September 19, 2020

Matakan Samun Damar Karbar Bashin Babban Bankin Nijeriya Na Manoma Da Masu Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i

Matakan Samun Damar Karbar Bashin Babban Bankin Nijeriya Na Manoma Da Masu Kanana Da Matsakaitan Sana’o’in Ba Tare Da Jingina Ba

Don Allah ku tabbatar kun aika zuwa ga Jama’arku domin su amfana

Babban Bankin Najeriya (CBN) tare da Hadakar Kwamiti na Bankuna, sun fito da wani tsari domin Manoma da Masu kanana da matsakaitan Sana’o’i da za a iya bawa tallafin kudi a matsarin bashi domin habbaka kasuwancinsu tare da habbaka tattalin arzikin kasa da kuma rage zaman banza a cikin al’uma. Wannan shirin ana kiransa (Agri-Business/Small and Medium Enterprise Investment Scheme) AGSMEIS Loan, shirin dai shiri ne da aka fito dashi domin karfafawa gwamnatin tarayya da habbaka harkar kasuwancin Noma da Sanana da Matsakaitan Sana’o’i (SMEs) a cikin kasa ta hanyar sake kudin ga kananun bankuna kamar NIRSAL Microfinance Bank da wasunsu.
Duk wani dan Najeriya mai ra’ayin shiga harkar noma ko kasuwanci zai iya cin muriyar wannan shirin, inda zai iya neman kudi da suka kai kimanin N10m (million) ta wannan shirin na AGSMEIS, tare da ribar kashe biyar (5%) a duk shekara.
A kasan wannan bayanin tsarin yadda za a iya samun damar cin gajiyar wannan shirin ne kamar haka:
SUWAYE SUKA CAN-CANTA SU KARBI BASHIN AGSMEIS ?
Masu kasuwanci daban-daban na daga cikin jerin wadanda zasu iya neman wannan tallafin bashin domin inganta sana’arsu, ga misalai kamar haka:
• Manoma
• Makiyaya
• Kwalliya, dinki, Cosmetics, Catering
• Mining, da kuma petrochemicals
• Services sector kamar su Information and Communication technology (ICT)
• Creative Industry da dai sauran sana’o’i da babban bankin tarayya ya amince da zasu more wannan shirin
ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA MAI SON YA MORI WANNAN SHIRIN
• A tabbatar da cewa an cike form (ma’ana) Cike takardar neman gurbi
• Ana bukatar BVN
• Dole ne ga duk mai bukatar ya amfana da wannan shirin ya kasance ya mallaki takardar sheda daga makarantar koyon sana’o’in da babban bankin tarayya ya yarda da ita kamar misalin (Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association) da wasunsu.
• Takardar shedar rajistar sunan kasuwanci ko ta incorporation (idan kuna da ita)
• Domin samun dama ga wannan shirin, dole ne ka samu horo na musamman ga (Entrepreneurship Development Institute) (EDI) bayan training din sai su cike maka form su turawa CBN

Ziyarci shafin Nirsal Micro Finance Bank domin neman tallafin bashin CBN domin inganta sana’arku.
https://nirsalmfb.caderp.com/account/landingpage

HANYOYIN SHIGA CIKIN TSARIN
Mataki 1: Ku tabbatar kun samu horu na musamman (Training)
Wannan wajibi ne ga dukkan mai sha’awar cin muriyar shirin da ya tabbatar ya samu hour na musamman kan kasuwanci a daya daga cikin makarantun koyar da sana’o’i da babban bankin tarayya ya amince dasu; misalin Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association ko kuma wasu na daban, akwai su a sassa daban daban na wannan kasar.

Mataki 2: Neman Gurbi (Apply)
EDI/EDC da suka baka hour zasu yi iya kokarinsu na ganin sun taimaka maka tare da tabbatar da cewar ka mallaki duk wani abu a ke bukata na neman wannan tallafin na bashin AGSMEIS.
Mataki 3: Zaku karbi Kudin (Receive Funds)
Kudin za a biyaku a cikin asusunku ne. Sai dai kuma wadanda duk basu cancanta ba za a sanar dasu.
Mataki 4: Ku nemi taimakon tsarin kasuwanci
Zaku nemi EDI dinda suka baku horu ne su taimaka muku suyi muku tsarin kasuncinku, (Business Plan) kuma zasu zame masu masu taimaka a shirya sana’ar taku. Sai dai biyansu za ku yi, ba kyauta bane
Mataki 5: Ku sayar da Sana’arku
Ku cigaba da sayar da kayayyakin sana’arku ko domin ku biya bashin da kuka karba sannan kuma ku samu riba mai yawa, wanda ya karbin bashin ana tsammaninsa da zai cigaba da tanadar records, ya kuma kula da yadda yake sayarwa da sana’arsa, da kuma yadda yake kashe kudinsa domin ya tabbatar da samun ribar da zai iya biyan bashin.

TAMBAYOYIN DA AKA YAWAITA YI
1. Ta ya ya zan samu wannan bashin?
Kawai ka training a EDI da CBN ta yarda da su, (Entrepreneurship Development Institute) su zasu taimaka maku ta yadda zaku cika form din kuma su tabbatar da kun mallaki duk wani abu da ake bukata
2. Shin ina bukatar wani abu da zan jinginar?
A’a, wannan tallafi ne da aka shirya ba tare da neman wani abu da za a jinginar ba.
3. Tsawon wane lokaci zai iya kai kan na karbi kudi na?
Wannan bashin an tsara shine domin ya zama mai sauki wajen samu. Dukkan ayyukan kai tsaye ne. Tun daga matakin cikewarku da aikawarku zuwa saka muku zai iya daukar mako shida (6) zuwa takwas (8).
4. Shin ko bashin yana da ruwa?
o Bashin akwai wanda aka shirya shi ruwa na kashi 5% da zaku bayar duk shekara
o Akwai kuma wanda aka shirya shi da ribar 5% da zaku bayar duk shekara (marar ruwa kenan) ya rage naku sai ku zabi wanda kuke bukata
5. Shin ko an fara bawa jama’a kudin?
Sosai ma kuwa, tuna aka fara sakawa mutane kudinsu ta asusunsu wanda a halin yanzu an sake kudi kimanin N25b kuma ana kan bayarwa har yanzu ba a dai na ba.

WASU KARIN BAYANI
• Ana karbar kudin training 10,000 ne
• Kudin Business Plan kuma 5,000
Jimlar kudin da za a kashe 15,000 kacal

Ziyarci shafin Nirsal Micro Finance Bank domin neman tallafin bashin CBN domin inganta sana’arku.
https://nirsalmfb.caderp.com/account/landingpage

Kuyi sharing zuwa ga yan uwa da abokai domin suma su amfana da wannan damar, kuma su habbaka sana’arsu tare da taimakawa gwamnati wajen rage zaman banza da rashin abin yi a cikin al’uma.

 

Contact Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association coordinators

  • WhatsApp: 08103139272 Call: 08113777717