Karanta Dalilin Da yasa Bankunan Nijeriya suka dakatar da sayar da katin MTN

Rikici tsakanin bankunan Nijeriya da kamfanin sadarwa na MTN ya bar miliyoyin masu amfani da layin cikin zulumi bayan da suka kasa samun damar sayen katin waya a wayoyinsu ta hanyar amfani da USSD  tun daga ranar Juma’ar nan 2/4/2021

Hakan ya faru ne bayan bankunan kasar sun rufe wa kamfanin sadarwar tsarin na USSD a kan kudaden da aka caje su da shi.

Sai dai kamfanin na MTN ya shawarci masu amfani da layinsu da su nemi wasu hanyoyin da za su sanya wa layukan wayoyin nasu kudin ba tare da sanar masu takamaiman matsalar da take faruwa ba.

Majiyar DCL Hausa ta ga sanarwar da kamfanin na MTN ke aike wa kwastomominsu kamar haka; “ya kai abokin huldarmu, an toshe hanyoyin USSD daga bankuna a halin yanzu. Don haka kun sake neman wata hanya mafi sauki da za ku iya sayen kati ko ku sayi kati na zahiri domin yin amfani da shi. Muna neman afuwa game da wannan matsala. Mun gode, ”.

 

Source: DCL Hausa 

 

Kada ku manta ku shiga shafin mu na facebook kuyi like domin samun labarai na ku wace rana 

www.facebook.com/globnghub

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author

GLOBNG HUB - Best for All Globng Hub and SGL is for interested content creators who wants to share their experience to the whole world, you can create account with us, when your account is approve you can then proceed to create contents ranging from entertainment, sports, politics, health and fitness, society news, technology, business and industrial, lifestyle, education, pet and animals etc. The interested thing is you will get paid as far as your contents/articles worth paying. To Register click on the link below https://globng.com/register