Labarin Wata Baiwar Allah Wadda Ya Kamata Iyaye Su Karanta Don Gudun Kada Ya"Yansu Su Afka Cikin Wannan Halin Nasiha {1081}

Yana Daga Cikin Jahilci Da Duhun kai Na Wasu Daga Cikin Mutanen Qauye Shine Rashin Sanin Illar Dake Tare Da Bayyanar Da Tsarecinsu a Fili Tsirara Duniya Ta Gani Kamar Yadda Ya Faru Da Wata Baiwar Allah Lahaula Wala Quwwata Illa Billah, Domin Akwai Matan Da Haka Ta Faru Dasu Akayi Musu Nasiha Dan Gane Da Abin Daya Shafi Illar Bayyanar Da Tsareci Bisa Basu Fatawar Cewa Haramunne Bai Hallata Ba Ya Dace Idan Zasu Shayar Da Jaririnsu Su Kebance Ba Tare Da Wani Yaga Mamansu a Lokacin Da Suke Shayar Dasu Ba
.
Amma Wallahi Abin Da Zai Baku Mamaki Shine Mun Basu Fatawa Cewa Haramunne Mace Ta Riqa Bawa Jaririnta Nono a Fili Duniya Tana Gani Musamman a Cikin Kasuwa Akan Haka Muka Yi musu Nasiha Amma Budar Bakinta Sai Tace (AU DAMA BABU KYAU ITA WALLAHI BATA SANI BA) ? Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un
.
Jin Wannan Magana Daga Bakinta Hakan Ya Matuqar Dagamin Hankali Sosai Wadda Nayi Mamaki Iyakar Mamaki Daga Bisani Kuma Nayi Nazari Sai Na Fahimci Cewa Babu Abin Dake Tare Da Wannan Mata Face Jahilci Da Kuma Duhun Kai Kuma Fa Ta Manyanta Amma Duk Da Girman Datai Hakan Bai Bata Damar Nemawa Kanta Ilimin Addini Wadda Zai Zama Hujja Gareta Domin Tsare Mutuncinta Ba
.
Wannan Yasa Naga Ya Dace Na Yima Yan"Uwa Mata Nasihar Cewa Yaka Mata Su Kiyaye Mutuncinsu Kuma Bai Halatta Matar Aure Ta Riqa Fito Da Mamanta a Gaban Mutane Tana Shayar Da Jaririnta Ba Domin Tana Iya Shiga Cikin (KASIYATUN ARIYA TUN, MA'ILATUN MUMILATUN RU'USA HUNNA KA'AS NIMATIL BUKUT LA YAJ NA RIHAL JANNA WALA YAD KULUNAL JANNA FA INNA RIHAHA LAYU JADU MIN MASIRATI KAZA WA KAZA) Bukhariy Da Muslim
.
Wato Matan Da Basa Suturce Jikinsu Jikinsu Sune Sun Saka Sutura Amma Ana Ganin Yanayin Jikinsu Ta Ciki Kodai Su Kasance Masu Bayyanar Da Wani Sashi Na Tsarecinsu Manzon Allah s.a.w Ya Fada a Hadisin Bukhariy Da Muslim Cewa Masu Wannan Sifar Yan"Wuta Ne Baza Suji Koda Qanshin Aljanna Ba Balle Su Shigeta Matuqar Basu Kiyaye Tsarecin Su Ba Hadisi Ne Sahihi
.
Dan Haka Ya Zama Wajibi Mata Su Kiyaye Tsarecinsu Tahanyar Tashi Su Nemi Ilimi Domin Jahilci Bai Taba Zama Ilimi Gaba Ga Allah a Yinin Qiyama Ba Domin Hadisi Ya Inganta Daga Annabi Muhammad s.a.w Yana Cikin Littafin Kamsuna Hadith Hadisi Na (10) Annabi Yace (Wailun Liman La Ya'alamu) Riwayar Abu Na'imiy
Annabi Yace: Azaba Ta Tabbata Ga Wadda Bai Sani Ba, Wannan Hadisi Ya Isa Ya Tabbatar Mana Da Cewa Ba'a Kafawa Allah Hujja Akan Rashin Sanin Domin Zama Babu Neman Ilimi Kadai Ya Isa Mutum Azaba
.
Jama'a Mun Fahimta......?

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author