsa daya yanda Jasmine taki cin komai, gashi da ganinta xaka san abu na damunta, duk taki sakin jiki, though in yaje gidan da yamma ta kan je ta kwanta gefensa ko ta xauna kusa da shi, amma duk yanda xai yi da ita ta ci abinci bata ci, sai dai k'adan shi ma da kyar, in ya takurata tayi masa ihu, bini bini xaka ga ta kalli kofa ko taje can ta tsaya kamar dai tana jiran wani, on the third day Mama jummai ta dawo ya sallami nurse din, yasan yanxun xata fara cin abincin tunda ga mama jummai kila dama don bata saba da nurse din bane amma sai yaga otherwise don yi ma tayi kamar bata taba ganin mama jumman ba, ta kuma ki cin abincin still, da mama jummai ta tambaye Junaid El-Ameen ce mata yayi, yayi tafiya ne, duk abinda mama jummai tasan tana so sai da ta yi ta bata duk taki sai ketchup da take ta sha, duk baiwar Allahn ta rame. Yau Junaid na barin gun aiki ya nufi gidansu Faisal, yayi sa'an shi ma dawowan shi daga aiki kenan, Faisal yayi mamakin ganinsa barin da yaga ko canja uniform din jikinsa bai yi ba. Junaid ya xauna bayan sun gaisa yace "Ina son muyi wata magana da kai ne frnd" Faisal ya maida hankalinsa sosai yace "Am ol ears" Junaid ya shafa kai a nutse ya soma basa labarin mahaukaciyar tun daga farkon haduwarsa da ita, Faisal ya kwalalo ido yana kallonsa baki bude, har Junaid ya kai karshen labarin yana murmushi, Faisal ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace "Babban magana, but El-ameen bai kyauta ba, kuma ni ban ga abun fushi a nan ba, sabon da tayi da shi ne ya hanata sakin jiki da bata ganinsa, shiyasa take kin cin abinci!" Junaid ya tabe baki yace "Yanxu dai you are a Doctor, so nake plss ka gaya min yanda xaman psychiatry yake, is it advisable in kai ta can babu matsala?" Faisal ya kuma sauke wani ajiyar xuciyar yace "Gaskiya ina ga na gida kamar yanda El-ameen ke mata ya fi, kuma gashi har ta saba da shi samun lafiyarta ba lallai ya dau lokaci ba, yanxu dai kar ka damu xan je in same sa, nasan..." Junaid yace "No! no bana bukatan sa kuma, he shud hold on to his medication, idan taje psychiatry din suma xata saba da su" murmushi Faisal yayi, Junaid ya mike yace "Plss ka binkitar min psychiatryn da ka ga is ohk... I might come back later ko kuma in kira ka. Don yanxu Mumy xata fara kirana its almost six o'clock" Faisal ya bi sa da kallo har ya fita sannan ya shafa kai yace "Lallai Junaid da El-ameen, mahaukaciya kuma???" Mikewa yayi shi ma ya dau makullin motarsa ya fita xuwa gidansu El-ameen din, Ummi ce da Sumayya xaune parlor, ya gaida Ummi, ta amsa da fara'a tana tambayarsa mutan gida yace "Duk Suna lafiya Ummi, El-ameen na nan kuwa" tace "Ehh yana daki" dakinsa ya nufa ya tura kofar ya shiga da sallama, Ummi ta kalli Sumayya tace "Ki kai masa drink, ki tambayesa ko xai ci abinci" mikewa tayi ta nufi kitchen, kwance faisal ya sami El-Ameen da laptop a gefensa sai dai wayarsa yake dannawa, El-Ameen ya mike xaune ganinsa, Faisal yana murmushi ya karaso ya xauna gefensa yace "Yane the great Dr Ahmad El-ameen" El-ameen yayi murmushi shi ma ya mike xaune yace "Daga ina haka da yamma?" Faisal na kallon fuskarsa ganin yanda manyan idanuwansa suka fito yace "You look pale, are you ohk?" El-ameen ya lashe lebbensa yace "Stress ne frnd, ya aikin?" Faisal yace "Alhmdllh, Ya captain naka...." Dai dai sanda Sumayya ke kokarin shigowa dakin da faranti me dauke da drink da ruwa jin an ambaci Junaid ta tabe baki ta tsaya jikin kofar, El-ameen yace "Yana gidansu!" Faisal yayi dariya yace "Kuna nan har yanxu kamar 'yan biyu abun ku" El-ameen yayi murmushi yace "Sure!" Faisal yace "Uhmm!" El-ameen na kallonsa yace "Ya aka yi?" Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Bana tunanin akwai abinda ya isa ya hada ka da Captain..." Sumayya ta gyara tsayuwa da kyau ta baxa kunnuwa, El-ameen yace "Ban fahimta ba" Faisal yace "Daxu ya xo ya sameni ya kuma ban labarin baiwar Allahn da ku ke kokarin ganin kun ceto rayuwarta daga....." El-ameen ya katse sa yace "No! Da yake kokarin ganin ya ceto rayuwarta dai" Faisal yayi murmushi yace "Haba Dr, bayanin da Captain yayi min is not enough ace kayi fushi haka, kuma naga kun saba haka a tsakanin ku, kar ka manta lada ba kadan ba xaka samu idan yarinyar nan ta dawo hankalinta" El-ameen yace "No ni bn yi fushi ba faisal, just dat nayi quit ne, ya nemi wani likitan ko ya kai ta psychiatry..." Faisal yace "No pls, kar kace haka Dr, ba don Junaid xaka yi ba don Allah xaka yi...." El-ameen yayi murmushi yana girgixa kai yace "You know what?" Faisal ya girgixa kai, yace "Wllh wllh ban yi kuma, I've quit, he shud take her to the psychiatry, ka dai ji rantsuwar musulmi na maka, but babu damuwa xai iya ci gaba da amfani da gidana" Sumayya dake jikin kofa har lokacin duk tayi confuse ta rasa gane kan maganar, to wace yarinya suke magana a kai, yanke shawaran kiran Suhaima tayi tasan xata bata labari, El-ameen ya mike yace "kaga am going to clinic yanxu faisal" faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Ban ji dadin rantsuwar da kayi ba El-ameen, don Allah xaka yi ba don Junaid ba" El-ameen ya koma ya xauna yace "Look faisal, kullum! I mean everyday, karfe bakwae na safe baya karasawa nake barin gida in tafi gun yarinyar don akwai injections din da nake mata a lokacin, before leaving kuma sai na tabbatar tayi breakfast dat's around to eight, ina barin gidan xan kuma dawowa nan gida inyi wanka in shirya inyi breakfast snn in tafi clinic, a can clinic duk abinda nake da xaran sha daya da rabi yayi xan bari koma meye kuwa in tafi gun yarinyar don bata drugs dinta, in tilasta ta taci abinci sannan in kuma komawa clinic, duk abinda nake Karfe uku da rabi xan bari in kuma komawa gun yarinyar don bata drugs, sannan in sake komawa asibiti, Karfe bakwai da rabi a gidana yake min don a wannan lokacin ma tana da injections, baxan kuma bar gidan ba sai after ten don kafin ta kwanta Akwae drugs da xata sha, kasan sau nawa Junaid ke xuwa gidan?" Faisal yayi shiru yana kallonsa, El-ameen yace "Sau daya! shi ma sai da yamma ko kuma after magrib, kuma da ya xo xaka yi tunanin tsikararsa ake a gidan da kayi magana yace maka Mumy, ni ne ban san dadin tawa Mumyn ba, kasan matsalar da nake fuskanta yanxu gun parent dina kan yarinyar nan kuwa? yace ko biyar ban taba kashe mata ba I agree kuma dat is as a result of yana nuna shi me kudine, baya bukatan assistant din kowa, kasan dai yanda yake abubuwansa na girman kai, ni kuma kallonsa kawai nake don in kudin account dinsa sun yi wuta wllh basu wuce million uku ba in ma sun kai, kuma medication din hauka ba karamin kudi mutum xai kashe ba, yau da gobe yana cire dubu Dari dubu hamsin dubu dari biyu, dole kudin xai yi kasa, at dat time ko waye ubansa dole xai ce min i shud help ni kuma hakan nake jira dama, don kai kanka kasan waye ni idan baka tambayeni ba wllh baxan baka ba, in ko ka tambaya ko last card dina ne xan baka, kuma yace inyi excluding kai na a wa enda suka taimaketa a rayuwa tuni nayi hakan, don haka ka rakasa ya kaita psychiatry kawai frnd"Mikewa faisal yayi ya d'aga kafada ya nufi kofa, da sauri Sumayya ta bar jikin kofar ta shige dakinta rike da farantin jin takunsa, faisal yayi ma Ummi dake parlor har lokacin sallama ya fita daga gidan, El-ameen ya koma ya kwanta tare da lumshe idonsa. Suhaima ce ta shigo parlor rike da waya tana kallon Hajiyarsu tace "Hajiyarmu yanxu sumayya ta kira ni...." Da sauri ta kalli khadija da ke kwance parlon sai kawai ta juya ta koma daki, Hajiya ta mike ta bi bayanta, khadija ta tabe baki ta ci gaba da danna wayarta. Junaid na kwance parlon Mumy that same day, idonsa lumshe kamar me bacci kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune yana kallon wayarsa ya dauka yayi dialing number bugu uku aka d'aga, bayan sakwanni 20 jin ba ace komai ba daya bangaren yace "Uhn how you?" Jin an ki cewa komai still, yace "sai in kashe wayata ne" kamar xata yi kuka tace "Toh ina ruwana ni nace ka kira" murmushi yayi yace "Ohk, sai anjima" da sauri tace "Noo Ya Ahmad don Allah ka xo ka dauke ni, gida nake son dawowa" yace "Anki, xaman ki a can ya fi maki, sai kiyi ta neman fitina da Jawahir!" Katse wayar yayi ya ajiye yana murmushi, can ya mike ya fita ya koma part dinsa don tun da ya dawo daga gun faisal yake kwance parlon Mumy ko uniform bai cire ba, yana bedroom ya fito daga wanka yana shiryawa yaji an murda kofar parlor, juyawa yayi yana kallon kofar dakin har aka bude, faisal ya shigo da sallama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Glad you came" faisal ya karaso ya zauna gefen gado yace "ka jira har El-ameen ya sauko Captain, yayi sama da yawa, beside ni ban...." Da sauri Junaid yace "Xuwa kayi ka samesa?" Faisal ya d'aga masa gira, Junaid yace "Ohhh shit! Why? Meyasa xaka min haka, why did you go faisal, gaskiya ka bata min rai, who's he da yake tunanin without him Allah baxai bata lafiya ba, shi din banxa, bana bukatansa a lamari na kuma, bana bukata...." Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Haka kawai in sa baki daga karshe in ji kunya, da dai ban san ku bane, duk ku yi ku gama" Junaid yayi tsaki ya ci gaba da shirin sa, yana gamawa ya juya yana kallon faisal yace "Ka sama min psychiatry din ne frnd?" Faisal yace "Psychiatry me kyau sai Abeokuta or Lagos, but I will advice you to take haka to na Abeokutan ya fi, Neuro Psychiatric hospital Aro" Junaid yace "Har Ogun state? No plss samo min a nan north" faisal yace "Toh ai na can yafi komai ne, ga qualified neurologist..." Junaid ya xauna gefen gadon yace "Abeokuta kuma? Or kasan me I shud just look for a private neurologist for her...." Faisal yayi murmushi yace "That's money frnd, hospital ya fi!" Junaid yayi shiru, sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Allah xai rufa asiri, just get me a qualify one" faisal yace "ohkk dats not a problem, duk dai yanda ta yiwu in na gidan in na hospital," Junaid ya gyada kai yace "Toh shikenan" faisal yace "Sai da abu ya kwabe maku sannan xa a wani xo a sameni.... Ni kallonku kawai nake kai da El," Junaid yayi murmushi ya mike yace "Kaga xan kai mata fruits can gidan yanxu, muje part din mumy sai inyi kamar rakaka xan yi" faisal yayi dariya yace "Plss do and get ur freedom captain! You are getting old fa Mumys boy!" Junaid yace "Uhum kaga in tafiya xaka yi ka taso mu tafi!" Mikewa faisal yayi ya bi bayansa yana dariya, suka nufi part din Mumy, faisal yayi mata sallama, Junaid na shafa kai yace "Mumy bari in rakasa!" Mumy tace "Toh sai ka dawo" fita suka yi faisal na dariya, Suhaima dake tsaye bakin tap ta bi su da kallo tana tunanin xancen da Sumayya ta mata a waya, ajiyar xuciya ta sauke tana tunanin ta ina xata fara binciken da Hajiya ta sa ta, wai Mahaukaciya, tab, har Allah Allah take washegari yayi! Suna fita gidan Junaid ya kalli faisal yace "Kaga ban fito da mota ba, da taka xa mu je can gidan daga can sai ka ga Mahaukaciyar," faisal ya buda ido yace "Da take neman hada aminai biyu ba!" Junaid ya tabe baki yace "No bata hada mu ba, frndship din ne ya xo karshe dama" dariya kawai faisal yake, Junaid ya karbi makullin hannunsa ya shiga motar ya tada. A hanya suka siya fruits sannan suka kama hanyar gidan El-ameen, mama na sharan parlon suka shigo, ta mike tana masu sannu da xuwa, Junaid sai kalle kallen inda xai ganta yake, mama jummai ta lura da hakan ta nuna masa gefensu tace "Ga ta can" juyawa yayi ya ganta xaune ta jingina da bango ta d'an dukar da kai alamar bacci take, xai yi magana Mama jummai tace "Babu yanda banyi da ita ta bar wajen nan ba ta ki, kuma ta ki kwanciya, ni dai na rasa gane kan baiwar Allahn nan, ko abinci taki ci, dama Aminu kadai yasan kanta, rashin cin abincin nan ba karamin daga min hankali yake ba, toh ko dai bata da lafiya ne" Junaid ya tabe baki bai ce komai ba, faisal kuwa kallonta kawai yake, duk da ba ganin fuskarta yake ba, Junaid ya kallesa sannan ya karasa kusa da ita ya duka kamar me rada yanda bbu wanda xai ji sa a hankali yace "Jasmine!" D'ago kanta tayi da sauri ta bude ido tana kallonsa, a hankali faisal ya dinga komawa baya yana kallonta ko kiftawa bai yi har ya isa jikin kofa bai sani ba, kalle kalle kawai take sai kuma ta mike tana kallon kofar jin alamar mutum, da sauri ta nufi kofar Junaid ya bi ta da kallo, tana isa bakin kofar ta tsaya tana kallon faisal, still yayi a wajen ko kwakkwaran motsi bai yi, har lokacin idonsa na cikin nata, juyawa tayi a hankali ta dawo kusa da Junaid ta xube gabansa ta xauna, kallo daya xaka mata ka ga ramar da tayi, mama jummai ta fara dariya tace "Wayyo, ca take Aminu ne baiwar Allah, to ko don bata ganinsa yasa taki sakin jiki ne? Kasan fa ko mara hankali dole ya gane me kyautata masa" Junaid ya lumshe ido ya bude ya ajiye mata ledan fruits din hannunsa ya bude, kallon fruits din kawai take, a hankali ya 6alli ayaba guda daya a bunch dinsa ya mika mata, karba tayi tana ta kallon ayabar kamar me son gano abu, can dai ta sa hannu a hankali ta shiga cire peel din yanda ta ga El-ameen na mata, Junaid dai kallonta kawai yake, tana gama cirewa ta mika masa, ya karba ya kai mata baki ta ki ci, duk yanda yayi da ita kin ci tayi ta kwanta nan wajen, Mama jummai tace "Wai yaushe Ahmad din xai dawo ne, ina jin fa yarinyar nan sabon da tayi da shi yasa ta ki sake jiki rashin ganinsa, tausayi take ban wallahi" mikewa Junaid yayi bai ce komai ba, ya nufi kofa, faisal dake wajen har lokacin yana kallonta ya basa hanya ya fice, sannan shi ma ya juya ya bi bayansa, xama Junaid yayi a balcony ya fito da wayarsa yana jujjuyawa, faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Me ka fahimta game da reaction din yarinyar...." Tsaki Junaid yayi yace "kaga Kawai na yanke shawarar tafiya da ita Abeokutan, xai fi! Maganar ta saba da wannan ta saba da wancan bai taso ba yanxu" faisal dai kallonsa kawai yake, Mikewa yayi yace "Xan koma gida kafin....." Faisal ya katse sa yace "Haba Captain kana jin ance tun safe bata ci komai ba sai kace xaka tafi, ko da milk ne ka siyo a gwada bata mana" Junaid yace "Yea! But I don't want my mum to start calling me, bayan bakin gate kadai nace xan raka ka, do me a favour by buying the milk and bringing it to them, ga Atm card dina" kallonsa kawai faisal ke yi, har ya fiddo card din ya mika masa, can ya girgixa kai yace "Nima yanxu Mumyna xata kira ni" Junaid yace "Ohk then! Let me send the gate keeper!" Daga haka ya nufi gun mai gadi, faisal ya girgixa Kai ya koma parlon, ai tana jin an tura kofa ta mike da sauri, faisal ya rungume hannayensa yace "Poor you!" Komawa tayi a hankali ta xauna. Ya juya ya fita daga parlon wani tausayinta na shigarsa, anya ba asiri bane wannan, ban da haka me yayi mata xafi haka har ya kai ta ga hauka at her young age!" Ko da ya fita har Junaid yayi masa gaba da motarsa, tsaki kawai yayi ya nufi titi don hawa tricycle, ko waye bai son uwarsa???Washegari Junaid na office ya kira faisal, bayan sun gaisa yace "Plss frnd make arrangement for me ko xuwa gobe ko jibi sai a tafi da ita can din, ta flight" faisal yace "Who's going der with her?" Junaid yace "Yea xan ce ma Mumy an min transfer din sati daya xuwa lag, kaga kafin sati dayan duk xa ayi abubuwan da ya kamata, bari dai xan xo idan na bar gun aiki sai muyi magana" faisal ya tabe baki yace "Ohk," sannan ya katse wayar. El-ameen ne xaune office ya hade kai da table, ya ji an bude kofar office din, dagowa yayi da sauri don ganin waye, sanin ya gaya ma nurses din ya gama attending ma patients for that day, ganin faisal ne ya kalli agogo yaga uku ya gota, faisal ya karaso yace "What's the problem El?" El-ameen ya shafa kansa tare da lumshe ido yace "Bacci!"Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

GLOBNG HUB - Best for All Globng Hub and SGL is for interested content creators who wants to share their experience to the whole world, you can create account with us, when your account is approve you can then proceed to create contents ranging from entertainment, sports, politics, health and fitness, society news, technology, business and industrial, lifestyle, education, pet and animals etc. The interested thing is you will get paid as far as your contents/articles worth paying. To Register click on the link below https://globng.com/register