KOTUN JIHAR KADUNA TA YANKEWA WASU MATA 'YAN UWAN JUNA HUKUNCIN SHEKARA GOMA A GIDAN KASO

 
Mai Shari'a Muhammad Tukur na babbar kotun jihar Kaduna a ranar 24 ga watan Nuwamba, ya yanke hukunci ga Maryam Muhammad Jallo da Rukaiya Muhammad Jallo hukuncin daurin shekaru goma a kan laifukan da suka shafi cin amana, an gurfanar da matan ne a gaban kotun kan zargin cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC.
 
Mai karanta ƙarar ya ce, “ya mai shari'a Maryam Jallo da Rukaiya Jallo a ranar 30 ga Maris, 2019 a Kaduna an damka maku zunzurutun kudi Naira Miliyan daya da Dubu Dari Bakwai (N1,700,000) ta wani Alhaji Badamasi Shanono da Adio Bukar Hashia don neman magani ga wani Usman Umar wanda daga karshe suka karkatar da kuɗin ,sannan kuma sun aikata laifi wanda ya sabawa sashi na 293 na dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Kaduna, ta shekarar 2017 kuma za a hukunta su a karkashin sashe na 294 na wannan Doka.
 
Wadanda ake tuhumar sun amsa ‘laifi’ kan tuhumar da aka yi masu, Sakamakon haka, Mai Shari'a Tukur ya yanke musu hukuncin shekaru goma a kurkuku tare da zabin tarar N 100,000 (Naira Dubu Dari).

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author