Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yiwa matasa tanadi na musamman a wannan sabuwar shekarar da muke ciki.
Ya bayyana haka ne a jawabin da yayi na sabuwar shekara da safiyar yau inda ya bayyana cewa ya ji koken matasa dama duk wani ɗan ƙasa nagari.
"Dole ne a samawar Matasa ingantacciyar rayuwa saboda cigaban Najeriya a gobe, Gwamnatina nayi tanadi na musamman da zan yiwa matasa dan inganta rayuwarsu". Inji Shugaba Buhari
You must be logged in to post a comment.