Neymar Jr yadakatar da tattaunawar kara kwantiraginsa a PSG

          Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Paris saint Germain Dan asalin kasar Brazil Neymar Junior ya dakatar da tattaunawar kara kwantiraginsa da kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa 

       Tauraron gwarzon Dan wasan dai yadakatar da wannan tattaunawane saboda fahimtarsa da cewar Dan wasa Lionel Messi Dan kasar Argentina zai kara kwantiragi da kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona , 

        Dan wasan dai Neymar Jr nason kara hadewa da tsohon abokin wasansa Lionel Messi a filin wasa na Camp nou 

        Dan wasa Neymar Jr ya tuntubi sabbin mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona inda yatabbatarmusu da Babban burinsa nason dawowa kuma yaqara da gamsar da mahukuntan kungiyar ta Fc Barcelona cewar zaidace da yanayin tattalin arzikin Fc Barcelona na wannan lokacin

To Fc Barcelona Fans kunason sake ganin Fuskar Neymar Jr a Camp Nou ?

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author