Nan Da Wani Dan Lokaci Kadan Za Mu Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Nijeriya-Janar Leo Irabor

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Sabon shugaban hedikwatar tsaro a Najeriya, Manjo Janar Leo Irabor ya bada tabbacin cewa nan gaba kadan matsalar tsaro za ta zo karshe a Kasar.
Majo Janar Irabor ya bayar da wannan tabbaci ne jim kadan bayan ganawar da yayi da sauran shugabannin sabbin tsaron Nijeriya tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Manjo Janar Irabor ya ce shugaba Buhari ya ba su umarnin kawo ci gaba a harkar tsaro sannan kuma sun san cewa akwai tunanin zasu kawo canji dake zukatan mutane dan hakan ne ma za su dage wajan ganin sun yi iya bakin kokarinsu.
 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author