Na bada Rai na Fansa Idan har Zai zama dalilin Samun Kwanciyar Hankali a Arewacin Nigeria - Sheikh Nuru Khalid

Fitaccen Malamin addinin nan na Islama dake garin Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya yi martani game da tabarbarewar tsaro a Gwamnatin Buhari, Anga wani bidiyo inda fitaccen Malamin yake cewa “Zamu shiga Internet mu fadawa duniya, ba zamu iya yin shiru a yanayin da ake ciki ba ana ta kashe mu kamar kiyashi ba wanda zai yi magana.
 
“Anan wajen na taba fada cewa wallahi kaji a gonarsu baka isa kayi masu irin wannan kisan ba, amma ana ta kashe mu ba wanda zai yi magana?… Maganin ku ne ma ku ma ai… [talakawa] kune ranar zabe duk ku haukace, ai wallahi jihadi ne…, kiristoci zasu kwace Nigeria…, to shikenan basu kwace Nigeria ba an barta hannun wanda zai zauna ana kashe ku, iya abunda za ayi idan an kashe ku wai sai ace shugaban kasa yayi Allah wadai… wane irin Allah wadai? An zabe shi don yayi Allah wadai ne? An zabe shi don ya dauki mataki ne! Idan ba zai iya daukar mataki ba to ya sauka daga kan karagar mulkin kasar.
 
Sheikh Nura Khalid ya cigaba da fadin cewa, idan da ace inba da raina a matsayin fansa kuma a daina kashe 'yan arewa to wallahi zan yarda a kashe ni.
 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author