Nuhu Ribaɗo ya ce da kansa ya ɗauki ƴarsa da take amarya ya kaita ɗakin mijinta

 

Tsohon shugaban hukumar EFCC kuma tsohon ɗan takaran gwamnan jihar Adamawa, Malam Nuhu Ribaɗo ya bayyana cewa, shi da kansa ya ɗauki ƴarsa Fatima zuwa gidan mijinta, Alhaji Aliyu Atiku Abubakar (Turakin Adamawa).

 

Malam Nuhu Ribaɗo ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a cikin daren nan, inda ya ce hakan da yayi na daga cikin sauƙe nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na Uba.

 

Hakan na nufi cewa, ɗan siyasan bai bari wani ya ɗauki ƴarsa zuwa ɗakin mijinta ba, shi da kansa ya ɗauketa a mota zuwa gidan mijinta. 

 

A cewarsa, "Yanzu na kai ƴa ta Fatima gidan Mijinta. A halin yanzu na sauƙe nauyin ta dake kaina a matsayin mahaifinta". Malam Nuhu Ribaɗo 

 

Ya kuma miƙa saƙon godiya ga waɗanda suka halarci adu'ar ɗaurin auren da ya gudana a yau Asabar a Abuja, da ma waɗanda suka aiko da fatar alkhairinsu. 

 

A yau aka ɗaura auren ƴar tasa Fatima da Angonta Aliyu Atiku Abubakar, auren da ya samu kace nacen jama'a tun bayan bayyanar hotunan bikin, inda wasu ke bayyana cewa amaryar bata yi shagar mutunci ba a matsayinta na ƴa musulma, bafulatana kuma ƴar Arewa.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles