Naci Albarkacin Kwankwaso Kaga Ko Dole Inyi Murna-Matashi Dan APC

Wani Matashi kuma dan gwagwarmayar siyasa a cikin tutar jam'iyyar A P C mai mulki a tarayyar Najeriya mai suna, Comrd Yakuq Umar Masanawa ya bayyana farin cikinsa dajin dadinsa a game da mabiya bayan kungiyar darikar kwankwasiyya reshen jihar Kebbi bisa girmama shi da suka yi a garin birnin kebbi ranar 14 ga watan Janairu shekara 2021.  

Comrd Yakuq Masanawa yace, a irin kokarin da wani mabiyin kungiyar darikar kwankwasiyya yayi mar a ranar Juma'a 14 ga watan Janairu, shekara 2021, a babban ofishin M T N Nig. Da yake birnin na Kebbi, ya tabbatar da cewa duk da yake shiba dan jam'iyyar PDP bane to amma yaji yana Qaunar kungiyar ta kwankwasiyya. 

Comrd Masanawa, ya cigaba da bayyana farin cikin sa tare dajin dadin abinda mabiyin kungiyar kwankwasiyyar yayi mar, inda yace yana rokon suma 'ya'yan jam'iyyar ta APC da su ringa koyi da irin halayen na 'yan kwankwasiyyar.

Da wakilin gidan jaridar Globng.com ya tambaye shi ko wanne irin taimako da mabiyin kungiyar kwankwasiyyar yayimar sai yace, kawai da dan kwankwasiyyar ya ganshi da Takunkumin rufe fuska ( face mask) mai dauke da hoton tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Eng. Rabi'u Musa Kwankwaso sai ya rungume shi yana cewa wannan na gidane saboda haka anan ta ke a kayimar aikinsa kuma aka sallame shi babu ko sisin kobo.

Comrd Masanawa, yace kusan satin na biyu ina bin layin Welcome Back amma layi baizo kansa ba, sai ranar ta juma'a sai na ari takunkumin rufe fuskar na wani abokina dan kwankwasiyya naje ofis din aiko nan ta ke aka yimin kuma ko naira banbayar ba, kaga ko naci albakacin kwankwaso.

Daga karshe Comrd Yakuq Umar Masanawa yace, yana yiwa dukkanin mabiyan kungiyar ta kwankwasiyya da mai gidan nasu Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso fatan alheri tare da fatan Allah ya kawo rabo mai amfani.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author