Sai An Sayar Da Kusan Rabin ’Yan Wasan Barcelona Domin Yin Gyara – Iniesta

Tsohon dan wasan tsakiya kuma tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Andries Iniesta, yace idan shugabannin kungiyar suna son su gyara kungiyar ta koma kamar yadda take buga wasa a baya to sai an sayar da rabin kusan ‘yan wasan kungiyar an sayo wasu.

A kakar kwallon kafa ta bana dai ta nuna rashin kokarin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a gasar La liga, amma kuma tauraron ta yana haskakawa a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta Champions League a kakar wasa ta 2020 zuwa 21 wadda ake bugawa.

Barcelona tasha yin rashin nasara a hannun kungiyoyin da bai kamata su cita ba a bana wanda hakan ne yake nuna cewar abune mai wahalar gaske idan tana cikin wadanda ake hasashen lashe kofin La Liga na wannan shekara.

Ranar Asabar ne dai Barcelona ta buga wasa 2-2 da kungiyar kwallon kafa ta Balencia a gasar La liga lamarin da ya kawo har yanzu kungiyar take baya duk da kasancewa tana da sauran wasanni guda biyu wadanda bata buga ba.

 

“Mafi  yawa daga cikin ‘yan wasan na Barcelona a wannan yanayin basu cancanta su buga wasa a kungiyar ba saboda girman wannan Barcelona amma kuma a haka suke wakiltar kungiyar, kuma idan har ana son gyara ne to sai an sayar da rabin kusan ‘yan wasan kungiyar gabadaya” in ji Iniesta, wanda ya lashe kofuna da dama a kungiyar ta Barcelona.

 

kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana tare da shugaba na rikon kwarya wanda ke son ya zama mai jan ragamar mulkin nan gaba, bayan da kungiyar ke fuskantar matsalolin  biyan albashi, saboda matsin tattalin arziki da annobar cutar korona ta haddasa.

A wannan lokaci yanzu Barcelona tana ta biyar a teburin La Ligar kasar da maki 21, bayan da ta buga wasa 13 a wannan kakar ta bana, bugu da kari kuma kungiyar wadda mai koyarwa Ronald Koeman ke jan ragama ta ci wasa biyar a La Liga da canjaras uku da rashin nasara hudu da kwantan wasa biyu.

Kungiyar ta yi rashin nasara ne a wasanni da dama a bana kamar yadda ta yi a shekarar 2017 zuwa 2018 da kuma 2018 zuwa 2019 a La Liga, yayin da ta yi rashin nasara a wasa uku ta kuma lashe kofin a shekarar 2018 zuwa 2019.

Tuni dai kuma Barcelona  ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta Champions League ta bana da maki 15, yayin da Juventus tayi ta daya da maki 15 a rukuni na bakwai kuma yanzu Barcelona zata fafata da PSG a wasan zagaye na gaba.

 
 

A kakar shekarar 2003 Enric Reyna shi ne ya rike Barcelona a matakin rikon kwarya, bayan da Joan Gaspart ya yi murabus daga baya Radomir Antic ya maye gurbin Louis ban Gaal a matakin koci.

A waccan kakar Barcelona ta fuskanci kalubalen samun gurbin shiga gasar UEFA Cup, inda kungiyar ta sa kwazo ta kuma samu gurbin a wasan karshe da ta buga sannan kuma a lokacin Laporte ya kalli karawar a matakin shugaban kungiyar a lokacin da ya ci zabe ya zama jagora na hudu a kungiyar a kakar.

A kakar wasa ta 2020 zuwa 21 za ta kammala ne da shugaba uku, bayan Josep Maria Bartomeu sai Carles Tuskuets na rikon kwarya da wanda za a zaba ranar 24 ga watan Janairun shekara ta 2021.

 

Hakika Barcelona na bukatar sa kwazo anan gaba ko dai ta lashe kofin La Liga ko kuma ta ci Champions League, bayan da Kyaftin din kungiyar Lionel Messi a ke maganganun zai bar Camp Nou a karshen kakar ta bana.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author