Kebbi: Farmakin Yan bindiga a Sakaba, DPO, Safeto 1, Mopol 7 da yan sa kai 2 ne suka mutu

Bayanai na nuna cewa adadin jami'an tsaro da suka rigamu gidan gaskiya (mutu) a harin da Yan daban daji suka kai a yankin Makuku da ke a karamar hukumar ta Sakaba da wacce ta ke a Kar kashin mulkin Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi ya tabbatar da DPO na ofishin yan sandan Sakaba da Safeton yasanda guda daya da yan sandan kwantar da tarzoma guda 7 da kuma Yan sa Kai biyu ne aka nuna  mutuwarsu.

 
A baya dai bayanan farko a daren ranar Lahadi sun nuna karancin adadin mamata sabanin sabon bayanai da suka fito yau ranar Litinin 26 ga watan Aprilun 2021, kamar yadda jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya bayyana.
IMG-20210426-WA0023.jpg
 
Jami'an tsaron sun rasa rayukansu ne a lokacin da suke kokarin kare dukiya da rayukan al'umma ta hanyar gaba-da-gaba da Yan daban dajin da suka tafka babbar ta'asa bayan sun sace shanun jama'a kimanin 1000.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author