MAFARIN FITINAR

KO DA DA MUNAFUNCIN, SAURARI WANNAN

 

Da yawan mutane a social media suke ganin me yake faruwa a wannan zanga zangar, yayin da wasu kuma labari ake basu, shi ma kuma wanda ya bayar da labarin a social media ya gani. Dan haka ba lallai mutum ya san haƙiƙanin gaskiyar al'amrin dake gudana ba.

 

Shi kuma ganin abu a social media kai tsaye ba zai baka gundarin zahirin abin da ya faru ba, domin ta iya yiwuwa wanda ya fara ɗorawa shi kansa bai san me ya faru ba, dan haka zai bayyana kawai abin da ya fahimta ne.

 

A gefe guda kuma duk wanda ya san Gwabnati da kuma yadda ɓata garin masu madafun iko cikin Gwabnatin, ka na da gurɓatattun ƴan siyasa da suke neman biyan buƙatarsu cikin hargitsi irin wannan, ba zai yi wani mamaki ba idan ya san cewa akwai hannun irin waƴannan mutanen cikin wannan rikicin da muke ganin yana faruwa a wasu garuruwan.

 

Da farko zanga-zangar nan an faro ta cikin lumana da salama kamar yadda muka shaida mu dai da muke nan Abuja. Bari dai kawai za su rufe manyan hanyoyin wucewar mutane, amma dai amfani da makamai ban taɓa gani ba. Kuma aƙalla na riski irin wannan zaman nasu kusan sau 4, wanda a na uku ne kawai aka tare min hanya a Kubwa, wanda sai da na shafe awanni 4, kafin daga bisani su barni na wuce bayan motata ta matso jikin su.

 

Wallahi duk cikin kwanakin da suka fara babu wanda suka taɓa ko suka yiwa asara. An fara samun taƙaddama ne a Kubwa, ranar da ta ritsa dani. Amma sai bayan na wuce tukunna abin ya faru.

 

Wato akwai tawagogi da dama na ƴan daba, wanda mafi yawan su ƴan bola-bola ne da suke zaune a unguwannin Dutsen Alhaji da Dawaki da kuma Deidei. Waƴannan matasan, su ne suka zo suka hau su da sara da suka haka nan kawai, wanda nan da nan kowa yayi takansa. Daga baya sai suke ikirarin an taɓa wani mai babur ɗin Adaidaita Sahu, har ma kuma an fasa masa gilashi, shi ne fa wai suka fito ɗaukar fansa.

 

Daga baya naga Videon da ɗaya daga cikin waƴannan ƴan daban yake bayyana cewa Ogansu aka baiwa kwangila, shi kuma ya ɗauke su haya ta hanyar basu Naira 1,500. Kuma a cikin su an kashe mutum Ɗaya.

 

Wannan shi ne zahirin abin da ya fara faruwa na rigima kenan a Abuja, tun bayan fara zanga-zangar da kwanaki 5.

 

Daga nan ne kuma sai aka sake far musu a Apo Garage, inda har hakan yayi sanadiyar ƙona motoci sama da 200, da kuma salwantar rayuka 2. A kuma wannan harin ne aka gano wata Labdcruiser Jeep tazo ta ɗauki wasu daga cikin waƴannan ƴan daban akan titin Adetokunbo Ademola dake wuse. Sannan kuma aka sake ganin wata motar ƴan sanda tana sauke irin waƴannan ƴan dabar, kuma ƴan sanda ne a cikin motar.

 

Jiya an samu hatsaniyar da ta janyo asarar rayukan mutane 9 a Dutsen Alhaji, sakamakon irin waƴannan ƴan daban. Inda wani Kirista aka ce ya kashe wani wanzami. Shi kenan sai rigimar ƙabilanci ta rincaɓe, rigimar da bata mutu ba har tsakar dare. Domin ƴan sanda sun sanya curfew a unguwar, amma tsakar dare bayan an tabbatar sun tafi waƴannan ƴan iskan suka taso suna bi gida-gida suna dukan arnan unguwar. Kuma har busa ƙaho suke cikin daren. Da yawan arnan a gidajen Musulman da suke maƙwabtaka dasu suka kwana.

 

Jahar Lagos ma hakan ne ya fara faruwa, domin sun ɗau kwanaki suna zanga zangar su, kafin daga bisani a tura musu ƴan daba, kuma mafi yawan su Hausawa. Da yawan mu munga Videon a wannan dandalin. Daga nan ne kuma rigin-gimu suka fara faruwa a jahar Lagos ɗin, domin ɓata gari sun ƙwace zanga-zangar.

 

Dan haka ni a gurina, ko ma me ya faru akwai sa hannun masu neman biyan buƙatarsu a cikin wannan hatsaniyar, kuma su ne suke sa ana wannan ta'addancin don su ƙara hargitsa Ƙasar.

 

Ba kuma na goyon bayan buɗewa masu zanga-zangar wuta da bakin bindiga a Lekkin jahar Lagos. Domin ina da yaƙinin ba su suke da alhakin ɓarnar da aka tafka ba, akwai waƴanda suka jingina dasu domin lalata tsarin nasu domin tabbatuwar nasu tsarin.

 

Ba wai goyon bayan su nake ba, bari dai kawai a ko da yaushe ina kallon kowani al'amari ne idona buɗe, ba wai a rufe ba. Dan haka ba zan taɓa goyon bayan zalunci ba ko da shi zai fi daɗaɗa min rai.

 

Fatan mu dai Allah ya bamu zama lafiya da kwanciyar hankali.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State