September 21, 2020

Kalli Video Yadda ake kulawa da Yaron da Kishiyoyi Uwa suka daure har shekaru biyu Sai dai yaci kashin da yayi

Jibril yanzu haka yana samun sauki a asibitin sir Yahaya dake birnin Kebbi a jihar Kebbi

 

IYanzu haka dai shugaban asibitin Sir Yahaya dake Birnin Kebbi ya taimaka masa da tufafin sakawa, abinci da magunguna.

Inda wata kungiya mai suna ZakiG suka taimaka masa da omo na wanki kayan abinci da takalmi

Jibril yaro ne mai dadin mu’amala. Kuma Yanzu haka harya saba da ɗan sandan da yake kula dashi

A ganin yanayin da yaron yake na fama da matsananciyar yunwa a tare dashi, kuma yanzu haka yana cikin farin ciki bayanda aka samar masa da abinci

 

Yanzu haka dai Mahaifinsa da sauran kishiyoyin mahaifiyarsa da suka masa wannan mummunan aikin suna hannun hukumar ‘yan sanda a tsare

 

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri