Lahanin Dake Faruwa Ga ƙwaƙwalwar Mutum Bayan Yasa Wa ƙwallon ƙafa Kai

Hukumomin ƙwallon ƙafa a ƙasashen turai sun ce daga yanzu yara 'yan shekara 11 zuwa ƙasa ba za a riƙa koya musu buga ƙwallo da kai ba yayin ɗaukan horo.
Ƙasashen turai da suka haɗa da Ingila, Sukotlan, da kuma Arewacin Ailan sun ɗauki matakin hana yara buga ƙwallo da kai ne biyo bayan wani bincike da aka gudanar a Jami'ar Glasgow da ke Ingila, wanda aka wallafa sakamakon binciken a watan Oktoban 2019, inda binciken ya yi nuni da cewa tsoffin 'yan ƙwallon ƙafa na da ninki uku da rabi na haɗarin mutuwa daga cutukan ƙwaƙwalwa kamar larurar gigi, wato 'dementia' a turance.
Bugu da ƙari, binciken ya sake yin nuni da cewa tsoffin 'yan ƙwallon ƙafa sun fi mutuwa daga cutukan da ke kawo wa aikin ƙwaƙwalwa koma-baya, kuma suna da ƙarin ninki biyar na haɗarin mutuwa daga cutar Parkinson.
[Cutar Parkinson matsalar motsi ce sakamakon raguwar ko ƙarewar sinadarin 'dorpamine' a ƙwaƙwalwa, kuma cutar ta fi shafar tsofi. Haka nan, ana gane alamunta na zahiri da bayyanar kyarma ko karkarwa a hannu ko yatsu da sauran sassan jiki, riƙewar gaɓɓai, nawa ko jinkirin motsi a ayyukan yau da kullum.]
Nauyin ƙwallon ƙafa dai ya kusa kai rabin kilogiram (0.5Kg) kuma masana sun ce ƙwallon za ta iya bugar kan ɗan wasa cikin sauri ko gudun da ya kai kilomita 128 cikin awa ɗaya (128km/h). A yayin da ƙwallo ta bugi kai cikin sauri zai haifar da zijjigawar ƙwaƙwalwa a cikin ƙoƙon kai wanda hakan ke haifar da kurjewa ga ƙwaƙwalwa.
Wani bincike da aka gudanar a Jami'ar British Columbia da ke Ingila a shekara ta 2018, ya nuna ƙaruwar sinadarin furotin a cikin jini wanda ke ƙaruwa bayan rauni ko lahani ga ƙwaƙwalwa.
Jawabin haɗin gwiwa da hukumomin ƙwallon ƙafan suka fitar ya ce an bai wa kociyoyi shawarar kada su riƙa koya wa yara sa wa ƙwallo kai lokacin ɗaukan horo. Yaran da aka hana su sa wa ƙwallo kai sun haɗa da 'yan firamare da 'yan shekara 11 zuwa ƙasa.
Amma hukumomin sun ce, yaran za su iya ci gaba da sa wa ƙwallo kai lokacin wasanin karawa, saboda ƙarancin faruwar hakan yayin wasannin karawar.
Har wa yau, sabuwar dokar ta ce za a fara koyar da yara 'yan shekara 12 sa wa ƙwallo kai ne kaɗan da kaɗan. Misali, yara 'yan ƙasa da shekara 12 za su riƙa sa wa ƙwallo kai sau biyar kacal a wata guda, a yayin da 'yan ƙasa da 13 kuma za su riƙa sa wa ƙwallo kai sau biyar a sati kawai.
Duk da haka, dokar ta ƙara da cewa kada a cika ƙwallon da iska sosai yayin ɗaukan horo, kuma ta kasance mai matsakaicin girma.
Gudanar da wannan bincike ya samu ƙaimi ne daga mutuwar ɗan wasa Jeff Astle a shekara ta 2002, wanda ɗan wasan ƙasar Ingila ne, kuma ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafan West Bromwich Albion, wanda binciken likitoci kan mutuwarsa ya tabbatar da cewa ɗan wasan ya mutu ne sakamakon bugun ƙwaƙwalwa da ya riƙa samu akai-akai tsawon lokaci yayin sa wa ƙwallo kai a wasanni.
Ana sa ran sabuwar dokar za ta taimaka wa yara kauce wa haɗarin samun bugun ƙwaƙwalwa akai-akai yayin sa wa ƙwallo kai wanda binciken ya alaƙanta da cutukan ƙwaƙwalwa daban-daban.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author