Mu Muna Nan Daram-Dam A Jam'iyyar PDP-Gwamna Tambuwal

Gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar Jam'iyyar PDP, sun sake nanata aniyyarsu da kuma jajircewa wajen karfafa Jam'iyyar.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal ne yayi magana a madadin takwarorinsa a taron NEC na 90, na Jam'iyyar da yake gudana a sakatariyar Jam'iyyar ta kasa, a Wadata House dake Abuja.

"Duk mu 15 muna nan, kuma kowanne dayan mu ya himmatu da kyawawan shugabanci a jihohinmu sosai daban-daban domin karfafa Jam'iyyar mu ta PDP" inji Gwamna Tambuwal.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author