Karanta Abubuwan Ban Mamaki Guda 10 Game Da Zuciya.

1] Zuciya na fara bugawa tun kwanaki 21—23 da halittar ɗan tayi a mahaifa.
2] Girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum.
3] Zuciya na bugawa sau 60 — 100 a minti ɗaya yayin hutu, wato yayin da ba a wani aiki.
4] Zuciya na bugawa kimanin sau dubu ɗari (100, 000) a kowacce rana.
5] Zuciya tana harba jinin da ya kai yawan galan dubu biyu (2,000) a kowacce rana.
6] Zuciya na iya ci gaba da bugawa bayan an cire ta daga jikin mutum.
7] Zuciya na da tsarin lantarki na kanta domin buga jini zuwa sassan jiki. Saboda haka, zuciya ke aiki ba tare da karɓar umarni daga mutum ba. Wannan ya sa zuciya ke ci gaba da aiki har lokacin da ake bacci.
8] Jarirai na da bugun zuciya mafi sauri da ya kai bugu 70 — 190 a minti ɗaya.
9] Zuciya na harba jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 miles), in da za a ware tsayinsu.
10] A Afirka aka fara dashen zuciya na farko a duniya. An fara dashen zuciya na farko a duniya, daga mutum zuwa mutum, a ranar 3 ga watan Disamba 1967, wato kusan shekara 53 kenan, wanda likitan tiyatar zuciya ɗan Afirka ta Kudu, Dr. Christiaan Barnard ya gudanar a Asibitin Groote Schuur a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author