Karanta Dalilan Da Yasa Muka Rasa Kwanciyar Hankali-Dr Ahmad Buk

Babban malamin addinin Islama a jihar kano dake Najeriya, Sheikh Dr Ahmad Ibrahim Buk yace akwai dalilai masu tarin yawa wadanda muka rasa kwanciyar hankali, amma ga kadan daga cikin su.
 
"Dalilin da ya sa muke shan wahala a rayuwa shine mun dauka kudi shine maganin kowacce matsala a rayuwa. Shi ya sa idan muka rasa su sai mu shiga matsala. Mun dauke su da matukar muhimmanci da idan muka ga mai kudi sai mu yi kamar mu bauta masa.
Abinda ba mu sani ba shine shi kudi ba shine maganin kowacce matsala ba, wani bangare ne na jin dadin rayuwa. Arziki ne kuma ba shi kadai ne arziki ba. Ba wai iyu ka ga Allah Ya hadawa mutum komai na rayuwa a duniya ba. Idan ya ba shi kudi kai ma akwai wani arziki da Allah Ya ba ka.
Shin Lafiya ba arziki ba ne? Ilimi ba arziki ba ne? Kyau ba arziki ba ne? Maikudi zai iya rasa lafiya kai Allah Ya ba ka. Maikudi zai iya samun 'ya'ya su kangare masa Allah Ya Shirya maka naka. Duk abinda Allah Ya ba ka da za ka iya amfani da shi arziki ne. Sana'ar ka idan ka yarda da Allah ka yarda da ita sai Allah Ya daukaka ka a cikin ta.
Don haka ka nemi dukiyar Halak sai Allah Ya sa mata albarka fiye da dukiyar Haram. Ba yadda za a yi ka tara dukiyar Haram ka ce daidai take da dukiyar halak. Karamin ma'aikaci da ya ke cin halak sai ka ga ya yi hidimar gidansa hankali kwance, a aurar da wance a yi wancan. Idan yaro ba lafiya a jika wancan a ba shi ya warke. Idan ya sayo karamar atamfa ya Kawowa matarsa ta yi godiya ta sa albarka. Idan ta je shagon sayayya idonta kan kaya masu araha zai je a zo a sarrafa komai ya tafi daidai hankalinsu a kwance. Saboda Allah Ya sa albarka a dukiyar.
Amma wanda ya tara dukiyar Haram idan yaro ba lafiya sai an je private an je waje an kashe kudi. Idan ya zagaye garin nan ya sayo atamfar da ta fi kowacce sai shaidan ya kawar da idonta ta raina ta. Idan ma taje gidan biki sai ta ga wacce ba ta kai tata ba amma taji kamar tafi tata. Idan ta je shagon sayayya idonta ba zai tsaya kan kananan abubuwa ba sai masu tsada. Haka zai yi ta kashe kudaden saboda Allah Ya cire musu albarka.
Sarki ne, Shugaban Kasa ne, Gwamna ne, 'Yan Siyasa ne haka za suyi ta satar dukiyar Al'umma kuma Allah Ya hana su zaman lafiya a rayuwa. Sun saci kudaden kuma sun zagaye ko ina a duniya suna neman kwanciyar hankali amma sun rasa. Saboda Allah ba ya barin zalinci. Ba su san ma yadda zasu samu kwanciyar hankalin ba. Kuma kullum satar suke suna tara dukiyar.
Allah Yace abu Haramun ne kuma ka bi wannan hanya ka tara kudi ka ce daidai kake da wanda ya tara dukiyar Halak? Ba daidai suke ba.
Daga karshe shehin malamin yayi addu'a da Allah Ya Gafarta mana, yasa mudace.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author