KASA TA RIKICE SAI YADDA HALI YAYI

KASA TA RIKICE SAI ABIN DA HALI YAYI!!!

 

Aminu S Miko

 

A ranar 02/10/2019 Chief Bisi Akande ya bayyana cewa: Najeriya ta yi bikin shekara 59 da 'yanci, za kuma tayi na 60. Amma ba lalle tayi na 70 ba.

 

Kwanaki kadan bayan nan Gen. TY Danjuma ya bayyana cewa: da zai bayyana abin da yake faruwa a kasar nan, to ba wanda zai kuma barci da ido biyu. 

 

Abin da arewawa basu sani ba, Yarabawa da Inyamurai suna da zaunannen tsari da suke son Najeriya ta tafi a kansa sama da shekara 106 tun Amalgamation (hade yankunan kasa) kuma har yanzu wannan bukatu na su ba su biya ba. Kuma ba za su taba hakura ba, za su bi duk wasu hanyoyin da  za su kai su ga nasara.

 

A 'yan kwanakin baya, kiraye-kirayen sake fasalta kasa ya kuma tasowa haikan, daga bakin jagororin al'umomin kudu, manya daga ciki, sune

 

PA Fasoranti

Oni of Ife Ogunwusi

Edwin Clark

Pastor Ayo Adebanjo

 

Ba na goyon bayan sauya fasalin kasa, balle kuma rabata. Saboda mu ba jagoranci mai kyau da kishin al'umma a yankin arewa, za su yi amfani da wannan damar su kara damalmala yankin da rikicin addini da kabilanci da siyasa.

 

Komai na iya faruwa a kasar nan, nan da wani dan lokaci, zaben ma na 2023 ba lalle ya yiwu ba. 

 

Allah dai ya kyauta.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State