Matakai Uku Bayan Karaya Kafin Garzayawa Asibiti

1 A tsayar da zubar jini idan buɗaɗɗiyar karaya aka samu ta hanyar dannewa ko naɗewa da mayani ko ƙyalle mai tsabta. Kada a yi ƙoƙarin daidaita ƙashin da ya karye. Domin hakan na iya raunata jijiyoyin jini ko jijiyoyin laka da ke wurin.
2 A tallafi karayar ta hanyar amfani da kara ko itace a gefe da gefe sannan a ɗaure domin hana karayar motsi.
3 A sanya ƙanƙara a wurin karayar domin rage kumburi da raɗaɗin ciwo.
Da zarar an kammala ɗaukar waɗannan matakai to lokacin garzayawa asibiti🚑 ya yi.
 
 


Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author