Kungiyar Kauran Gwandu A Jihar Kebbi (KAGAF) Tayi Ka6akin Arziki Ga Matasa 320

Hadaddiyar kungiyar Kauran Gwandu da ke jihar kebbi wato ( Kauran Gwandu Advocacy Forum), tayi bikin kaddamar da  rabawa daruruwan Matasa Fom din jarrabawar JAMB kyauta, Inda ta samar wa fiye da Matasa dari 320 fom kyauta.

A ranar Laraba ne 21 ga watan Aprilun 2021, Shugaban kungiyar a jihar Kebbi Mansur Sarki Gwandu shi ne ya bayyana hakan yayin taron.

20210421_184922.jpg
Hon Mansur Sarki Gwandu ya ce "Ita dai wannan kungiya na Kauran Gwandu Advocacy Forum KAGAF, muna da jajirtattun  wakilai a kaf kananan hukumomi 21 da ke jihar ta Kebbi, kuma  masu burin cigaban Matasa da kuma samar da ilimi kyauta a jihar, wannan shi ne babban dalilin da ya hada mu da su a KAGAF.
 
Adon haka ne ma muka zakulo marasa karfi, domin tallafa masu da wannan Fom.
20210421_182512.jpg
Sai dai tun da farko mun shirya bayar da wannan Fom ne ga 260 wanda yanzu suka zama mutum 320 duk wanda ya sami damar amfana da wannan Fom na kungiya da ta samar a cika shi kyauta.
 
Inda Hon Samaila Mabo, ya bayar da kyautar FOM 50 ne, Sai kuma Alh Zayyanu ya kara bayar da kyautar FOM 10 Wanda aka jimillar adadin na farko 260  Zuwa 320.
20210421_184759.jpg
Taron ya gudana ne a babban dakin taro na 'Royal Event Arena' da ke shiyar Gwadangaji a jihar Kebbi.
 
Inda ya samu halartar manya-manyan mutane da gogaggun yan siyasa a fadin jihar ta Kebbi.
 
Kadan daga cikin manyan bakin da suka sami damar halarta taron sun hada da:
Hon. Umar Altine Suru
Alh. Kabiru Giant
Alh. Zayyanu Sanka
Alh. Sagir Muhammad
da kuma  Alh. Bello O.G.
20210421_183849.jpg
Inda suma kadan daga cikin Matasan da suka amfana da wannan kyautar Fom din sun hada da:
Bello Abdulkadir, 
Mudassir Isah Fakara daga karamar hukumar Fakai. Sai
Khadijat Musa da
Tukur Sani Kwasara da
Bello Abdulkadir
da kuma Faruku Aliyu.
 
Daga karshe shi ma anasa bayanin shugaban kungiyar (KAGAF) ya tabbatar da samuwar irin wadannan Foma-fomai  anan gaba.
 
Domin samun wasu cikakkun bayanai sai Ku ziyarci shafin mu na WhatsApp
https://chat.whatsapp.com/FkwQ5aI1kcFGBg7zPKVR5A

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author