Matsayin Benzema A Harkar Murza Leda Na Dabam Ne - Zidane

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana dan wasa Karim Benzema na kungiyar a matsayin dan wasan da yake da wani matsayi na dabam a harkar murza leda.

Benzema yaci kwallo daya, ya kuma taimaka aka zura ta biyu a raga a wasan da Real Madrid suka tisa Eibar da ci 3-1 a ranar Lahadi a gasar cin kofin La Ligar na kasar Spain.

Wannan shine karo na 30 da dan wasa Benzema yake  taimaka aci kwallo bayan ya zura tasa a cikin wasan na La Liga, dan wasa Cristiano Ronaldo ne kawai ya zarce shi, da gudummawa sa har guda 44, fiye da kowane dan wasan Real Madrid a karni na 21.

Zidane ya kuma jinjina namijin kokarin da Benzema yayi bayan da Real Madrid tazo kai daya da Atletico Madrid a matsayi na farko a teburin La Liga da maki 29, sai dai kuma sun fi 'yan wasan  na Diego Simeone da yawan wasanni biyu.

 

Zidane ya bayyana cewa Benzema dan wasa ne mai baiwa kungiyar nasarori, kuma matsayinsa na dabam ne a harkar kwallon kafa, ba wai dan kawai yana cin kwallaye ba.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author