Matakin Da Buhari Ya Dauka Yayi Dai-Dai Na Hana Tashin Jirage A Zamfara–Sheikh Jingir

Daga  Isah  Ahmed, Jos.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, shi ne shugaban majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’kamatis Sunnah ta tarayyar Najeriya ya ce matakin da shugaba Buhari ya dauka a kwanakin baya na hana shige da fice da kuma tashin jirage a jihar Zamfara ya yi dai-dai.

Shehin Malamin ya sanar da haka ne a lokacin da yake gabatar da Khuduba a Masallacin Juma'a na 'yan taya dake garin Jos, domin wasu marasa kishin kai suna debo 'yan kasar Afirika suna satar Zinari a Zamfara, sannan sun tashin kauyuka da hare-hare ta hanyar amfani da jiragen sama.

Malam Jingir ya bayyana cewa wadannan barayin, suna dibar Zinari ne suna kaiwa kasashen turai daga wannan yankin na jihar Zamfara, ga kuma kashe mutanen mu da su ke cigaba da yi a kowacce rana ta Allah.

Ya cigaba da cewa ko shakka babu matakin da shugaba Buhari ya dauka shi ne dai-dai, na hana tashin jirage daga Jihar ta Zamfara domin yin hakan shi ne zai magance miyagun ayyukan da wadannan mutanen su ke yi a fadin kasar Zamfara.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author