Rashin Fahimtar Kalamaina Yana Janyo Rikici A Jihar Kano, Inji Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Kano

Shugaban kwamitin riƙon na jam'iyyar APC a jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas, yace mutane basa fahimtar kalamansa a gidan siyasa, shi yasa suke ƙoƙarin haddasa tashin hankali tsakanin jam'iyyar APC da sauran jam'iyyun adawa a jihar Kano, kawai dai yana amfani da yanayin maganar ƴan adawa, sai shima yayi martani da irin abinda suka ce.
Shugaban yayi wannan jawabin ne, yayin da wata ƙungiyar matasa mai rajin tsaftace siyasa a jihar Kano (Kano Youth Political Forum), ƙarƙashin jagorancin Mukthar Dauda Raula, suka kai masa ziyara, harma ya shaida musu cewa, "Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, mutumin kirki ne mai kamala, wannan tasa bazan bari a taɓa martabar gwamnatinsa ba tare da na kare shi ba".
"Wasu ƴan adawar suna shiga sha'anin mu ne, wanda shine dalilin da yasa muke tura musu saƙo mai tsauri, amma fahimta ce kowa da irin tasa". Inji Abbas
A nasa ɓangaren, shima shugaban ƙungiyar, Mukthar Dauda Raula, yace sun shirya tsaf domin canja akalar siyasar Kano, wajen kakkaɓe ƴan siyasar dake ɓoye ƴaƴansu a gida, amma kuma suna gayyato ƴaƴan talakawa suna dorasu a turbar shaye-shaye da jagaliyancin siyasa, wannan tasa tilas su hadu da shugabannin dake damawa don ganin goben matasan Kano tayi kyau.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author