Karanta Hanyoyi Shida Da Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Lissafa Don Kiyaye Hawan Jini

1. Rage cin gishiri zuwa ƙasa da giram biyar (5 gram) a kullum. Wato giram biyar shi ne zai yi dai-dai da cikin mitsitsin cokalin shayi, amma ba babban cokalin da ake cin abinci da shi ba.
 

2. Cin 'ya'yan itatuwa / kayan marmari da ganyayyaki akai-akai. Amma ba jifa-jifa kawai ba.

3. Ƙaurace wa ko rage cimakar da ke maƙare da daskararren mai (saturated fat) kamar kitse / kakide, madarar shanu, man shanu, cuku/cukwi, man kwakwar manja, manja da sauransu. Bugu da ƙari, a guji cin sarrafaffen kitse (artificial trans fat). Sarrafaffen kitse shi ne kitsen da ake sarrafawa a masana'antu bayan an cakuɗa haidirojin (hydrogen) a cikin tsinkakken mai domin ya daskare ko kuma ya yi kauri. Abubuwan da suke ɗauke da irin wannan sarrafaffen kitse sun haɗa da: 'margarines' wato bota, 'doughnuts', 'cakes', 'pie crusts', 'biscuits', 'frozen pizza', 'cookies', 'crackers' da sauransu.
 

4. Ƙaurace wa shan taba sigari.

5. Ƙaurace wa shan giya/barasa.

6. Kasancewa cikin motsa jiki ko atisaye a kullum, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawara na aƙalla mintina 30 a kullum.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author