Na Lashe Shekaru Ina Sayar Da Mushen Kaji A Maiduguri - Ebere

Rundunar jami'an tsaron farin kaya Civil Defence a Jihar Borno ta yi nasarar cafke wani mutum daya daɗe yana safarar mushen kaji gami da sayarwa jama'a a Jihar Borno na tsawon shekaru.
A lokacin da yake amsa tambayoyi a helkwatar rundunar, ya tabbatar da cewar a kalla ya yi nasarar sayar da Mushen Kaji sama dubu bakwai a Jihar Borno da kewaye.
Ɗan kimanin shekaru 33 Mutumin mai suna Hassan Ebere, ya ƙara da cewar bai san adadin shekarun da ya shafe yana gudanar da muguwar sana'ar ba a Maiduguri.
"Kasancewata Maraya ne ya jefani shiga cikin wannan mummunan aiki domin samun rufin asiri, amma na yi nadama kuma da yardar Allah ba zan sake ba".
Rundunar tsaron farin kayan ta bayyana cewar bayan ta kammala binciken ta zata iza ƙeyar Ebere kotu domin girbar abin da ya shuka.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author