Karya Tarihin Pele Ni Ban Damu Ba-Messi

Dan wasan Barcelona, Leonel Messi yace  bai damu da karya tarihin tsohon dan wasan Barzil ba wato  Pele, duk da yawan maganganu da hakan ya kawo a baya.

A baya ne aka ce dan wasa Leonel Messi ya karya tarihin da tsohon dan wasan Pele ya kafa, wanda zura kwallaye masu tarin yawa a kungiya daya rigis, matakin daya kawo maganganu iri-iri akan a adadin kwallayen da dan wasan ya zura a raga.

Sai dai ana cikin maganganun ne kawai sai  kungiyar kwallon kafa ta Santos dake kasar Brazil, domin itace  kungiyar da shahararren dan wasa Pele ya bugawa wasa a lokacin da yake matashi ta karyata zancen da akeyi na cewa dan wasa Messi ya karya tarihin Pele gurin cin kwallaye a kungiya daya tilo.

Leonel Messi, yayi daidai da tarihin tsohon dan wasan Brazil Pele, daya kafa na zura kwallaye 643 a kungiya guda daya, bayan da yaci wa kungiyarsa ta Barcelona kwallo a wasan da su kayi da Balencia sannan ya sake cin kwallo daya wadda tasa ya zarta Pele din a wasan da suka fafata da Balladolid a satin daya gabata.

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author