Kalli Mutum Rike Da Zuciyarsa Bayan Anyi Masa Dashen Zuciya A Kasar Amurka

Mutumin ɗan shekara 68 mai suna Lee Walden, kuma ɗan jihar Texas a Amurka, an yi masa dashen zuciyar ne a asibitin Baylor University Medical Center a watan Afirilu, bayan shafe shekaru yana dogara da na'urar da ke temaka wa zuciya bugawa.
Mista Lee na samun izna kai tsaye yayin da ya ke riƙe da tsohuwar zuciyarsa a hannunsa. Wannan na faruwa ne watanni uku bayan dashen zuciyar, inda asibitin kan kirawo waɗanda aka yi wa dashen zuciyar domin su riƙe tsohuwar zuciyarsu domin samun izna kan yadda za su kula da sabuwar zuciyar da aka dasa musu.
Idan kana son lafiyar zuciyar ka:
1. Rage cin gishiri a abinci/abin sha.
2. Zaɓi lafiyayyen/ingantaccen abinci
3. Zaɓi zama mai matsakaicin nauyi(ƙiba/teɓa).
4. Ƙaurace wa barasa/giya.
5. Ƙaurace wa sarrafaffen mai da daskararren mai a cimaka.
6. Guji shan taba-sigari.
7. Yi atisaye/motsa jiki a kowacce rana na aƙalla minti talatin.
Tushen hoto: \WebMD

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author