Ana Zargi Sarkin kano Aminu Ado Bayero da badakalar kudi Naira bilyan 1.3 na filaye
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin sarkin Kano Aminu Ado Bayero da handame makudan kudaden filaye 22 wanda yawan kudin su ya kai kimanin Naira Biliyan 1.295, shekara daya bayan hawansa karagar mulki.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano tana tuhumar sarkin tare da manyan makarrabansa bisa karkatar da kudaden zuwa aljihunsu.
Shugaban hukumar Muhuyi Magaji ne ya tabbatar da hakan ga majiyar DCL Hausa yana mai jaddada cewa hukumar ba zata kyale duk wanda ya fada komarta ba.
Filayen da ake takaddamar akansu za su cigaba da zama a hannun hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan badakalar wadda ta fara tun lokacin tsohon sarki Sanusi.
Source: DCL Hausa
Ka da ku manta kuyi mana sharing zuwa ga shafukanku na Facebook da Twitter da WhatsApp kuma ku yi liking shafin mu na facebook www.facebook.com/globnghub ku yi following shafin mu na twitter https://twitter.com/globng
You must be logged in to post a comment.