Musababbin Ciwon Damuwa Da Hayyoyoyin Magance Shi

Musababbin Ciwon Damuwa Da Yadda Za A Taimaki Wanda Ya Kamu

 

Daga Mairo Muhammad Mudi

 

Kwanakin baya a kafafen sada zumunta na ci karo da rubuce-rubuce kan matar nan da ta kashe 'ya'yanta biyu inda wasu suka yi maza suka yanke hukunci cewa saboda kishi ne. Kowa na fadar albarkacin bakinsa, wasu na la'antarta, wasu na tsine mata. Kalilan mutane ne suka tsaya suna tambayar ko a yi bincike saboda babu wani kishi da zai sa uwa ta kashe 'ya'yanta duka kuma iyakacinsu kenan mata a duniya. Wasu masana suka yi maza suka ce a binciki matar nan don daga magagganunta da namiji da ita yarinyar rikonta da ta tsira daga wannan hari nata, ya nuna tana dauke da ciwon damuwa watau depression.

 Can sai na ga wata ta yi rubutu inda ta alaka ciwon damuwa da rashin imani da tawakalli. Wannan ne ya jawo ra'ayina da in yi wannan rubutu bayan na yi bincike. Abinda na ke tsoro shine mutane su dauki mai wannan ciwon akan ba shi da imani ko ba mai tawakalli ba ne, hakan zai iya sa duk wanda ya tsinci kansa a wannan hali, ya kara durbiya cikin ciwon don zai kara ganin laifin kansa na rashin tawakalli kana wadanda ya kamata su taimaka masa za su kara tsangwamarsa wanda za a wayi gari a ga kashe yaranta da matar nan ta yi, ya zama tamkar wasan sallah ne, Allah Ya kiyaye. Amin.

 

Da farko menenen ciwon damuwa kuma me ke kawo shi?

 

Ciwon damuwa watau depression bincike ya nuna cewa shine na biyu a duniya da ke haifar da rashin kwanciyar hankali.

Ciwon damuwa, ciwon kwalkwala ne da ka iya haifar wa mai shi, rashin walwala da zama cikin bakin ciki wanda zai iya jin zaman duniya ya ishe shi ko ya ishe ta ko kuma ya shiga halin son kashe kansa. Mai ciwon kan ji ba shi ko ba ta da wani amfani a rayuwa, in ya yi tsanani zai rinka jiye-jiye da gane-gane inda mutane ba su ji ko ganin abinda mai ciwo kan ji ko kan gani ba.

 

Zai kasance suna jin wasu abubbuwan da ke fada masu a kwalkwalwarsu su aikata wasu abubbuwa wadanda ba su dace ba ko kuma wadanda in da lafiya mai ciwon shi kan shi zai ji mamaki wadanda suka aikata abinda shi ya ke son aikatawa.

 

Masana ba za iya tattacen ainihin abunda ke kawo ciwon danuwa ba amma su kan dangata wadannan abubbuwa da zan zayyana akan matakai da za su iya kai mutum ga shiga wannan matsala.

 

Hallita mutum, yanayin kwalkwala da gadon yanayin halinta kan iya sa mutum ya samu ciwon.

Cututtuka kamar na suga, hawan jini, zuciya, yawan jin zafin ciwo kamar sanyin kashi tun in cututtuka sun taru sun yi wa mutum yawa kan sa mutum fadawa ciwon damuwa.

Wasu magugguna da mara lafiya kan sha, ka iya jawo ciwon damuwa.

Jinsi mace saboda irin raunin da Allah Ya yi ta da shi ka iya fadawa cikin wannan ciwon.

Tsufa kan iya saka dan adam cikin wannan yanayi.

Yanayin wani ciki da sabon haihuwa kan sa mace ta samu ciwon damuwa.

Saki, mutuwar makusanci, rashin aikin yi, talauci da rashi mahalli duk za su iya kawo wannan cuta.

 

Kamar yadda na fada tun farko, ana gadon ciwon, idan akwai wadanda suka samu wannan cuta a layin jinin mutum to akwai yiwuwar mutum ya kamu da ciwon.

Sannan in mutum ya taba yin ciwon a baya to akwai yiwuwar zai iya sake kamuwa da shi.

Rashin jituwa tsakanin iyalai, misali, iyaye da 'ya'yansu ko miji da mata.

In mutum ya taba buge kansa.

 

Ciwon rashin barci watau insomnia kan iya kawo ciwon damuwa kamar yadda ciwon damuwa kan iya kawo rashin barci.

 

Depression ba cikin lokaci daya ake kamuwa da shi ba kamar ciwon ciki, shiga ya ke a hankali inda in ba an lura ba babu wanda zai gane makusanci na dauke da wannan ciwon sai in illa ta faru.

 

Ciwon damuwa, ciwo ne da ke tabar kwalkwala amma yawanci mutanenmu ba su farka da haka ba sai an ga mutum yana hauka tuburan sannan a san ya shiga halin da za a taimaka masa.

 

Tayaya za mu yi mu gane mai ciwon damuwa?

 

Rashin barci ko yawan barci alamomi ne na wannan ciwon.

 

Kadaicewa, mai wannan ciwon ko kuma wanda wannan ciwo ke son kai masa hari, zai kasance ma'abocin kadaita. Ba za ta so shiga mutane ba, ta fi son a kowane lokaci tana ita kadai.

 

In sun sami kansu cikin mutane da wuya suke saka baki cikin magagganun da ake saboda suna wurin ne amma hankalinsu ba ya wuri.

 

Za ku tsinci me wannan ciwon da yawan tunani, hankalinsu na nesa daga inda suke.

 

Mai ciwon zai kasance ciki tsoro ko firgita. Wani zai kasance ba su magana ko kuma a same su da yawan magana ko fada ko kuma yawan kuka ko babu abun kuka.

 

Yaya za mu taimaka wa wannan mai ciwon?

 

Mutum da kan shi zai iya taimaka wa kansa in ya tsince kansa cikin yawan tunani ko ganin daya daga cikin alamomin da na zayyana tare da shi, ya yi maza ya ga likita ko wani wanda ya amince masa ya bayyana masa matsalarsa. Sannan in mutum ya lura makusancinsa na fuskantar wannan hali, ya hanzata ya kai shi ga likita inda zai ko za ta samu kulawa na musamman.

 

Sannan a duk lokacin da wani naku ya ce yana ganin wani abu ko yana jin wani abu,  kar ku yi saurin karyatawa ko kuma a jirgita daukan mataki.

 

Mai wannan ciwo na bukatar kulawa da nuna so, kulawa na sosai sannan a kasance a kowane lokaci ana tare da shi. 

 

Babban wani mataki bayan ganin likita shine addu'a. A taimaka mata ko masa da addu'a sannan a rinka karfafa masu gwiwa wajen addu'a.

 

Za mu iya kare kanmu da makusantanmu daga fadawa cikin wannan ciwon ta hanya yin addu'o'i da suka sauwaka a gare mu dare da rana da kowane lokaci don neman samu lafiya da kariya daga mumunar kaddara.

 

A duk lokacin da muka tsinci kan mu cikin wani yanayi da muka ga ya fi karfinmu ko yana son ya fi karfinmu, mu yi hakuri, mu dogara ga Allah sannan mu san cewa Shi Kadai ne ke da mafita a duk matsalolin da muka tsinci kanmu.

 

Mu daina yawan yanke hukunci kan abubbuwa da Allah Ya jarabci dayarmu ko kuma mu rinka buga kirji cewa wannan abun ba zai taba faruwa da mu ba ko laifin wanda ya faru da shi ne. Ko kuma mu rinka ganin iyawarmu ne hakan ya wuce kanmu, maimakon hakan , mu kasance masu addu'o'i kan wadanda Allah Ya jarabta kana mu yi wa kanmu da wadanda hakan bai faru da su ba addu'o'in kariya.

 

Ma'aurata, dole ne mu rinka hakuri da juna, muna sauke hakkin junanmu da Allah Ya daura mana, muna tausaya wa juna.

 

An gane mata ne suka fi shiga cikin wannan yanayin na damuwa saboda haka kalubalenku maza tumma mazan Hausawa, mata 'yan lallashi ne. In na miji na nuna wa matarsa soyayya da lallashi a gare ta to za ta kasance cikin walwala da farin ciki a kowane lokaci yadda koda wane hali ta tsinci kanta, za ka same ta mai hakuri da biyayya.

 

Don Allah maza, zan rufe wannan rubutu da rokonku kan cewa ku kasance masu lallashi da nuna wa matanku soyayya ta zahiri, wannan kadai shine maganin ciwon damuwa.

 

Allah Ya kare mu, Ya bai wa masu shi sauki a duk inda suke, amin.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author