Muggan Sinadaran Tabar Shisha Sun Ɗara Na Taba Sigari — Ayesha Mohammed.

Binciken masana da aka gudanar a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya yi nuni da cewa muggan ɓirɓishin ƙarafe da ke danƙare a cikin tabar shisha ko lofe sun ɗaram ma na taba sigari.
 
Sinadaran ƙarafen da ba sa jituwa da jiki, kuma suke da haɗarin janyo kansar huhu da baki da kuma cutukan zuciya da jijiyoyin jini sun haɗar da ɓirɓishin ƙarafen "nickel", "chromium", "zinc" da "copper".
 
Binciken ya ce kwarkwaron da mashayan ke zuƙar tabar shisha ba shi da ingantacciyar rariyar da zai iya tace ɓirɓishin muggan ƙarafen. Kuma hakan ne ke sanya ɓirɓishin ƙarafen zarcewa zuwa cikin baki, huhu da jijiyoyin jini.
 
Jagorar binciken, Ayesha Mohammed, wacce masaniyar kimiyyar kemistiri ce a jami'ar Sharjar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. An kuma buga sakamakon binciken a mujallar "Oxford University Press's Journal of Analytical Toxicology".
Ciwon kansa/daji/sankara.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author