Ku Kula Da 'Ya'Yanku Baza Mu Iya Samar Da Tsaro Ba A Makarantu-Gwamnati

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta jaddada aniyarta ga yan Kasar da su shiga taitayin su kana suyi taka tsantsan don kawo karshen matsalolin tsaro a makarantu da sace dalibai da ake yi.

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne wanda ya sanar da hakan a wata hira da gidan jaridar (The PUNCH) a ranar Litinin 15 ga watan Maris, 2021, ne ya tabbatar da cewa gwamnati ba zata iya kawo tsaro a kowacce makarantar dake fadin kasar ba.

Mr Chukwuemeka yace, gwamnati ta bada umarnin cewa makarantu da su dinga kai bayanai ga duk wata barazanar tsaro da ta kunno kai ga hukumar tsaro mafi kusa da su.


Ya kara da cewa, Gwamnati ba zata iya tsare kowanne gida ba a fadin kasar, saboda haka kowa na iya taka tsan-tsan akan lamarin muna isar da wannan sakon ne ga makarantin mu na ko'ina dake fadin Najeriya da zarar sunga wata barazanar tsaro to su hanzarta wajen hukumomin tsaro mafi kusa da su.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author