Ranar Tarin Fuka ta Duniya-WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta ware duk ranar 24 ga watan Maris na kowace shekara don bikin ranar tarin fuka (tarin TB) a faɗin duniya don wayar da kan al'umma illar cutar, hanyoyin kariya, da ma tallafa wa masu fama da ita a faɗin duniya.
 
Tarin fuka ita ce cuta mai yaɗuwa mafi kisa a duniya. Inda cutar ke lashe rayuka fiye da 4000 a kullum. A yayin da kimanin mutum 30,000 ke harbuwa da cutar kowace rana. Hukumomin lafiya na duniya sun samu nasarar ceto rayukan mutane miliyan 58 daga cutar daga shekara ta 2000.
 
Taken ranar ta bana shi ne "Lokaci Yana Tafiya". Wannan take hannunka-mai-sanda ne ga hukumomi domin su ƙara zage dantse wajen kawar da cutar a duniya.
Ƙwayar cutar bakteriya nau'in "mycobacterium tuberculosis" ce ke kawo cutar. Kuma tana kama sassan jiki daban-daban musamman ma huhu.
 
Idan kana fama da tari tsawon sati biyu ko fiye, garzaya asibiti don tantance ka.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author