Rashin Imani: Ta Kulle Tagwayenta A Daki Masu Shekaru 3 Har Tsawon Kwana 3 Ba Ci Ba Sha

Hukumar yan sanda a jihar Ekiti tayi  nasarar kama wata mata mai suna Joy Fatoba, a bisa zargin ta na kulle tagwayenta masu shekaru 3 a cikin daki har kwana 3 ba tare da ta ajjiye masu abinci ko ruwan sha ba.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Ekiti, DSP Sunday Abutu ne ya bayyana faruwar lamarin a wata takarda da ya aika da ita ranar Litinin 5 ga watan Maris 2021. Ya kara da cewa yan sanda sun sami nasarar ceto yaran kuma har sun kai su ga Asibiti domin samun kulawan Likitoci .

 

DSP Abutu ya ce a ranar Lahadi ne 4 ga watan Aprilu, 2021 yan sanda suka sami kira daga karamar hukumar mulki ta Igbara-Odo, dake Ekiti ta kudu maso yamma a jihar ta Ekiti da cewa wata mata ta kulle yaranta a cikin daki har kwana 3 ba tare da ta ajjiye masu abinci ko ruwan sha ba.

 

Ya bayyana cewa matar ta yi ikirarin cewa za ta kashe yaran idan aka tilasta mata da ta bude kofar.

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author