Matsalar Fyade: An Dakatar Da Kwamishinan Muhalli Na Jihar Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta bada umarnin dakatar da Kwamishinan Muhalli na jihar, mai suna Mr. Abiodun Abudu-Balogun, a bisa tuhumar da ake yi masa na yiwa karamar yarinya fyade.

An tabbatar dakatar da Mr. Abudu-Balogun ne dai daga ofis bisa tuhumar cin zarafi da kuma keta haddin wata karamar yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Barakat Mayowa Melojuekun.
A wata sanarwa da aka bayyanawa manema labarai da sakataren gwamnatin jihar ya fitar, Mr. Tokunbo Talabi a ranar Lahadi a garin Abeokuta, ya tabbatar da sanarwar da dakatar da gwamantin ta yiwa Kwamishinan har zuwa lokacin da za aga an kammala bincike kan tuhumar da ake masa.


Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin dakatar da Abudu-Balugun ne domin ba shi damar samun lokacin da zai bayyana domin amsa tambayoyin da ‘yan sanda ke masa kan tuhumar dake kansa.


Sanarwar ta tabbatar da cewar, gwamnatin jihar ko da wasa ba za ta jure cin zarafin Dan-Adam ba, yana mai shaida cewa idan har aka samu kwamishinan  da hannu dumu-dumu da laifin, to ko shakka babu  gwamnatin zata nuna masa fushinta, idan kuma aka tabbatar da bashi da laifin da ake tuhumarsa a shirye gwamnatin take ta sake rungumarsa da farar zuciya.


Mr. Talabi ya shaida cewa gwamnatin jihar zata yi kokarin ganin an  tabbatar da adalci a tsakanin wanda ake tuhuma da masu kara, domin  samar wa mai gaskiya da gaskiyarsa da hukunta mai laifi in an samu.


Sanarwar ta cigaba da cewa, gwamnatin ta umarci dakataccen kwamishinan daya ajjiye mukaminsa a hannun babban sakataren dindindin na ma’aikatar muhalli ta jihar nan take.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author