Kano: Za A Koma Biyan Karancin Albashi Na Naira Dubu 18-Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da daina biyan ma'aikata karancin albashin naira dubu N30,000 tare da gaggauta komawa biyan karancin albashin zuwa naira dubu N18,000 kamar yadda aka saba kuma aka gada.
Gwamnan ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan karayar tattalin arzikin da aka shiga saboda Covid-19 Annobar ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.
A yayin tabbatar da wannan sauyin mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, yace halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.
Tanko Yakasai Yace: "Gwamnatin jihar ta koma biyan tsohon karancin albashi saboda halin da ta shiga. Abinda muke samu a matsayin gwamnati yanzu ya ragu kuma ba za mu iya cigaba da biyan N30,000 ba a matsayin karancin albashin."
Amma kuma, ma'aikatan gwamnatin dake jihar sun jajanta yadda gwamnatin jihar bata bada wata sanarwa ba kafin ta fara zabtare musu albashi, sai dai suka wayi gari da ganin giɓi a Albashin nasu.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author