Mahara Sun Sace Mutum 60 Sun Kona Garin Ruwan Tofa A Jihar Zamfara

Jama'ar yankin Ruwan Tofa na karamar hukumar Maru a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya, sun gamu da tsaka mai wuya a wajen 'yan bindiga, inda rahotanni sun bayyana cewa an kona rabin garin da dukiya mai tarin yawa, sannan suka tafi da mutane a kalla fiye da sittin.

Hakan ya faru ne a lokacin da matsalar satar daliban 'yan makarantar jeka-ka-dawo a yankin Runka dake jihar Katsina.

Halin da ake ciki yanzu haka al'ummar garin sun ranta ana kare (Gudu) inda wanda majiyarmu ta saka ye sunansa yace, matsalar tayi mana nauyi da yawa domin ko shekaranjiya da kuma jiya sun kawo mana hari, sannan sun kona mana gari da motoci da shaguna ga kuma gidaje masu tarin yawa.

Kusan rabin gari sun kone shi kurmus, inji wani mazaunin garin, sannan ya cigaba da fadin cewa ba a samu asarar rai ba ko daya amma kuma maharan sun harbi wani wanda yanzu haka yana kwance a gadon asibiti.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author